Tarihin Charlie Chaplin (Dan Sauri)


 


Tarihin Charlie Chaplin (Dan Sauri)


Sir Charles Spencer " Charlie " Chaplin KBE ɗan wasan kwaikwayo ne na Ingilishi, mai shirya fina-finai, kuma mawaki. Ya shahara sosai a fina-finan shiru (Silent Movie) ( Fim Wanda babu magana ko sauti). Ya yi aiki, ya ba da umarni, ya rubuta, kuma ya samar da mafi yawansu.


Charlie Chaplin ya kasance dan wasan kwaikwayo kusan Shekaru 70. Ya fara Fim tun yana dan shekara 5, kuma ya yi aiki Har ya kai shekara 80. Acting din da Charlie Chaplin ya fi fitowa Ana kiransa da “The Little Tramp”. “Tramp” mutum ne mai Kyawawan halaye, sanye da riga, da Babban wando, da takalmi, Da gashin baki, da bakar hula.


Haihuwa 


An haifi Charles Spencer Chaplin a ranar 16 ga Afrilun 1889 a birnin Landan na kasar Ingila, Chaplin Bai sami kyakkyawar ƙuruciya da mahaifiyarsa Hannah Hill Chaplin ba, wacce mawaƙiya ce mai basira, 'kuma yar wasan kwaikwayo, da kidan piano, wacce ta shafe yawancin rayuwarta a asibitin Kwakwalwa. Mahaifinsa Charles Spencer Chaplin Sr. ya kasance mawaƙi mai Shaye-Shaye.


Chaplin Ya Girma A Gidan Marayu.


Kamar yadda lafiyar mahaifiyar Chaplin ta tabarbare, haka ma komai Nasu ya tabarbare. Ya yin da lamarin yayi muni sosai a shekara ta 1896 sai aka tura Chaplin da babban ɗan’uwansa zuwa makarantar kwana ta Gwamnati ta marayu da yara marasa galihu.” Chaplin ya shafe kusan watanni 18 a makaranta a wurin. Lokaci mafi tsayi na lokacin da ya taɓa samu yana Karatu. Ya koyi karatu da rubutu amma da alama ya sha fama da wulakanci sosai kuma mai tsanani ciki har da aske masa kai a lokacin da ake fama da ciwon makero. Mahaifinsa, bai taka rawar a zo gani ba a wajen kula dashi kuma ya mutu saboda shaye-shaye yana da shekaru 37.


Zuwansa America 


Chaplin ya fara yin wasa tun yana karami, inda yake zagaya dakunan wake-wake, daga baya kuma ya yi aiki a matsayin dan wasan kwaikwayo na wasan barkwanci. Lokacin da yake kusan goma sha biyu, ya sami damarsa ta farko don yin wasan kwaikwayo kuma ya fito a matsayin "Billy. Yana da shekaru 19, ya sanya hannu da kamfanin Fred Karno, wanda ya kai shi Amurka. An kuma zaɓe shi a masana'antar fim kuma ya fara fitowa a cikin 1914 a kamfanin Keystone Studios.


Chaplin Ya Kyamaci fim dinsa na farko.


A Amurka a cikin 1914, Keystone Studios ya ɗauke shi aiki akan $150 a mako. Ya yi fitowar fim ɗinsa na farko a farkon shekarar 1904, ya fito a fim din Making a Living a matsayin mai zamba, fim din ya samu karbuwa" sai dai kuma ya zargi daraktan da yanke warare masu kyau a Fim din saboda yi masa bakin ciki.


Chaplin da sauri ya zama miloniya.


Chaplin ya koma Kamfanin Essanay Studios a watan Disamba Na 1914, wanda ya ɗauke shi a matsayin "babban ɗan wasan Barkwanci na duniya." Sannan ya sanya hannu da Kamfanin Fina-Finai na Mutual kan dala 670,000 a shekara, bayan da ya Amince ya yi fina-finan barkwanci takwas na First National kan Sama da dala miliyan daya. A ƙarshe, a cikin 1919, ya kafa nasa Ɗakin studio tare da abokansa a fina-finan Hollywood, Douglas Fairbanks, Mary Pickford da DW Griffith. 


Chaplin Ya Ƙi Fim Mai 'Sauti.


An fara fim mai sauti a shekarar 1927, fina-finai masu sauti da sauri suka fara maye gurbin masu shiru takwarorinsu. Amma duk da haka Chaplin ya yi jinkirin yin amfani da sabuwar fasahar, yana fargabar za ta lalata masa Takensa na Little Tramp. A cikin fina-finansa na 1930s guda biyu, "City Lights" da "modern times" Chaplin ya haɗa da kiɗa amma babu magana, sai dai wani yanayi wanda ya yi waƙa a cikin harshen Italiyancin karya marar ma'ana. A ƙarshe, a cikin 1940, ya fito da cikakken fim Mai sauti, Mai Suna "Geat Dictator," ya fito a matsayin Shagube Ga Hitler.


