Yadda Iran ke samun tallafin China wajen kewaye takunkuman Amurka

 Yadda Iran ke samun tallafin China wajen kewaye takunkuman Amurka

Ƙasar Iran ta ƙaddamar da harin jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami fiye da 300a kan Isra'ila, a tsakiyar watan Afrilu, wani abu da ya ƙara yawan kiraye-kirayen ƙara ɗaukar matakai masu tsauri kan man da ƙasar ta Iran ke fitarwa wanda shi ne ƙashin bayan tattalin arziƙinta.

Duk da matakan da ake ɗauka a kan Iran, amma yawan man da ƙasar ke fitarwa a farkon wannan shekarar ta 2024 ya fi na kowane lokaci a tsawon shekaru shida, inda ta fitar da man na tsabar kuɗi dala biliyan 35.8, kamar yadda shugaban hukumar hana fasaƙauri na Iran ɗin ya shaida.

Yanzu dai abin tambaya shi ne ta yaya aka yi Iran ta samu damar kewaye takunkuman da aka ƙaƙaba mata?

Amsar wannan tambaya na tare da dabarun kasuwanci da ƙasar China take ɗauka- ƙasar da ta fi kowace ƙasa yawan sayen man Iran ɗin, inda take sayen fiye da kaso 80 na man Iran da ya kai yawan ganga miliyan 1.5 a kullum, kamar yadda wani rahoto na Kwamitin Kuɗaɗe na Amurka ya shaida.

Me ya sa China ke sayen mai daga Iran?



Kasuwanci da ƙasar Iran na da nasa haɗarin - takunkuman da Amurka ta ƙakaba - ke nan ko me ya sa China ta kasance ƙasar da ta fi kowacce a duniya sayen man Iran?

Kai tsaye za a iya cewa saboda man ƙasar Iran na da araha kuma yana da kyau.

Yanzu haka farashin man a kasuwar duniya na tashi saboda halin rikici da duniya ke fuskanta, to amma Iran, na nuna zaƙuwa ta sayar da man nata da aka sanyawa takunkumi, ta hanyar farashi mai rahusa.

Wani rahoto da aka samu bisa dogaro da alƙaluma daga 'yan kasuwa da masu bibiyar jiragen mai da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya tattara a watan Oktoban 2023, ya nuna cewa China ta samu ragin kuɗin da ta ajiye kusan dala biliyan 10 a watannin taran farkon shekarar 2023 ta hanyar sayen mai daga ƙasar Iran da Rasha da Venezuela waɗanda dukkannin su ke sayarwa a farashi mai rahusa.






Farashin ɗanyen man fetur a kasuwar duniya na sauka da hawa, to sai dai yana ƙasa da dala 90 a kan kowace ganga.

Homayoun Falakshahi, babban mai fashin baƙin alƙaluma a kamfanin Kpler ya ce Iran na sayar da manta bisa farashi mai rahusa na ragin dala biyar. A bara, wannan ragin ya kai dala 13 a kan kowace gangar ɗanyen mai.

Akwai siyasa da ɓangaranci da ke taka rawa in ji mista Falakshahi.

“Iran na tsakiya a yanayin da ake ciki tsakanin Amurka da China,” ya ƙara faɗi.

Ta hanyar tallafa wa tattalin arzikin Iran, "China ta ƙara siyasa da ɓangaranci da kuma ƙalubalen soji ga Amurka a yankin Gabas ta tsakiya, musamman yanzu da rikici ke ƙaruwa da Isra'ila." Ya ƙara da bayani.

‘Ƙananan matatun mai’
Masu fashin baƙi sun yi amanna cewa Iran da China sun gina wani tsari na kasuwancin man Iran da ke fama da takunkumi a tsawon shekaru.

"Manyan abubuwan da ke cikin wannan tsari na kasuwanci su ne "ƙananan matatun man China da jiragen dakon mai da kuma rumbunan ajiyar mai na ƙasar China da ƙasashen waje ba su san da su ba sosai," in ji Maia Nikoladze, mataimakiyar darektar majalisar tattalin arzikin ƙasashen Atlantic ta shaida wa BBC.

