Uncategorized

MATSATSUBI LITTAFI NA UKU PART H

4
download

MATSATSUBI LITTAFI NA UKU PART H 

 **MATSATSUBI**💥💥
LITTAFI NA UKU ✍️✍️
PART H ❤️❤️Hbad:”;xgn

NA: ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴

POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️

TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️

GORON JUMA’A ❤️🙏

https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share

MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA…..

Guluz yayi dariya yace

aikoda maganin ya kare nasan ‘yan uwana

bazasu tafi su barni ba

kasan muna da matukar hadin kai

da dai su tafi su barni gwara su tsaya duk

abinda

zai sameni ya samesu gaba daya

kodajin haka sai gimbiya ashwarya ta tsoma

baki acikin zancen tace

au kana nufin ku aljanu bakwa tsoron mutuwa

nikam ina ganin idan sukaga wani bala’ìn zasu

iya guduwa su barka

guluz ya sake bushewa da dariya yace

aimu aljanu muna da son junanmu

fiye da mutane

kuma munsan mahimmancin alkawari bama

karya shi

ku kuwa mutane akan dukiya ma kuna iya karya

alkawari ko kuci amana

wannan batu ba karamin haushi ya baiwa

gimbiya ashwarya ba

ta bude baki zata mai d raddi sai yarima

sammaru

ya tari numfashinta da cewa

hirar nan ta isa haka kuzo muci gaba da tafiya

cikin hanzari ya haye bayan aljani guluz ya zauna

koda ganin haka sai dukkansu suka hau kan

sauran aljanun

alokaci guda aljanun shida suka tashi sama

tafiyar rabin sa’a sukayì kacal suka iso nahiyar

wadansu manyan dodanni wadanda suka

kasance dogaye zankala zankala

saboda tsawon su duk sun kere bishiyoyin dajin

da tsaunika

koda wadannan dodannin suka hango su

yarima sammaru

asama ‘yan kanana kamaI’m tsuntsaye zasu

gifta

ta samansu sai suka daga kawunansu sama

suka wangame bakunansu suka hura musu

wata iska mai tsananin karfi wacce inda acikin

garice zata iya rushe gidaje.

kuma zata iya daukar mutane ta rinka yawo

dasu asama

nan da nan gagarumar iskar ta birkita hankalin

su yarima sammaru da

aljanun shida ya zamana sun kasa gaba sun

kasa baya

kuma sai gware suke da juna, tabbas idan aka

kara ‘yan dakiku ahaka

zasu iya hallaka, cikin karaji yarima sammaru ya

baiwa su guluz umarnin saukowa kasa

nantake kuwa suka bi umarnin

kafin su iso kan turba tuni jaruman shida sun

zare takubbansu

suna dira kasa wuri ya hautsine da rurin mazaje

dana dodannin

wannan karon sai su yarima sammaru suka

gane ruwa ba sa’an kwando bane

domin saran dodannin suke amma

kamar a banza domin dodannin sun kasance

masu tsananin juriya

karfi da taurin kai

nanfa dodannin suka kuntata musu yazamana

su

yarima sammaru basa iya komai sai kokarin kare

kai

ana cikin hakane wani dodo ya kama kafar

yarima yauhana ya

karyata da karfin tsiya

yauhana ya kwarara uban ihu cikin dimaucewa

kafin yauhana yayi wani yunkuri tuni dodon

ya saka kafar gaba daya abakinsa ya gutsireta

da bakinsa

ya kama ci kamar mutum yana asuwaki da

cinyar kaza

nantake yauhana ya sulale kasa sumamme

koda ganin abindaya faru sai yarima sammaru

ya

fusata ya daka tsalle sama tun a saman yarima

sammaru ya

zare wata rantsatstsiyar wuka kawai saiya duro

akan dodonnan dake cin kafar yauhan

take ya luma masa rantsatstsiyar wukar a

tsakiyar kansa

kuma ya zareta da karfin tsiya take jini ya kama

tsartuwa asama kamar an fasa goran ruwa

nanfa dodon ya kama make make da ruri ya fadi

nan

ya tashi can har rai yayi halinsa

wannan ce damar da jaruman shida suka samu

suka gano makasar dodannin

don haka suka ci gaba da saransu da sukarsu

aka

kawai sai gani akayi dodannin suna zubewa

kasa matattu

a wannan lokacin ne yarima sammaru ya samu

dama y kwararawa yarima lauhana

wannan ruwan maganin

a karshen cinyar guntulalliya

take wajen ya bushe kamar anfi shekara da

gutsure kafar

adaidai wannan lokacin ne wasu dodanni suka

kawowa yauhana sura don su karasa cinyeshi

cikin zafin nama sammaru ya daukeshi ya

azashi abayansa

sannan ya kaiwa dodannin sara aka alokaci

guda

cikin sa’a kuwa ya raba musu kawuna Kamar an

datsa kabewa

gida biyu take suka zube kasa matattu

nanfa aka cigaba da ragargazar dodannin nan

saida aka shafe sa’a uku

ana gumurzu sannan aka karar da dodannin

awannan yaki babu wanda bai samu rauni ajikin

sa ba

sama da guda uku

yarima sammaru ne kadai ya sami rauni biyu

daya akafarsa wani dodo ya yankeshi da farcen

hannu

daya kuwa a cinyarsa aka caka masa kahon ka

wanda saidaya durkusa kasa yana mai ihu

amma cikin tsananin juriya ya sake mikewa

tsaye

yaci gaba da sara da suka her aka gama yakin

yarima lauhana

yana sabe akafadar yarima sammaru kuma

asume

gimbiya ashwarya ce kadai tayi jarumtaka

kwatankwacin irin wacce

yarima sammaru yayi, amma itama ta sami rauni

abayan kafarta

saikuma larbuz wanda ya taka mahimmiyar rawa

awannan yaki

gaba dayan su dai babu wanda baisha wahala

da samun raunika da yawaba, don har jirine ya

rinka dibarsu saida

sammaru ya kai masa daukin magani

da gaggawa sannan ya dawo hayyacinsa

bayan an gama yakinne kowa ya sharbe akasa

harda suma aljanun shida

sai yarima sammaru ya bisu daya bayan daya ya

saka

musu magani aci wukansu

saidaya gama da kowa sannan yaje kan gimbiya

ashwarya wacce

take zaune agefe guda akan wani karamin dutse

koda yazo gareta ya kalleta sama da kasa baiga

wani rauniba

saiya juya da nufin tafiya

ya zaka tafi baka samini magani ba?

