Rundunar sojin Nijeriya tana tuhumar jami'anta kan kisan mutane a Tudun Biri

 Rundunar sojin Nijeriya tana tuhumar jami'anta kan kisan mutane a Tudun Biri

Edward Buba ya ce an kammala bincike kan sojojin kuma hedkwatar tsaron Nijeriya za ta hukunta duk wanda ta samu da laifi a kisan mutanen na Tudun Biri, tare da yi wa 'yan'uwan waɗanda aka kashe adalci.

Hedkwatar tsaron Nijeriya ta ce tana tuhumar wasu dakarunta bisa zargin kisan fararen-hula a ƙauyen Tudun Biri na jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar.

Mai magana da yawun hedkwatar, Edward Buba, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya gudanar ranar Alhamis a Abuja babban birnin ƙasar.

Edward Buba ya ce an kammala bincike kan sojojin kuma hedkwatar tsaron Nijeriya za ta hukunta duk wanda ta samu da laifi a kisan mutanen na Tudun Biri, tare da yi wa 'yan'uwan waɗanda aka kashe adalci.

“Rundunar soji ta yi cikakken bincike kan lamarin sannan ta soma bin tsarin hukunta waɗanda aka samu da laifi. Don haka, waɗanda ke da hannu a wannan lamari za su fuskanci hukunci daga kotun soji. Ba na so na yi maganar da ta wuce wannan," in ji shi.

A ranar 3 ga watan Disamba ne wani jirgi maras matuƙi na rundunar sojojin Nijeriya ya kai hari a kan wasu mutane da ke bikin Maulidi a ƙauyen Tudun Biri inda sojojin ƙasar suka ce an kai harin ne a bisa kuskure.

Harin ya yi sanadin mutuwar fararen-hula kusan 100 kuma ya jawo kakkausan suka daga cikin da wajen Nijeriya. A wancan lokacin, shugaban ƙasar Bola Tinubu ya lashi takobin gudanar da bincike mai tsauri kan lamarin tare da hukunta waɗanda ke da laifi.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url

';