Tarihin Sayyada Mariya Al-Qibtiyya (R.A)



Tarihin Sayyada Mariya Al-Qibtiyya (R.A) 

Mariya bn Shamʿūn (da Larabci: MARیة بنت شمعون ), wanda aka fi sani da Mārīya al-Qībṭīyya (da Larabci: MARیة القبطیة ), ta kasance daya daga cikin matan Manzon Allah (SAWW). Ita wata baiwa ce da aka aika wa Manzon Allah (SAWW) tare da wasu kyaututtukan da al-Muqawqis, mai mulkin Masar da Iskandariya na lokacin ya aiko wa Manzon Allah (SAWW). A lokacin da ya amsa wasikar Manzon Allah (SAWW). A cikin matan Manzon Allah (SAWW) ban da Khadija, Mariya ita kadai ta haifi da, ana kiransa Ibrahim.

Kafin Auren Ta Manzon Allah (SAWW)

An haifi Mariya Al-Qibtiyya Sham'un a unguwar Hufn a unguwar Ansina a kasar Masar. A cikin 7 / 628-9, Annabi (SAWW) ya aika Hatib bn Abi Balta'a zuwa ga al-Muqawqis, mai mulkin Masar da Iskandariya da wasikar kiransa zuwa ga Musulunci. Domin amsa kiran Annabi (SAWW) al-Muqawqis ya aika masa da Mariya tare da ‘yar uwarta, Sirin ko Shirin, da sauran kyaututtuka. Ya kuma aika wa Annabi (SAWW) da wata wasika da ke cewa: "Na girmama manzancinku, kuma na aiko muku da wasu kuyangin mata guda biyu wadanda suke da daraja a kasar Masar mai girma ko al-Qibt". An ruwaito cewa Hatib bn Abi Balta’a ya gabatar musulunci ga kuyangin biyu, kuma sun musulunta a hanyarsu ta zuwa Madina

Aure da Annabi (SAWW)

Lokacin da suka isa Madina, Annabi (SAWW) ya zabi Mariya da kansa, kuma ya baiwa Hatib, Sirin. Gidan farko da Ummul Muminina Mariya ta zauna a cikinsa shi ne gidan Haritha bn Nu'man. Ta zauna a wurin har tsawon shekara guda. Falalar Mariya da kulawa ta musamman da Manzon Allah (SAWW) ya yi mata ya sanya kishin sauran matan Manzon Allah (SAWW) musamman A'isha da Hafsa (Allah Ya Kara Yarda Da Su).

Mariya ta kasance saliha kuma baiwar Allah, kuma Annabi (SAWW) ya yi mata falala ta musamman. Marubuta tarihi da tarihin rayuwa sun yaba da ibadarta. 

An karbo daga Manzon Allah (SAWW) yana cewa ga musulmi: "Idan kuka ci Misira, ku kyautata musu, domin ni surukinsu ne.

Haihuwar Ibrahim

Bayan an zaunar da ita a sabon gidanta, Mariya ta haifi dan Manzon Allah (SAWW) Ibrahim, a ranar 8 ga watan Zu al-Hijja wanda yayi daidai da 8 ga watan maris Maris 630 miladiyya. Kamar yadda hadisi ya nuna a wannan lokaci jibrilu ya bayyana ga Annabi (SAW). kuma ya gaishe shi da suna "Aba Ibrahim" (mahaifin Ibrahim). An ruwaito cewa Annabi (SAWW) ya nuna wa A’isha Ibrahim ya ce mata: “Dubi yadda yake kama da ni”. A’isha saboda kishi, ta ce: “Ba ya kamance da ku”. 

Ibrahim ya rasu a shekara ta 10/631 kuma aka binne shi a makabartar al-Baqi'. Manzon Allah (SAWW) ya yi bakin ciki matuka da rasuwarsa, ya ce, “Wannan bakin cikin yana sa hawaye na zubowa daga idanuwa, kuma yana sanya zukata cikin bakin ciki, ba zan ce wani abu da zai kawo fushin Ubangiji ba. 

“Ido suna zubar da hawaye, zuciya ta yi bakin ciki, amma ba mu ce komai ba game da abinda Ubangijinmu ya yarda. Lallai ya Ibrahim mun yi bakin ciki da tafiyarka”. (Sahihul Bukhari, hadisi na 1303).

(Lokacin da Ibrahim ya rasu) An sami kusufin Rana kuma mutanen Madina suna cewa: "Rana ta yi kusufine saboda bakin cikin rasuwar Ibrahim." Annabi ya hau kan mimbari ya yi wa mutane jawabi da cewa fadar wannan kuskure ne:

Ya ku mutane, rana da wata alamu ne guda biyu na ikon Allah Madaukakin Sarki kuma a wurinSa ne ya kaddara su kuma ba za su yi bakin ciki da mutuwar kowa ba.

Hakika rana da wata ba sa yin husufin mutuwa ko rayuwar wani, saboda haka idan kuka fuskanci irin haka, sai ku fara yin salla."

Rayuwar Mariya Bayan Wafatin Manzon Allah (SAWW)

Bayan wafatin Annabi Muhammad (SAW) Sayydina Abubakar (RA) ya ware mata Albashi daga baitulmali kuma an ci gaba da biyanta a zamanin halifa na biyu Umar Ibn Al-Khattab (RA).

Mutuwa

Mariya ta rasu shekaru 5 bayan wafatin Manzon Allah (SAWW) a ranar 16 ga watan Muharram 16 a watan Fabrairu 637 miladiyya a zamanin Sayyadina Umar Ibn Al-Khattab (RA) kuma Umar Ibn Khattab ya kira jama'a don jana'izarta ya yi mata Salla. kuma an binne ta a makabartar al-Baqi'.
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url


';