SABBIN DOKOKIN HUKUMAR KAROTA NA 2024



SABBIN DOKOKIN HUKUMAR KAROTA NA 2024๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

●Kada wani direban adaidata sahu ya kuskura yana tuki da gajeran wando. 

●Kada a kama ka kana tuki kuma kana shan sigari' Ko kana dauke da askin banza. 

●Kada ka dauki mata fiye da adadin abin da sit dinka yake dauka wato (mutum uku) banda daukar mata a gefen ka. 

●Kada wani direban adaidata sahu ya dauki mace ya kaita zuwa wurin da ake aikata lalata' Idan har yayi hakan aka kamashi hukuma zata dauki mataki akan sa. 

●Banda daukar aboki a gefen mashin kuna haya tare' Domin hakan na kawo barazanar tsaro.

●Banda daukar kaya fiye da kima (overload) ko kuma parking a wurin da bai dace ba. 

■Kar kuma a manta tsofaffin dokokin suna nan yanda suke.

⚠️Duk wanda aka kama ya karya daya daga cikin wadan nan sabbin dokokin' Doka zatai aiki a kansa.

Edited by: Hafiz Lamin Hassan
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url


';