Uncategorized

Wataƙil Tuchel ya je Man Utd, Arsenal na tattaunawa da Gabriel

4

 Wataƙil Tuchel ya je Man Utd, Arsenal na tattaunawa da Gabriel

9221f470 09c9 11ef b9d8 4f52aebe147d

Tsohon kocin Chelsea da ke horar da Bayern Munich Thomas Tuchel na cikin jeren mutanen da za su iya maye gurbin Erik ten Hag idan ya bar Manchester United a wannan kaka. (Times – subscription required)

Amma Tuchel ya dauko hanyar da zai yi wahala idan bai cigaba da zama a Bayern Munich ba bayan wannan kaka, duk da cewa a watan Fabarairun farkon shekara an sanar da cewa zai tafi. (Florian Plettenburg)

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya sa ɗan wasan Newcastle da Sweden Alexander Isak, mai shekara 24, cikin manyan ‘yan wasan da zai shiga farauta. (Independent)

Mai buga gaba a RB Leipzig da Slovenia Benjamin Sesko, ɗan shekara 20, na iya kasancewa zabi ga Arsenal idan ta gaggara samun abin da take so. (Football Transfers)

Arsenal ta shiga tattaunawa da ɗan wasan atsakiya a Brazil Gabriel, mai shekara 26, a kokarin ganin ta sha gaban manyan ƙungiyoyin Turai da ke gogayya da ita a farautar ɗan wasan. (Football Insider)

Mataimakin shugaban Inter Milan Javier Zanetti ya ce ƙungiyar da ke buga Seria A za ta kalubalanci Manchester United da Arsenal a cinikin ɗan wasan Bologna mai shekara 22, Joshua Zirkzee. (Mirror)

Manchester United ta tuntubi wakilin ɗan wasan Faransa Adrien Rabiot, mai shekara 29, wanda kwantiraginsa a Juventus ke karewa a karshen kaka. (Team Talk)

Ɗan wasan Fulham Tosin Adarabioyo, mai shekara 26, na son tafiya Newcastle idan kwantiraginsa ya kare a karshen kaka. (Mail)

Everton na fatan shawo kan Jarrad Branthwaite, mai shekara 21, ya tsawaita zamansa a Goodison Park da shekara guda, sai dai Manchester United na da kwarin-giwar za ta saye shi akan tsakanin fam miliyan 60 zuwa 70.(Football Insider)

Tottenham za ta saurari tayin da aka gabatar mata kan ɗan wasan gaba a Brazil Richarlison, mai shekara 26. (Telegraph – subscription required)

Real Madrid ta gabatar da tayi kan ɗan wasan River Plate mai shekara 16 daga Argentina, Franco Mastantuono. (Fabrizio Romano)

Barcelona ta sa sunan ɗan wasan Arsenal da Ghana Thomas Partey, mai shekara 30, cikin manyan ‘yan wasan da take farauta a wannan kaka. (Caught Offside)

Manchester City na duba yiwuwar saye golan Lazio Christos Mandas, yayinda ita ma Manchester United ta nuna kwadayinta kan ɗan wasan mai shekara 22 daga Girka. (Corriere dello Sport, via Teamtalk)

Daraktan wasannin a Crystal Palace Dougie Freedman na cikin wadanda Newcastle ke duba yiwuwar aiki da shi. (Mail)

Kocin Sporting Lisbon Ruben Amorim na nazari kan Chelsea bayan rashin cimma daidaituwa kan tafiya Liverpool da West Ham. (Mirror)

Inter Miami na tattaunawa da tsohon ɗan wasan Real Madrid da Argentina da ke buga tsakiya Angel Di Maria, mai shekara 36. (ESPN Argentina, via Marca)

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button