MATSATSUBI LITTAFI NA UKU PART I NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI
MATSATSUBI LITTAFI NA UKU PART I
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI
🤴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️
TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️
https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA....
Yɑku abokan tafiyata ina mai sanar daku cewa gwagwarmayar da muka sha abaya tamkar sharar fage ce akan wacce zamu tunkara agabanmu
ina mai rokonmu damu kara damu kara zage dantse
mucire tsoro da fargabar komai domin matsoraci baya zama gwani
ko wanene ko dan wa
musa aranmu cewa ko mu mutu ko muyi rai
sai mun kai gaci, ku tuna cewa akwai sauran
aiki agabanmu don haka zamanmu anan tamkar hutun jaki da kaya aka ne
ina mai umartarmu damu tashi mu kara gaba
ba zamu tsaya ako'ina ba harsai mun karar da dukkannin dodannin dake cikin wannan daji
koda sammaru ya zo nan azancensa saiya zare takobinsa ya dagata sama
yayi kururuwa
irin wacce ke firgita maza afilin daga
nantake kururuwar tasa
ta cika dajin harda amsa kuwwa izuwa nesa
al'amarin daya janyo hankalin sauran kabilun dodannin
kenan suka san cewa lallai yau sunada baki
don haka sai kwadayi ya kamasu, suka fara tande baki
suna dalalar da yawu akasa,
lokacinda yarima sammaru suka gama rurinsu
don karawa kansu kaimi da kuzari sai suka dane bayansu guluz
sukaci gaba da tafiya a sama cikin tsananin gudu
aikuwa cikin kankanin lokaci suka riski kabilar dodanni ta uku
ana haduwa yaki ya barke akayi dauki ba dadi
wohohoho
awannan rana rayuka sun salwanta, jini kuwa ya malala
don saida ya zamana koramai da fadamomin dajin
sun rine sun zama jini maimakon ruwa
awannan gumurzun da akayi ne da kabilar dodannin ta uku yarima lubaiku ya rasa rayuwarsa
domin saida dodannin sukayì walima da sassan jikinsa
ba'a samu komai ba daga barin jikinsa hatta gashin kansa
saida suka cinye tabbas awannan lokaci su yarima sammaru
sunga tashin hankali irin wanda basu taba ganiba
alokcinne aka cirewa boka karluz kunnuwansa aka cinye
shikuwa yarima larbuz saida ya rasa 'yan yatsun hannunsa na hugu
babu wanda ya bada mamaki kamar yarima lauhana domin
duk da kasancewar kafarsa daya zamewa dodannin alakakai
yayi musu muguwar barna domin saidaya kashe sama da guda dubu uku shi kadai
kuma har aka gama yakin saidaya sami rauni ajikinsa
inbanda sammaru da ashwarya babu wanda bai samu mugun rauni ba a wannan yakin
bayan an gama yakin ne su duka suka zauna suka fashe da kuka
bisa tunawa da irin mutuwar da yarima lubaiku yayi
gaba dayansu sai jikinsu yayi sanyi hankalinsu ya dugunzuma
kowa zuciyar sa ta fitar da rai ga rayuwa
kuma sukayì nadamar baro kasashensu da sukayì
don cika wannan buri nasu mai matukar hadari
anan ne dare ya riskesu kuma yunwa d kishirwa
ta addabesu bisa dole aka kunna wuta aka zagayeta anajin dumi
saboda hunturun sanyin dake kadawa sannan aka fara
tunanin yadda za'a samu abinci da ruwan sha
tunda shi kansa ruwan dake dajin ya zama jini
anacikin yin shawarane boka karluz ya dubi aljani guluz yace
kune aljanu ina dabara? ko zakuje kudan zagaya
ku samo mana abinci da abinsha?
guluz yace haba bakaji kunyaba ka fadi haka
ka tuna cewa kai bokane zaka iyayin tsafi abinci da abinsha su bayyana nantake
karluz ya daka masa harara yace
baka da hankali, ai kasanma idan na mayi tsafin wani aljaninne zai kawo
kasan kuwa babu wani aljani dazai iya shigowa
cikin jejin nan don ya tabbatar da cewa halaka zaiyi
ai kawai ku cire tsoron komai kuje ku samo mana abinci
abinci dai idan kukayi hakuri mun kusa rabuwa daku
tunda saura jeji biyu kacal mu iso takiyar duniyar nan
cciki damuwa da tsoro boka guluz yace
shikenan
munyarda zamuje mu nemo muku abinci amma ka duba
mana cikin madubin tsafinka inda zamuje mu nemo muku abinci
batareda munsha wahalaba ko mu afka cikin bala'i
boka karluz ya bushe da dariya yace
oh! waiyau aljani ne da tsoro kamar farar kura
nandanan ya fiddo madubin tsafinsa ya ajiye a kasa
ya shafeshi
saiga hoton wata katuwar barewa kwance acikin wani rami
acan gaba kadan daga inda suke zaune yanzu
kuma abayan ramin wata korama ruwa na gudu
acikinta mai kyau da haske wanda jini bai gurbatashiba
agaba daya harabar wajen babu alamar dodanni
koda ganin haka sai aljani guluz ya dubi aljani amzil
da hurus yace maza kuje ku dauko barewarnan
kuma ku debo ruwan koramar nan isasshe
ku kawo musu, kafin ya gama rufe bakinsa