Matatun da ake tace man ƙasar Iran ƙanana ne kuma waɗanda ba na gwamnati ba ne kai tsaye da su ake amfani maimakon na gwamnati.

Ana kiran su da suna "teapots" waɗnda kalmomi ne na masana'antar mai, in ji Mr Falakshahi, saboda " matatun sun yi kama da butar shayi inda suke da kayan aiki taƙaitattu da ke yankin Shandong a kudu maso gabashin Beijing."

Waɗannan ƙananan matatun na da ƙarancin matsaloli ga ƙasar China idan ka haɗa su da kamfanonin gwamnati da ke aiki ga ƙasashen duniya da kuma buƙatar aiki da tsarin kuɗaɗen Amurka.

"Ƙananan matatun mai masu zaman kansu waɗanda ba sa gudanar da ayyuka a wasu ƙasashen, ba sa cinikayya da dala saboda haka ba sa buƙatar kuɗaɗen ƙasashen waje domin yin mu'amilar cinikayya," kamar yadda Mista Falakshahi ya shaida wa sashen BBC na Persia.

‘Jiragen da ba iya bin sahunsu’



Ana iya bin sahun jiragen dakon mai a tekunan faɗin duniya ta hanyar wata manhaja da ke sa ido kan wurin da suke da yanayin tafiyarsu da kuma inda za su tsaya.

Domin gudun bin sahun jirgin, Iran da China na amfani da "jiragen da ba a iya tantance mamallakansu waɗanda kuma ba sa bayar da bayani na takamaiman wurin da suke," in ji Mis Nikoladze.

"Za su iya kewaye jiragen dakon man ƙasashen yammaci, da ayyukan dako da dai sauran su. Ta hakan ne, ya sa ba lallai ba ne su bi dokokin yammaci da suka haɗa da takunkumi," ta ƙara haske.

Waɗannan "jiragen na ɓaddami" da ke cire tsarin bin sahunsu domin gigita masu ƙoƙarin bin sahun nasu.

An haƙiƙance cewa jiragen ɓandamin na yin juye a tsakaninsu ta hanyar 'yan ƙasar China da ke tekunan duniya, a wajen wuraren da aka amince a yi juyen, kuma wasu lokutan ma ana yin juyen ne a yanayi maras kyau domin ɓoye ayyukan inda hakan zai zama abu mai wahala a gano da inda man yake.

Mista Falakshahi na Kpler ya bayar da shawarar cewa irin wannan juyen da ake yi na faruwa ne a kudu maso gabashin ruwan yankin Asiya.

“Akwai wani wuri da ke gabashin Singapore da Malaysia da tuntuni ya kasance wurin da ake samun jiragen dakon mai da ke zirga-zirga kuma suke yin juye a junansu."

Abu na gaba kuma shi ne fagen "kwaskwarima".

ta wannan hanya kamar yadda mista Falakshahi ya bayyana cewa " jirgi na biyu na tafiya daga ruwan Malaysia zuwa arewa maso gabashin China domin kai ɗanyen man. Manufar ita ce nuna cewa man ba daga ƙasar Iran yake ba domin nuna daga wataƙila ƙasar Malaysia yake."

Hukumar da ke tattara bayanai kan makamashi ta Amurka, EIA, ta nuna cewa alƙaluman hukumar hana fasaƙauri sun nuna cewa China na shigar da kaso 54 na ɗanyen mai daga Malaysia a 2023 fiye da 2022.

Lallai, yawan man da aka rawaito Malaysia na shigarwa zuwa China ya wuce yawan man da take samarwa, in ji mai sharhi Nikoladze, "wanda hakan ne ya sa aka yi amanna cewa Malaysia na shigar da man daga ƙasar Iran".

