Uncategorized

Rasuwar Hauwa Maina 2018 Yau Shekaru (6) Kenan Tarihin Ta da Aiyukan Da Tayi

4

FB IMG 17146464735148835

 

Rasuwar Hauwa Maina 2018 Yau Shekaru (6) Kenan Tarihin Ta da Aiyukan Da Tayi

A Rana Mai Kamar Ta Yau 2 Ga Watan Mayu 2018, Allah Yayiwa Shahararriyar Yar Hausa Film Hauwa Maina Rasuwa.
A ranar Laraba ta farkon watan Mayu ce Hauwa Maina ta rasu a asibiti a Kano bayan doguwar rashin lafiya.
Ta kwanta a asibitin kasa da ke Abuja, kafin daga baya aka mayar da ita Asibitin Nasarawa da ke Kano inda ta rasu.
Da safiyar Alhamis ne kuma aka yi jana’izarta a mahaifarta jihar Kaduna, inda kuma a nan ne ta zauna gabanin rasuwarta.
Tauraruwar ta fina-finan Hausa ta rasu tana da shekara hamsin a duniya.
Ta taba yin aure, kuma tana da ‘ya’ya biyu, Muryam Bukar (Baby), da kuma Abdurrahman Bukar.
Makusantanta sun ce tana yawan fama da ciwon kirji, amma likitoci sun ce ba gembon ciki ba ne (ulcer).
Rayuwarta
Duk da yake an haife ta a Kaduna, amma ‘yar asalin karamar hukumar Biu ce a jihar Borno, kuma ‘yar kabilar Pabur (Babur) ce.
Tana alfahari da kasancewarta ‘yar kabilar ta Pabur, duk kuwa da gorin da wasu suke yi mata cewa ba Bahaushiya ba ce.
Ta yi karatun zamani har zuwa matakin jami’a inda ta samu shaidar Babbar Diploma ta Kasa HND.
Kuma gabanin rasuwarta ta koma karatun digiri a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, bangaren jagoranci da bada shawara.
Hauwa Maina na daga matan fina-finan Hausa da suka jima ana damawa da su a Kannywood.
Ta fito a fina-finai da yawa na tarihi da kuma na zamani.
Wasu daga fitattun fina-finanta sun hada da fim din tarihin Sarauniya Amina ta Zazzau, da “Bayajidda” inda ta fito a matsayin Saruniya Daurama, da “Baban Mulika” inda ta taka muhimmiyar rawa.
Haka kuma ta yi fina-finan turanci na Kannywood da kuma na Nollywood na kudancin Najeriya.
Daga cikin fina-finanta na turanci akwai “Waves,” da “Midnight Sun”, da “Dry” na Stephene Okereke da “There is a Way” na kabiru Jammaje.
Haka kuma ta yi fina-finai da yarenta Pabur (Babur), wanda ta ce ta assasa shi ne saboda kishin yarenta, da kokarin wanzar da yaren ga ‘yan baya.
Hauwa Maina ta ce ba kowane irin fim take amincewa ta fito ba.
Ta ce tana fitowa ne kawai a fim din da ta gamsu cewa labarinsa ya yi ma’ana, kuma zai ilmantar.
Tana daga cikin mata da suke gudanar da shirya fina-finan Hausa, da daukar nauyi, da bada umarni.
Baya ga fina-finai, Hauwa Maina ta kuma gabatar da shirye-shirye na gidan talabijin.
A lokacin rayuwarta ta dukufa wajen koyar da mata sana’o’i, musamman girke-girke.
Rayuwar Hauwa Maina a takaice
Tun 1999 ta fara fim din Hausa, bayan ta koma garin Kaduna da zama
Fim din ta na farko shi ne Tuba wanda Malam Yahya, wani tsohon ma’aikacin gidan talbijin na kasa NTA ya bayar da umarni
Ta fara fitowa a matsayin budurwa, sai kuma matar aure, sannan ta koma tana fitowa a matsayin uwa
Ita ce ta fito a fina-finai na tarihi kamar Sarauniyar Zazzau Amina, da Bayajidda inda ta fito a matsayin Sarauniya Daurama
Ta yi fina-finan turanci na kudancin Najeriya Nollywood da kuma na Kannywood
Ta kafa harkar fina-finai da harshenta na Pabur (Babur)

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button