tuni su amzil sun bace, saida dakika dari uku da sittin ta wuce
amma basu dawoba, al'amarin daya tayarda hankalin kowa kenan
gimbiya ashwarya tace
kai jama'a ruwafa baya tsami banza
lallai akwai abindaya faru ga su amzil donya kamata ace sun dawo
tun dazu, kodajin haka sai boka karluz yace
kwarai kuwa hakane kinyi gaskiya
amma bara mu duba muga halinda akeciki
cikin sauri ya sake fiddo madubin tsafinsa ya ajiye akasa ya shafe shi
saiga hoton aljani amzil shikadai
asama daukeda barewa da kumA ruwa
acikin babbar batta
duk jikinsa jina jina yana tafe yana kayi asaman kamar zai fado kasa
koda ganin haka sai Hankalin su ta sake dugunzuma
ba'a jimaba saiga aljani amzil ya fado agabansu
yana kakarin mutuwa nanfa kowa ya manta da batun yunwa da kishirwa
akazo kan amzil aka tsaya
aljani guluz ya tallafo kan amzil ya dora akan cinyarsa
yana mai kallon fuskarsa yace
yakai dan uwana mai ya faru gareku kaida hurus na ganka cikin wannan hali
cciki matukar karfin hali amzil yace
yakai guluz kayi sani cewa alokacinda
muka shiga cikin kogon nan
don kama barewarnan bamu fuskanci matsalar komai ba
har muka fyadeta ta mutu sai bayan mun fito daga cikin kogon
sai kawai mukaga wasu irin dodanni sunyi mana kawanya
kafin mu yunkura sunfara kai mana cafka
mukuwa saimuka fara kokarin ceton kanmu
inaji ina gani suka kama hurus suka dinga yaga jikinsa
sunaci saida suka cinyeshi tas, nikuwa dama iyakar karfina nake yakarsu
dayake su biyarne kacal saina zame musu alakakai
kasancewar nafisu karfi saida suka kusan hallakani
dakyar ma samu na tsere musu, koda yake tsiran banza nayi don na tabbatar mutuwa zanyi
yakai guluz ina mai rokonka daka kula da matata
idan har kana da sauran kwana aduniya kuma ka sami damar komawa gida
kasani cewa matata tana da tsohon ciki
haihuwa yau ko gobe
idan ta haihu lafiya kuma ta sami da namiji kasa masa sunana
idan kuwa macece asamata suna muddarul ikisina
don ta zamo abin tunawa da iyakar rayuwata
koda amzil yazo nan azancensa sai idanunsa
suka kafe, komai na jikinsa ya daina motsi
guluz ya rungume gawar amzil ya fashe da kuka
al'amarin daya karya zuciyar sauran aljanun kenan
wato karmash, karfil, da azgar suma suka kama kuka
saida aka dan jima ana alhilin wannan mutuwa ta aljani amzil
sannan aka gasa naman barewar nan kowa yaci ya koshi
akasha ruwa, daga nan sai yarima sammaru ya tashi
ya koma gefe daya ya zauna yana mai tunanin gida
koda ya tuno da mahaifinsa sarki alyasil buhus
ya tuno halin daya baroshi na kamuwa da cutar mutuwar rabin jiki
saiya fashe da kuka, sammaru ya sake tuno lokacinda mahaifiyarsa
ta rungumeshi tana kuka
sa'adda da suke bankwanan rabuwa
kawai saiya rushe da kuka
al'amarin daya jefa gimbiya ashwarya cikin tausayi kenan
ta taho ga sammaru da zuwa ta zauna dafdashi
ba tareda ta kalli fuskarsa ba tace
yakai abokina kayi sani cewa
aduniya babu abindaya fi dadi sama da zama da masoyi
tabbas nasan kana tunanin iyayenka ne
'yan uwanka, danginka da kasarsu
shine sanadin wannan kuka naka
kayi sani cewa nima na kasance acikin irin wannan tunani naka
kuma duk da kasancewata 'ya mace ban bari
kukana ya fito filiba
amma nayi na zuci harnagaji, inason mu kasance masu hakuri
domin ya zama wajibi agaremu
koda ashwarya tazo nan azancenta sai yarima sammaru ya dago kai
ya dubeta inda yaga kwallah cike a idanunta
nan take yaji tausayi da kaunarta sun dabaibaye zuciyarsa
baisan sa'adda ya saki murmushiba agareta
jim kadan sukayi shiru su biyu dayansu bai ce uffan ba
daga can sai sammaru ya katse shirun
da cewa
yake kawata hakika tun lokacinda na baro gida naji ina cikin kadaici
fargaba da rashin kwanciyar hankali
amma kuma sanda na farajin kalamanki sai naji duk wadannan abubuwa sunyi kaura daga gareni
aduk sa'adda na kalleki ko naji muryarki
sainaji kamar ina cikin gidanmu ne
tareda iyayena da 'yan uwana
tabbas duk wanda ya sami mace kamarki mai dadadan kalamai
masu tausasa zuciya ya gama morewa don ko abakin
kura yake bazaiyi fargaba da bakin ciki ba
koda yarima sammaru yazonan azancensa sai ashwarya taji wani irin farinciki ya baibayeta
take itama taji ta kamu da tsananin kaunarsa
batasan sa'adda ta kura masa ido ba
harsuka shagala da kallon juna
duk wannan abu dake faruwa larbuz, yauhana, da karluz nadaga can gefe suna kallo.
https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share
MU HADU A PART J DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️
Najibullahi Muhammad
#LEGENDs.