Uncategorized

Ten Hag na iya komawa Bayern, Liverpool na da kyakyawan zato a kan Kloop

4

 Ten Hag na iya komawa Bayern, Liverpool na da kyakyawan zato a kan Kloop

39d6b4d0 0a92 11ef b9d8 4f52aebe147d

Kocin Manchester United Erik ten Hag ake tunanin zai maye gurbin Thomas Tuchel a Bayern Munich. (Christian Falk)

Ɗan wasan Liverpool Darwin Nunez, mai shekara 24, ya kasance wanda Barcelona ke hari a wannan kaka domin maye gurbin Robert Lewandowski na Poland mai shekara 35. (Sun)

United na shirin karban tayi kan ɗan wasan Brazil Antony mai shekara 24, yayinda take shirin bada dama ga ɗan wasan Crystal Palace da ke buga tsakiya Michael Olise. (Rudy Galetti)

Arsenal ta cimma yarjejeniyar baka da Brentford kan golan Sifaniya da ke zaman aro David Raya mai shekara 28 domin bashi kwantiragin dindindin na fam miliyan 27. (Fabrizio Romano)

Liverpool na fatan mataimakin kocinsu Pep Lijnders, da ke shirin barin kulob din tare da Jurgen Kloop, za su dawo Anfield a nan gaba. (Mirror)

Manchester United na son amfani da mai tsaron baya Harry Maguire, wajen kwadaita Everton ta sayar musu da ɗan wasanta Jarrad Branthwaite, mai shekara 21a wannan kaka. (Star)

Kocin Palmeiras Abel Ferreira na son shugaban kungiyar Leila Pereira ya datse sayar da ɗan wasan Brazil mai shekara 17, Estevao Willian ga Chelsea, da ta gabatar da tayin yuro miliyan 55. (£47m) offer. (Goal)

Tsohon kocin Chelsea Graham Potter na neman aikin horar da Ajax bayan ya fid da rai da batun maye gurbin Ten Hag a Manchester United. (De Telegraaf)

Getafe ta shiga tattaunawa da Manchester United domin duba yiwuwar cimma yarjejeniya kan dan wasan Ingila mai shekara 22 Mason Greenwood. (The Athletic – subscription required)

Ɗan wasan gaba a Juventus Dusan Vlahovic, mai shekara 24, ya ja hankalin kocin Arsenal Mikel Arteta. (Tuttosport – in Italian)

Mai tsaron baya a Ingila Jarell Quansah na dakon a tsawaita kwantiraginsa bayan nuna bajinta a wannan kaka a Liverpool. (Mirror)

Inter Milan za ta kalubalanci Manchester United da Arsenal kan cinikin ɗan wasan Bologna mai shekara 22, Joshua Zirkzee.

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button