Ya ɗauki ƴata da niyyar saya mata biskit amma ya yi mata fyaɗe'

Ya ɗauki ƴata da niyyar saya mata biskit amma ya yi mata fyaɗe'





Shugaban Saliyo Julius Maada Bio ya fito ya ayyana dokar ta-ɓaci kan fyaɗe da kuma cin zarafi a 2019. Shekara biyar bayan nan, Sashen Binciken Ƙwaf na BBC Africa Eye ya yi duba don gano ko waɗanda ake ci wa zarafi na samun adalci.

Gargaɗi: Wannan labari na ɗauke da bayanai da za su iya tayar da hankalin mai karatu

A birnin Makeni mai nisan sa'a uku daga gabashin Freetown, babban birnin Saliyo, wata mata ce ke zaune a wajen gidanta tare da ƴarta mai shekara uku.

Anita, wanda ba shi ne asalin sunanta ba, ta kwatanta wata rana a watan Yunin 2023 lokacin da ta ga jini na zuba daga jikin ƴarta.

"Na yi wa wannan mata aiki, kuma a ranar wata Asabar, ta aike ni zuwa kasuwa," in ji Anita, inda ta ƙara da cewa a nan ne ta bar ƴar tata a wajen uwar ɗakinta mai shekara 22.

"Ya ɗauki ɗiyata, domin ya je ya saya mata biskit da sauran kayan maƙulashe, in ji shi. Karya yake yi."

Wani lokaci, idan matar na tare da ƴarta, mahaifiyar mai shekara 22 za ta riƙa gani tana zub da jini. Ta ɗauke ta zuwa asibiti inda bayan gwaje-gwaje, aka tabbatar da cewa an yi mata fyaɗe.

"Ma'aikatan jinya sun fara duba yarinyar, kuma sun ce: 'Wayyo Allahna, me mutumin nan ya yi wa wannan yarinyar?' In ji likitan da ke kula da ƴata."

Anita ta garzaya zuwa wajen ƴansanda sai dai matashin ya tsere kuma tsawon shekara ɗaya, sun ƙasa gano inda yake.

"Shugaban ƙasa ya kirkiro da doka don a kama tare da tura duk wanda ya yi fyaɗe zuwa gidan jari," in ji ta, inda ta nuna ɓacin-rai ganin cewa babu abin da aka yi kan hakan har yanzu.

Tana magan ne kan wata dokar cin zarafi mai tsauri da aka kirkiro shekara biyar da suka wuce, bayan da shugaba Maada Bio ya ayyana dokar ta-ɓaci kan fyaɗe.

Hakan ya biyo bayan zanga-zanga da ta ɓarke a watan Disamban 2018, inda ɗaruruwan mutane sanye da fararen riguna da aka rubuta "A bar ƴaƴanmu mata" suka yi maci a faɗin Freetown, babban birnin Saliyo.

Labarin sake yi wa wata yarinya fyaɗe ya girgiza ƙasar; wata yarinya ƴar shekara biyar wadda fyaɗen ya janyo wani ɓangare na jikinta daga kwankwaso zuwa ƙasa ya daina aiki.

Ƴan jarida na ruwaito a lokacin cewa fyaɗe da cin zarafin na jima'i ya ninƙa cikin shekara ɗaya a ƙasar, wanda kashi uku ya kasance kan yara. Lamarin ya yi kamari a Saliyo.

Ayyana dokar ta-ɓaci ta tsawon watanni huɗu daga Febrairun 2019, ya bai wa shugaban ƙasar damar karkata kuɗaɗe zuwa ɓangaren domin daƙile batun cin zarafi na jima'i.

Garanbawul ɗin dokar cin zarafin jima'i ya janyo ɗaukar tsauraran hukunci kan waɗanda suke aikata laifin.

An ƙara hukuncin laifin aikata fyaɗe zuwa ɗaurin shekara 15, ko kuma rai-da-rai idan aka yi wa yarinya. An kuma kirkiro da wata kotu kan batun cin zarafin jima'i a Freetown a shekara ta gaba, domin samun yanke hukunci cikin sauri.

An ga alamun samun ci gaba - rahotanni kan zargin aikata fyaɗe da kuma cin zarafi na jinsi ya yi ƙasa da kusan kashi 17 daga sama da 12,000 a 2018 zuwa 10,000 a 2023, a cewar alkaluman ƴansanda.

