Nigerian NewsHausa NewsLatest News

Sheikh Gumi Ya Gargadi Kan Yarjejeniyar Samoa: “Manakisar Turawa Ta Wuce Yadda Mutane Ke Tunani”

Sheikh Gumi Ya Gargadi Kan Yarjejeniyar Samoa: "Manakisar Turawa Ta Wuce Yadda Mutane Ke Tunani"

4
Sheikh Gumi Ya Gargadi Kan Yarjejeniyar Samoa: "Manakisar Turawa Ta Wuce Yadda Mutane Ke Tunani"
IMAGES IS NOT OUR COPYRIGHT IS FROM FACEBOOK.COM NOT KUMURYAMEDIA WEBSITE

 

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmed Gumi ya yi gargadi kan yarjejeniyar Samoa da gwamnatin Najeriya ta sanyawa hannu, yana mai cewa akwai boyayyar magana a ciki da ta fiye auren jinsi tsanani. Ya ce ya tattauna da Minista Atiku Bagudu kan lamarin kuma ya gano cewa gwamnati ta rufe ido kan wasu muhimman batutuwa saboda son kudi. Sheikh Gumi ya yi kira ga gwamnati da ta sake duba yarjejeniyar kafin a aiwatar da ita.

Sheikh Gumi Ya Gargadi Kan Yarjejeniyar Samoa: “Manakisar Turawa Ta Wuce Yadda Mutane Ke Tunani”

 

 

Samoa: Sheikh Gumi Ya Yi Martani Kan Yarjejeniyar,

 

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmed Gumi ya yi magana kan cece-kucen da ake yi game da yarjejeniyar Samoa Sheikh Gumi ya ce bayan samun labarin yarjejeniyar ya kira Minista Atiku Bagudu inda ya nemi bahasi kan lamarin Malamin ya ce ya ga yarjejeniyar a bayyane babu auren jinsi amma maganar gaskiya a kunshe akwai maganar

Yadda zaka goge sakonnin damfara a wayarka su daina zuwa kwata-kwata

Sheikh Ahmed Gumi ya yi martani kan yarjejeniyar Samoa da gwamnati ta sanyawa hannu. Sheikh Gumi ya yi gargadi kan lamarin inda ya ce manakisar Turawa ta wuce yadda mutane ke tunani.

 

Wannan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da @el_uthmaan ya wallafa a shafin X a yau Lahadi 7 ga watan Yulin 2024.

 

Malamin ya ce ya duba yarjejeniyar tabbas babu auren jinsi amma akwai ta a kunshe watakila son kudi ya rufewa gwamnatin ido. Ya bayyana cewa idan Turawa ne za su iya yaudararsu babu auren jinsi da zarar an zo karbar kudi sai magana ta sauya.

Yadda Iran ke samun tallafin China wajen kewaye takunkuman Amurka

Sheikh Gumi ya yi gargadi kan Samoa “Daga samun labarin rahoton Daily Trust na cewa an sanya hannu kan yarjejeniyar na kira Minista Atiku Bagudu inda ya tabbatar babu auren jinsi a ciki.” “Ya ce kafin rattaba hannun sun samu ma’aikatu guda uku suka duba suka tabbatar babu abin da ya shafi auren jinsi a ciki.” “Daga baya an turomin yarjejeniyar na gani, maganar gaskiya a bayyane babu amma a kunshe akwai.” “Watakila idon gwamanti ya rufe saboda son kudi ba su kula da hakan ba saboda suna ganin za su yiwa Turawa wayo.”

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim
Back to top button