ta tambaya tana murmushi

cikin mamaki yarima sammaru ya waigo ya

dubeta yace

ai banga rauni ko daya ba ajikinki

ashwarya tace baka duba sosai bane

zagayo bayana ka kwaye rigata ka ga ʀɑuɳi

batareda d gardama ba yarima sammaru ya sa

hannunsa zai kwaye rigarta sai hannunsa

ya kama kakkarwa, bakomai ne ya haddasa

hakanba

face ganin kyakkyawan surar jikinta da kuma

fatarta

mai tsananin haske da laushi, duk da cewar

raunin dake bayan nata na da dan girma

amma bai razana sammaru ba kamar yadda

kyakkyawan jikinta

ya razanashi, kamar tasan halin daya shiga sai

tace

me kake jirane ko kuwa kaima zuciyar ragwaye

gareka ciwon y firgita ka

sammaru yayi murmushi yace

ai abin tsoro baya firgita mazajen kwarai

saidai abin mamaki

hakadai ya daure ya zuba mata maganin

hannunsa na karkarwa

bayan ya gama da ita saiya juya don ta koma

inda yake

ba zato ba tsammani saiyaji ankira sunansa

cikin mamaki ya waigo suka dubi juna tana mai

murmushi agareshi

zauna nan abinda tace dashi kenan kawai

sammaru ya zauna

yana mai mamakin hakan kawai saita karbi

kutt
un maganin

dake hannunsa ta fara zubawa akan rauninsa

dake cinya

gaba daya. jaruman nan kuwa da aljanun nan

shida sai suka zuba musu ido

tuni awannan lokaci kishi ya turnuke yarima

lubaiku da larbuz

idan na barka kasa maganin da kanka

banyi maka adalciba

domin kai kadai kasawa kowa maganin nan

kamata yayi kaima ayi maka kara

koda jin wannan batu sai sammaru ya yi

murmushi yace

nagode ammafa inason zama da mutumin dake

da kara

kuma inason zama da mace mai zuciyar maza

ashwarya ta bushe da dariya sannan tace

daina kodani haka karkasa

kaina y fashe in banda abinka ina abin yake

ai gadai mAce can mai zuciyar maza tana

kafsawa dasu

cikin mamaki sammaru yace

wakenan kike nufi?

gimbiya fauwaz mana

duk lokacinda na tunoda lokacinda boka

hulumul bakahur

ya nuna mana ita amadubin tsafinsa sa’adda

take ragargazar maza

sai naji kishi ya kamani tabbas fauwaza ta fini

jarumtaka

da kyau nesa ba kusaba

ace nice ita da dolene na shahara ko ina acikin

duniya

awannan zamani, sammaru yayi murmushi yace

ai yanzu ma zaki shahara aduniya idan her kika

sami nasarar

shiga cciki kogon muddarul ikisina kika debo

ruwan

tsumin tsafin bokanya tazubul luhucul acan

taskar tsafinta

kodajin haka sai ashwarya tayi ajiyar zuciya tace

tana zaton dayanmu zai iya cika wannan buri

ka sani cewa naji daga bakin manyan bokayen

duniya cewa

fiye da shekaru dubu baya

babu wani mahaluki daya taba shiga cikinsa ya

fito araye

don haka ba shigar bace wahalaba fitowarce

wahala

sammaru ya jinjina kai yace

hakika zancenki dutsene, to amma ai ance

faduwar gaba asarar namijine

dadai mu zauna mu zuba ido muna gani

iyayenmu su hallaka

gwara muma mu hallaka kan kokarin cetonsu

kafin ashwarya tace wani abu saiga boka karluz

ya taho garesu

da zuwa ya durkusa agabansu sannan ya fiddo

madubinsa na tsafi ya ajiye agabansu

yace, yakai sammaru jagoran tafiya kayi sani

cewa

zan iya nuna maka sauran hadarin dake

gabanmu acikin dajin nan yanzu anan wurin

cikin murna sammaru yace

maza ka nuna mini don musan matakin da zamu

dauka

nantake karluz ya shafi madubin tsafinsa

saiga hoton wadansu dodannin acan gaba

wadanda sunfi n baya girma daban tsoro

madubin ya sake nuna wasu acan gaba suma

sunfi na baya harsaida madubin ya nuna

kabilar dodanni kala biyar wato idan aka hada

dana baya

sunzama kabila bakwai cif cif koda gama ganin

su

sai hankalin sammaru dana ashwarya ya

dugunzuma

nan take sammaru yakira su lubaiku suma suka

gani

awannan lokaci ne yarima yauhana ya farka

daga dogon suman

da yayi

koda yaga kafarsa ta hagu a guntule saiya rusa

ihu

ya fashe da kuka, da kyar sammaru ya

rarrasheshi

ya daina kukan bayan nan sai sammaru ya dubi

jaruman duka

daya bayan daya yace.

https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share

MU HADU A PART i DOMIN JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button