Turkiyya ta dakatar da hulɗar kasuwanci da Isra'ila kan yaƙin Gaza

 Turkiyya ta dakatar da hulɗar kasuwanci da Isra'ila kan yaƙin Gaza




Turkiyya ta ce ta dakatar da duk wata hulɗar kasuwanci da Isra'ila dangane da yaƙin da ake yi a Gaza, saboda taɓarɓarewar yanayin jin ƙai a yankin.


An dai yi ƙiyasin adadin cinikayyar tsakanin ƙasashen biyu ya kusan dala bilyan bakwai a bara.


Ma'aikatar kula da harkokin kasuwanci ta Turkiyya ta ce za a aiwatar da matakin har sai Isra'ila ta bayar da damar shigar da kayan jin ƙai zuwa Gaza ba tare da matsala ba.


Kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu ta kai kusan dala biliyan bakwai a shekarar da ta gabata.


Ministan harkokin wajen Isra'ila ya zargi shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan da kasancewa kamar mai mulkin kama karya.


Israel Katz, a shafin X, ya ce Mista Erdogan yana burus da buƙatun al'ummar Turkiyya da na ƴan kasuwa da watsi da yarjeniyoyin kasuwanci tsakanin ƙasashen duniya.


Ya ƙara da cewa ya umarci ma'aikatar harkokin waje da ta samar da wasu hanyoyin kasuwanci da Turkiyya da nufin mayar da hankali kan samar da kayayyaki a cikin gida da kuma shigo da wasu kayayyaki daga wasu ƙasashe.


Cikin wata sanarwa, Turkiyya ta ce dakatar da hulɗar kasuwancin ta shafi duka kayayyaki.


A 1949, Turkiyya ce ƙasar da galibin al'ummarta musulmi ne ta amince da Isra'ila. Sai dai alaƙa tsakaninsu ta yi tsami a shekarun baya-bayan nan.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url


';