Akwai rahotanni cewa jiragen man Iran da Malaysia da Indonesia suka ƙwace saboda yin abin da ya saɓa da dokar "juyen mai ba bisa ƙa'ida ba" a watan Yuli da Oktoban bara

Ƙananan jirage


Maimakon tsarin kuɗaɗe da ƙasashen yammaci ke bibiya, Maia Nikoladze ta fayyace cewa hada-hadar ana yin ta ne ta hanyar amfani da ƙananan jiragen ƙasar China.

“China na sane da hatsarin da ke tattare da sayen man ƙasar Iran da aka sanya wa takunkumi, wani dalili da ya sa ba ta son shigar da manyan jiragenta a cikin hada-hadar," kamar yadda ta ce.

"Maimakon hakan, sai take amfani da ƙananan jiragenta da ba a san su a ƙasashen duniya ba."

Sannan an yi amannar cewa ana biyan Iran ɗin kuɗn man ta hanyar amfani da kuɗin ƙasar China domin zagayewa tsarin hada-hadar da ake yi da dalar Amurka.

“Za a kuɗin ne a asusun bankuna da ke China da ke da alaƙa da ƙasar Iran," in ji Mr Falakshahi. “Daga nan kuma sai a yi amfani da kuɗin wajen sayen kayayyaki a China sannan kuma tabbas wasu kuɗaɗen za su koma Iran ɗin.

“To amma dai abun a faifaye yake wajen gano yadda ake wannan hada-hadar sannan kuma ana tantamar ko ƙasar Iran na iya kai dukkan kuɗaɗen gida," ya ƙara da bayni.

Wasu rahotanni na nuna cewa ƙasar Iran na amfani da amfani hanyoyin musayar kuɗi a cikin gida domin gujewa gano hanyoyin samun kuɗaɗen.

Tsoron tashin farashin mai
A rsanar 24 ga watan Afrilu, shugaban Amurka, Joe Biden ya rattaba hannu kan wani tallafi ga Ukraine wanda ya haɗa da faɗaɗa takunkumi ga harkokin man ƙasar Iran.

Sabuwar dokar ta faɗaɗa takunkuman da suka haɗa da tashoshin jiragen ruwa da jiragen ruwan da matatun mai da suke dako ko kuma sarrafa ɗanyen man Iran, inda suke ƙin sharuɗan takunkuman da Amurka ta sanya wa Iran ɗin.

Harwayau, takunkuman sun hau kan dukkan hada-hadar kuɗaɗe tsakanin Iran da China da bankunan China ke yi da kuma bankunan ƙasar Iran ɗin ke yi wajen sayen abubuwa masu alaƙa da mai.

Falakshahi mai fashin baƙi a Kpler, ya ce ba lallai Amurka ta iya ɗabbaƙa dukkannin abubuwan da za su daƙile abun ba.



Wannan na faruwa ne saboda abin da gwamnatin Biden ta fi bai wa muhimmanci shi ne farashin man fetur a cikin gida. Hakan ya fi tsarin Amurkar na ƙasashen duniya", in ji mista Falakshahi.

Iran ce ƙasa ta uku da ke samar da man fetur a cikin jerin ƙungiyar ƙasashe masu samar da man fetur, sannan ƙasar na samar da kusan ganga miliyan uku a rana ko kuma kimanin kaso uku na yawan man da duniya ke samarwa.

Taɓa harkar samar da man na Iran ka iya shafar tashin farashin mai a kasuwar duniya in ji masana.

“Biden ya san cewa idan Amurka ta rage yawan man da take shigarwa ƙasar da shi daga Iran, hakan na nufin za a samu ƙarancin samar da mai a kasuwa sannan zai ƙara farashin ɗanyen mai a duniya. Idan hakan ya faru, to za a samu ƙarin kuɗin man fetur a Amurka," in ji Mista Falakshahi, inda ya ƙara da cewa wannan abu ne da Biden ka iya gujewa gabanin zaɓen shugaban ƙasa.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url


';