Chaplin Ya Yi Aure Sau Uku.


A cikin 1918 Chaplin ya yi gaggawar ɗaura aure da wata ’yar fim ’Yar shekara 17 Maisuna Mildred Harris, auren da ya yi Nadamarsa ba da jimawa ba, Bayan rabuwar auren, ya auri Lita Gray, ’Yar shekara 16, itama wata ‘yar wasan kwaikwayo ce Wadda suka rabu da ita. Kuma a cikin 1943, Chaplin mai shekaru 54 ya auri Oona O'Neill mai shekaru 18, wanda wani wakilin Hollywood ya hada shi da ita, mahaifin O'Neill, marubucine kuma Dan wasan kwaikwayo, Eugene O'Neill, ya ji haushin yin Auren Har ya hana yar tasa gadonsa, yace babu ita babu shi, amma sabanin sauran Auren da Chaplin yayi wannan Auren ya dore, Su biyun sun kasance tare har zuwa mutuwar Chaplin a Lokacin da Yake Da shekaru 88 kuma su Haifi 'ya'ya takwas.


Da Gaske Ya Bar Amurka 


Duk da zama a Amurka kusan shekaru 40, Chaplin bai taba zama dan Amurka ba. saboda yayi suna a matsayin mai Ra'ayin Kwaminisanci. A lokacin McCarthy, FBI ta sa masa ido, kuma wani dan majalisar Mississippi ya yi kira da a kore shi daga Kasar.


Daga nan sai Gwamnatin Amurka ta soke izinin sake shigar Sa kasar a shekarar 1952 yayin da yayi tafiya zuwa Ingila hutu. Maimakon ya koma ya amsa tuhume-tuhume a gaban hukumar kula da shige da fice ta Amurka, Chaplin ya yanke shawarar kwashe Iyalansa Zuwa Switzerland. Amma daga baya ya sake ziyartar Amurka sau ɗaya kawai, a cikin 1972, don karɓar lambar yabo da Kwalejin (Honorary Academy Award) ta bashi.


Yunkurin kisa


Chaplin dai shi ne aka yi yunƙurin kashewa wanda ya yi sanadiyar mutuwar Firaministan Japan Inukai Tsuyoshi.


A ranar 15 ga Mayun 1932, wasu matasa jami'an sojan ruwa goma sha daya (mafi yawansu sun Haura shekaru ashirin) sun harbe firaminista Inukai Tsuyoshi a gidansa. Asalin shirin kisan ya haɗa da kashe Chaplin wanda ya isa Japan a ranar 14 ga Mayu 1932, a lokacin liyafar Girmama wanda Firayim Minista Inukai ya shirya. Lokacin da aka kashe firaministan, dansa Inukai Takeru yana tare da Charlie Chaplin a wajen kallon wasan kokawa wanda watakila hakanne ya ceci rayukan su, su biyun.


Girmamawar Sarauniya Ta (Sir)


A Rãnar 9 ga Maris 1975, Sarauniya Elizabeth ta biyu ta Bai Charlie Chaplin kyautar Girmamawa Ta (Sir) A Ingila.


Mutuwa


Chaplin ya mutu a ranar Kirsimeti a ranar 25 ga Disamba 1977, a Vevey, Vaud, Switzerland. Ya mutu sakamakon bugun jini a cikin barcinsa, yana da shekaru 88. 


Barayi Sunyi Garkuwa Da Gawar Chaplin.


Bayan ‘yan watanni da mutuwar Chaplin, A Ranar 1 Ga Watan Maris 1978 wasu ‘yan fashi biyu sun sace akwatin gawarsa a makabartar kasar Switzerland inda suka aika wa matarsa ​​bukatar kudin fansa Dala 600,000. Da ta ki biya, sun yi wa ‘ya’yanta barazana. Ba da jimawa ba aka kama ’yan fashin kuma an gano akwatin gawar Bayan Makwanni 11 a Kusa Da Tafkin Geneva, daga nan aka sake binne ta a karkashin dakin din Suminti don Tsoron kada A Sake Sace ta.


Kudin da Ya Mutu Ya Bari


A lokacin mutuwarsa, Charlie Chaplin ya mallaki akalla dala miliyan 100, wanda daidai yake da kusan dala miliyan 400 a Dalar yau.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url


';