An kama mutum 17 da zargin hada-hadar canjin kuɗi ba bisa ƙa'ida ba a Kano

 SHARED

An kama mutum 17 da zargin hada-hadar canjin kuɗi ba bisa ƙa'ida ba a Kano

..


SP Abdullahi Kiyawa/FacebookCopyright: SP Abdullahi Kiyawa/Facebook

Rundunar ƴan sandan Najeriya, reshen jihar Kano ta kai wani samame kan kasuwar ƴan canji ta Wapa inda ta kama mutum 29 da ake zargi da gudanar da hada-hadar musayar kuɗin waje ba bisa ƙa'ida ba.


Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Fesbuk.


Sanarwar ta ce rundunar ta kai samamen ne tare da haɗin gwiwar jami'ai daga hukumar tsaro ta farin kaya DSS.


A cewar kakakin, mutum 12 cikin mutanen da aka kama daga bisa an sake su bayan da aka gaza gano hujjar da ta tabbatar suna gudanar da hada-hadar ba bisa ƙa'ida ba sai kuma ragowar 17 da aka gano kuɗin CFA kimanin dubu 68 sai kuɗin Rupees 30.


Ƙarin binciken da aka yi ya nuna mutanen 17 da ake zargi suna aiki ne ƙarƙashin wani kamfanin ƴan canji da ba shi da rajista kuma za a gurfanar da su gaban kotu.


Rundunar ta ce tana kai samamen ne domin murƙushe masu hada-hadar canjin kuɗi ba bisa ƙa'ida ba da nufin tsaftace kasuwar musayar kuɗi a Najeriya sannan rangadin bai shafi ƴan canjin da ke gudanar da ayyukansu bisa tsarin doka.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url


';