Latest NewsHausa NewsNigerian News

Muna Buqatar A Raba Jahar Kano Biyu A Baiwa Tiga Jaha Kuma Bama Goyon Bayan Raba Masarautu :Cewar Kawu Sumaila

4

Muna Buqatar A Raba Jahar Kano Biyu A Baiwa Tiga Jaha Kuma Bama Goyon Bayan Raba Masarautu :Cewar Kawu Sumaila

 

Daga: Safiyanu Iliyasu Kumurya

Takun Sen. Suleiman Kawu Suleiman a zauran majalisar dattawa a yan kwanakin nan.

Muna Buqatar A Raba Jahar Kano Biyu A Baiwa Tiga Jaha Kuma Bama Goyon Bayan Raba Masarautu :Cewar Kawu Sumaila
Muna Buqatar A Raba Jahar Kano Biyu A Baiwa Tiga Jaha Kuma Bama Goyon Bayan Raba Masarautu :Cewar Kawu Sumaila

A satin da ya gabata, Kawu sumaila ya mike a zaurensu na majalisar dattawan Nigeria domin jaddada goyon bayansa da murnar sa akan kudurin da Hon. Kabiru Alhassan Rurum ya kai zauren majalisar tarayya na samar da Federal Polythecnic a garin Rano. Da yake jawabia gavan majalisar ta su, Kawu Sumaila ya bayyana garin Rano a matsayin Headquater yankinsa na kano ta kudu mai dauke da kananan hukumomi goma sha shida, kuma yanki mai dauke da kiyasin mutane milyan biyar da mazabu dari da saba’in da daya. Babban abin da ya kuma jan hankalin al’umma shine yadda kawun ya sake tunantar da zauren majalisar dattawa cewa “……..I repeat, Rano is also the Headquater of RANO EMIRATE COUNCIL….” Ma’ana dai cikin hikima da dattako Kawun yana fadawa duniya matsayarsa ne cewa su har yanzu Rano tana nan a matsayin masarautar su, kuma bisa ga dukkan alamu Sanata Kawu baya tare da matakin rusa masarautu da gwamnatinsu a matakin jiha tayi, kuma hakan kamar nuni yake da cewa yana tare da umarnin kotu.

 

A yau kuma Sanata Kawun ya sake shigar da kudurin samar da sabuwar jihar TIGA. wanda idan bukatar Kawun ta samu nasara fa, magana ake ta raba jihar kano zuwa gida biyu, ba ma wai batun raba wata Masarauta ba. Kuma muddin hak’an Kawun ya cimma ruwa to fa bisa ga alamu Masarautar Rano zata zama Headquater Jihar TIGA domin ba zai yuwa ace Masarutun wata jihar suna karkashin ikon gwamnatin makwabtanta ba. Hakazalika kudurin Kawun na nufin za’a samarwa da Gwamnan kano karin abokin aiki a cikin gwamnonin Nigeria kamar yadda aka samar da Gwamnan jigawa bayan da aka yakice jigawa daga jihar kano. Kuma za’a sake fasalta rabon arzikin kasa a diba daga Kano a bawa Mutanen Jihar Tiga nasu kason domin su gina yankinsu.

 

Lallai a yau gogewar siyasar Kawu Sumaila ta sake bayyana a duniya. Da wannan muke kira ga al’ummar da suke farin ciki da Samun Jihar TIGA da su taya Kawun da addu’a domin tabbas zai gamu da kalubale musamma

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Leave a Reply

Back to top button