Kamfanin Binance: Wasu Macuta Ne Na Kusa Da Gwabnatin Nigeria Suka Buqaci Mu Biyasu Cin Hancin Naira Billion Dari Biyu Da Goma (210 Billion Naira) Ko Mubarak Kasar Cewar Shugaban Kamfanin


Kamfanin Binance: Wasu Macuta Ne Na Kusa Da Gwabnatin Nigeria Suka Buqaci Mu Biyasu Cin Hancin Naira Billion Dari Biyu Da Goma (210 Billion Naira) Ko Mubarak Kasar Cewar Shugaban Kamfanin. 


Naji kunya kwarai da gaske da naga kalaman Richard Teng akan wasu mahukuntan Nigeria da abinda aka yi musu a Nigeria.

   ~ Wasu mutane da suka bayyana kansu cewa su wakilan Gwamnati ne ko wakilan House of Representatives sun nemi Binance ta biya Dala Miliyan 150 ta bayan fage, wato Naira Biliyan 210, idan Binance ta biya za'a warware matsalar da take fuskanta kuma za'a bata dama tayi operating a Nigeria yadda ya kamata, amma ana so su biya 210 Billion Naira din ne ta cikin Crypto ba ta Account din Gwamnatin kasar ba.


Binance suka ce ba kudi ne damuwar su ba, 210 Billion Naira sunfi karfin wannan kudin, amma abinda suke so shine ayi abun in a legal and formal way, sai mutanen suka ki ayi haka. Ana zargin wasu 'yan Majalisu ne da wasu na kusa da fadar shugaban kasa.

   ~ Bayan Binance taki biyan Kudin, tace sai dai ayi a rubuce, kuma a fitar da takardar public kowa a kasar ya gani, sai wadancan mutanen suka ce tunda Binance taki bayar da wancan kudin toh zata gani.


A lokacin sai aka sa wasu mutane ko jami'an tsaro suka kama su aka kulle, biyu daga cikin suka tsere daga baya, dayan su kuma har yanzu ana rike dashi fiye da kwana 70.

   ~ Ana zargin wadancan mutanen suka ingiza Gwamnati, suka hura wuta kuma suka dauki nauyin jefawa mutane cewa Binance ce take da alhalin tsadar kayan Abinci, tsadar Dala da sauran su.


Takarda aka turawa Binance cewa ta turo wakilan ta ana son zama dasu a Nigeria sai ta turo, daga nan ne aka kwace passport dinsu, aka hana su fita daga kasar.

   ~ Shugaban Binance Rich Teng yace mutanen da suka tare wakilan su sun basu warrant of arrest cewa za'a kama su, yace sun san cewa wadannan mutanen basu da hurumin kawo musu warrant of arrest. Richard Teng yace zasu kalubalanci abinda aka yi musu a Kotu a Nigeria ta hannun Lauyoyin su na Nigeria tare da batun daure wakilin su na tsawon kwanaki fiye da 70 zuwa yanzu.


Bayan an shafe wata biyu ana zargin Binance da karya darajar Naira da kin bin dokokin Nigeria, daga karshe dai sabon shugaban Binance Mista Richard Teng ya fito karara ya bayyana hakikanin abinda ya faru a tsakanin Binance da hukumomin Nigeria (ta bangaren su Binance).

   ~ Richard Teng yace bai kamata suyi shiru ba domin an cutar dasu kuma anyi musu karya da sharri sannan ana binsu da makirci, dan haka shi da kansa yayi magana ba ta bakin Spokeman dinsa ba.


A takaice:

1. Richard Teng yace:

Gwamnatin Nigeria ta gargadi 'yan kasar su kauracewa Kamfanin "Binance Nigeria Limited", yayin da Binance suka tabbatar da ba su suka yi register da wannan sunan a CAC ba.


Sun nemi a fito da sunan wadanda suka yi Rijistan anki.


2. Sun cike ka'idar hukumar SEC amma Anki ayi musu reply cewa registration dinsu yayi ko baiyi ba, sunyi zama da Financial Intelligence Unit, duk don subi dokokin Nigeria sau da kafa.

   ~ Richard Teng yace wakilan su sun zauna da EFCC akan yadda za'a kaucewa cutan mutane ko cin hanci ko boye Kudin Haram da Binance daga Nigeria.


3. Yace an nemi su bayar da Naira Biliyan 210 a boye ta cikin Crypto.


Ta yaya Binance zata biya wannan kudin bayan tasan gwamnatin kasar bata fara karban Kudi ta Crypto ba.

Ta yaya zasu biya kudin bayan anki ayi rubutu, anki yarda a bayyanawa duniya ga abinda aka yi.

Wannan abun kunyar har Washington Post sai data ruwaito. A kasashen waje ana ta magana cewa dama haka Nigeria suke, idan baka biya musu bukatar su ba zasu bika da sharrin da ba zaka iya tsallakewa ba.


Mu abinda muke cewa shine ya kamata gwamnati ta gano su waye suka nemi Binance ta basu Naira Biliyan 210.

Sune mutanen da suka tayar da kiyayya da gaba da 'dora laifin tsadar Dala akan Binance.

   ~ Saboda bukatar su bata biya ba suka dinga bayar da shawarar yadda za'a dakile kasuwannin crypto a Nigeria.


Richard Teng yace idan ance ba'a bukatar su a kasar ko ba za'a basu dama ba zasu hakura, ba zasu ce dole sai anyi dasu a Nigeria ba.

   ~ Amma a sani zasu shigar da kara Kotu kan wadannan zarge zarge da aka yi musu da kama Wakilinsu babu ghaira babu dalili.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url


';