Saudiyya da Maroko da Masar sun yi kira a gaggauta tsagaita wuta a yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza.

 Saudiyya da Maroko da Masar sun yi kira a gaggauta tsagaita wuta a yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza. 




Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda a yau ya shiga kwana na 212, ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 34,654 — kashi 70 daga cikinsu jarirai da ƙananan yara da mata — kana ya jikkata fiye da mutum 77,908.

Hare-haren da Isra'ila ta kai Rafah da ke kudancin Gaza sun yi sanadin mutuwar mutane da dama, ciki har da ƙananan yara, a cewar jami'ai a ranar Juma'a./ Hoto: AP

0331 GMT — Za a ci gaba da taro a Masar kan tattaunawar tsagaita wuta a Gaza


Ana sa ran ci gaba da tattaunawa a Masar a ranar Lahadi kan batun tsagaita wuta a Gaza a yayin da Isra'ila ke matsa ƙaimi wurin luguden wuta a kan Falasɗinawa.


Ƙungiyar Hamas ta ce ta yi watsi da duk wata yarjejeniya da ba za ta kawo ƙarshen yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza ba sannan ta zargi firaiminista Benjamin Netanyahu da "yin ƙafar-ungulu" a yunƙurin cim ma yarjejeniyar.


Tun da farko, masu shiga tsakanin na Qatar, Masar da Amurka sun gana da wakilan Hamas a birnin Alƙahira kuma wani babban jami'i na Hamas da ke cikin tattaunawar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa za a gudanar da "sabon zagaye" na tattaunawa a ranar Lahadi.


Masu shiga tsakanin, waɗanda suke nema Isra'ila ta daina kai hare-haren da ta kwashe watanni bakwai suna kai wa a Gaza, sun bayar da shawarar a tsagaita wuta ta kwanaki 40 tare da sakin Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su da kuma Falasɗinawan da ke ɗaure a gidajen yarin Isra'ila.


2233 GMT —Mambobin OIC sun yi kira ga Isra'ila ta yi gaggawar tsagaita wuta a yaƙin Gaza


Saudiyya da Maroko da Masar sun yi kira a gaggauta tsagaita wuta a yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza.


Ƙasashen, waɗanda mambobi ne na ƙungiyar OIC ta ƙasashen Haɗin-kan Musulmai, sun yi kiran ne ranar Asabar a taron da suka gudanar a Banjul babban birnin Gambia.


Taron da suka gudanar na kwanaki biyu mai taken "Yauƙaƙa haɗin-kai da goyon baya ta hanyar tattaunawa mai ɗorewa," yana fatan warware matsalolin da suka addabi duniya, musamman halin da Falasɗinu ke ciki da kuma yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza wanda kawo yanzu ya yi sanadin mutuwa sama da mutum 34,600.


A yayin taron, an bijiro da batutuwa uku da za a miƙa wa Majalisar Ministocin Harkokin Waje don ta tattauna a kansu — batun Falasɗinu da abubuwan da aka cim ma a Banjul da kuma yarjejeniyar ƙarshe kan lamarin.




2247 GMT — Kaso 38 na Amurkawa na ganin ƙasarsu tana bai wa Isra'ila taimako mai yawa


Kimanin mutum huɗu cikin 10 na Amurkawa sun ce suna ganin ƙasar tana bai wa Isra'ila taimako da yawa a yaƙin da take yi da Falasɗinawa a Gaza.


Wani bincike da aka gudanar daga ranar 25 zuwa 30 ga watan Afrilu kan mutane 2,260 ya nuna cewa kawunan Amurka sun rabu kan hare-haren da Isra'ila take kai wa a Gaza.


Binciken, wanda US News Ipsos ya gudanar ya nuna cewa kaso 38 na Amurkawa na ganin ƙasarsu tana bayar da goyon baya mai yawan gaske ga Isra'ila, yayin da kaso 20 ke ganin Amurka ba ta taimakon da ya dace ga Isra'ila a yaƙin da take yi a Gaza, sannan kaso 40 na da ra'ayin cewa Washington tana yin abin da ya dace.


Kazalika binciken ya nuna cewa kashi 37 na Amurkawa suna ganin tsohon shugaban ƙasar Donald Trump zai fi Shugaba Joe Biden iya tafiyar da batun yaƙin Gaza; yayin da kaso 29 suke tunanin Biden ya fi iya shawo kan lamarin.


Amma kaso 33 sun ce ba su amince da kowanne daga cikinsu ba, sai kuma kashi 1 na Amurkawa da ba su bayyana ra'ayinsu ba.


2145 GMT — Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna sun kai wa taron Falasɗinawa hari a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan


Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna sun kai wa taron Falasɗinawa hari a Jericho da arewacin Kwazazzabon Jordan, a cewar wata ƙungiyar Falasɗinu wadda ta ce a watan Afrilu kaɗai an kai irin wannan hari sau 347 a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan


Ƙungiyar mai suna Al Baidar Organization for the Defense of Bedouin Rights ta fitar da sanarwar da ke cewa sau biyu Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna suka kai hari a unguwar Arab al Mleihat Bedouin da ke arewacin Jericho.


“Wani gungun Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna masu tsattsauran ra'ayi ya mamaye unguwar Arab al-Mleihat da ke kudu maso arewacin Jericho karo na biyu fa kwana guda," in ji shugaban ƙungiyar Hassan Mleihat.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url


';