Daga cikin abubuwan da suka janyo raguwar hakan shi ne ƙara wayar da kai da kuma yin abin da ya kamata, sai dai tabbatar da ganin cewa mutane, irin ɗiyar Anita sun samu adalci, shi ma wani abu ne da ya kamata a yi.

Wata ƙungiya mai zaman kanta Rainbo Initiative, da ke aiki da waɗanda aka yi fyaɗe, ta ce shari'o'i kan fyaɗe kashi biyar ne kaɗai cikin 2,705 suka samu damar kai wa Babbar Kotu a 2022.

Ɗaya daga cikin batutuwan shi ne samar da kuɗaɗe ga waɗanda ya kamata su ɗabbaka dokar.

A can ofishin ƴansanda a Makeni inda Anita ta kai rahoton fyaɗe da aka yi wa ƴarta, Assnt Supt Abu Bakarr Kanu wanda ke jagorantar Sashen Taimakawa Iyalai (FSU), ya ce suna samun rahotannin aikata fyaɗe kan yara kusan sau huɗu a kowane mako.

Babban kalubale shi ne tawagarsa na fuskantar matsalar rashin kuɗin tafiye-tafiye domin zuwa kama waɗanda ake zargi da aikata laifin fyaɗe.

Shi yake kula da dukkan ofisoshin ƴansanda guda bakwai na yankin, kuma babu wadda ke da abin hawa ko guda ɗaya a cikinsu.

"Akwai lokutan da ga waɗanda suka aikata laifin a fili, amma saboda rashin ababen hawa ba za ka iya kai wa gare su ba domin kama su," in ji Mista Kanu.

"Yin abin da ya kamata a lokacin da ya kamata shi ne kalubale."

Shi, kamar sauran mutane a Saliyo, sun nuna farin ciki da irin matakin da gwamnati ta ɗauka bayan ayyana dokar ta-ɓaci.

"Muna da isassun...dokoki masu kyau da kuma tsare-tsare, sai dai yanayin aiki da kuma jami'ai sune kalubale gare mu wajen ganin mun shawo kan matsalar cin zarafin jima'i da kuma na jinsi a Saliyo."

Ko da an kama wanda ake zargi, kai su wurin alkali shi ne ma babban kalubale da ake fuskanta.

Domin ganin an saurari karar wanda ake zargi da aikata fyaɗe, akwai mutum ɗaya tilo da zai sanya hannu a takardu a ƙasar - shi ne babban attoni janar. Zai sanya hannu ne domin shari'ar ta yi sauri da kuma zuwa kotu, sai dai abin ya zamo alaka-kai.

"A halin yanzu babu wani jami'in tsaro da zai sa hannu kan takardar tuhumar cin zarafi," in ji Joseph AK Sesay, wani lauya da ke yi wa gwamnatin ƙasar aiki.

"Kamar yadda dokar 2019 da aka yi garambawul ta bayyana cewa attoni janar ne kaɗai zai iya sanya hannu kan takardar tuhuma. Hakan ya zama kalubale idan aka zo ga batun kai waɗanda ake zargi zuwa kotuna."

Ministan yaɗa labarai Chernor Bah, ya bayyana cewa wannan tsari ba shi ne daidai ba, amma "Tsari ne da za mu ci gaba da inganta shi".

Da aka tambaye shi cewa ci gaba kaɗan aka samu idan aka zo ga batun yi wa waɗanda aka yi fyaɗe adalci, ya ce "haka wasu al'ummomi ke ji".

Sai dai ya yi watsi da batun cewa babu wani ci gaba da aka samu.

"Ina ganin sauye-sauye da muka yi sun yi tasiri. Sabbin dokokin na nan a ƙasa. ina kuma ganin matakai da aka ɗauka, sun janyo cewar ba ma cikin irin wahalar da muka shiga a shekarar 2019."

Ga Anita, da ke can a garin Makeni, yanzu an ɗauki tsawon shekara ɗaya da yi wa ƴarta fyaɗe.

Ba ta samu wasu sabbin bayanai ba daga wajen ƴansanda, don haka ta karkata ga wallafa hotunan wanda take zargi da yi wa ƴarta fyaɗe a shafin Facebook.

"Ina son mutane su taimaka min wajen neman mutumin. Na ɗimauta kuma ba na cikin farin ciki. Abin da ya faru da ƴata, ba na son ya faru kan kowace ɗiya."
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url


';