MAZAN JIYA Littafi Na Daya (1) Part F


 MAZAN JIYA

Littafi Na Daya (1)

Part F

Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini

Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey



Koda sarki yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubo masa sannan ya cigaba bayani inaso kusani cewa a duniyar nan babu abinda nakeso sama da yata sahira, to amma inaji ina gani zan rabu da ita domin bincike ya tabbatar min dacewa rayuwata gajeriyace abune mawuyaci na kara shekara biyar nan gaba a duniya, daga yau na damka muka sahira a hannunku na sani cewa a halin yanzu duk biyun kun kamu da kaunar sahira, to amma fa kusani cewa dole daya daga cikin ku ya hakura yabarwa dayan wadda duk ya auri sahira acikin ku bazai tabayin sarauta ba kuma zai sota samada komai a rayuwar sa, kuma saita rigashi mutuwa wanda yarasa sahira acikin ku shine zai gaji sarauta ta kuma zaiyi tsawon rai a rayuwarsa har yabar duniya haihuwa daya zaiyi sannan ya mutu yabar abunda ya haifa, babu wani tsafi ko wani kokari dazai sauya wannan kaddara akan mu inaso ku kwantar da hankalinku akan fitar da zuciyoyin ku bisa samun mulki koh auren yata domin lokacin ne zai banbanta komai da wannan kalami nake muku sallama daku tashi kutafi gidajen ku amma kafin sannan akwai kyauta ta mussamman yacce zan baku koda gama fadin haka sai sarki hubru ya dubi yarsa gimbiya sahira yace jeki ki dauko musu kyautarsu cikin fara'a sahira ta mike tsaye ta shiga wani daki tana tafiyar kasaita tamkar dawisu jim kadan sai gata tafito da wadansu jakukkunan fata guda biyu sahira ta matso gabanmu tabawa kowa jaka guda koda muka karba muka bude ashe zinare ne acike makil nan take muka zube kasa muna gdy sarki hubru ko kallon mu baiyiba saiya kama hannun gimbiya sahira yashige da ita izuwa cikin wannan dakin data dauko kudin shigewarsa keda wuya sai maharaz ya rude ya rikice sbd ganin wadannan kudade niko sai naji sam kudin basu dameni niba.

Daga wannan rana wani abu sake faruwa ba sai bayan kwanaki goma sha bakwai da wata safiya sa'adda tafiya takama Sarki hubru izuwa wani kauwe da ake kira zumur domin yaje ya dubo wani tsohon abokinsa wadda ya kwanta ciwo tsawon wata uku, shidai wannan aboki na Sarki Hibru sunan sa abul husnu, kuma tun kuruciwa suka taso da sarki hubru abinda yasa yayi zamansa a zumur shine ya samu nasibi matuka a harkokin kasuwanci domin mutanen garin suna matukar kaunarsa sbd yawan taimakon sa da kuma kyautatawa ga talakawa, akarshe ma saida suka matsa mishi ya karbi shugaban cin birnin Sarki hubru ne dakanshi yazo ya nada shi a matsayin shugaban birnin akaxo akayi gagarumin biki bayan wata daya dayin bikin ne ciwo mai tsanani ya kama abul husuna lokacin da lbr ya riski sarki hubru sai hankalinsa ya dugunzuma aka nemi likitoti suyi masa magani saida likitoci sukai kwana goma suna lura da abul husuna basu gane irin cutar datake damunsa ba, bisa dole duka debi nasu da nasu sukaje suka sanarwa sarki hubru halin da ake ciki dajin bayanin likitocin sai hankalin Sarki ya kara dugunzuma akan hanyane sarki hubru ya tafi wajen wani amintaccen bokansa ya sanarda dashi halin da ake ciki, nan take bokan yayi bincike nan take yayi murmushi ya duvi Sarki yace ai wannan cuta ta abokin ka sharrin sihiri ne ba wani bane yayiwa abul husuna asiri sai tsohon shugaban kauyen zuhur sbd bakin cikin an sauke shi daga mukaminsa andaura abul husuna, shi dai wannan asiri an bunne shine a kofar gidan abul husuna.

Abul husuna bazai taba warkewaba sai an tono asirin kuma idan an tonoshi take wanda yayishi zai mutu babu mai iya tono wannan asiri sai Sarki mai karfin mulki kamarka. Ya shugaba yazama dole kaje dakan ka kaje ka tono wannan asiri amma kada kaje sai randa asirin ya cika kwana casa'in da binnewa domin idan ka tonoshi kafin cikar kwana casa'in da wanda yayi asirin da wanda aka yiwa duk mutuwa zasuyi.

Lokacin da bokan yaxonan azancen sa sai sarki hubru ya cika da mamaki daga can kuma sai ya dubi bokan yace toh yanzu idan naje kofar gidan abul husuna yaza'ayi nagane daidai inda aka bunne asirin boka yayi murmushi yace dazarar kaje kofar gidan kadaga kwagirinka na sarauta sama kasake shi, a duk inda kwagirin ya fado to daidai wajen zaka saka a tone kodajin wannan batu sai sarki hubru yadauko dukiya mai yawa yabawa bokan nasa yana mai matukar farin ciki sannan sukayi sallama sarki ya tafi gida. 

A ranar da abul husuna ya cika kwana casa'in a kwance yana jinya mukayi shiri tareda dakaru dubu arba'in muka tafi kauyen zumur saida mukaci rabin tafiya mun shigo cikin wata sahara inda babu gida gaba babu gida baya babu bishiyoyi ko duwatsu babu ruwa sai kawai mukaji wani irin tsananin zafi yana fesowa, nan da nan dawakanmu suka dimauce suka kama tutsu suna yada mahayan su suna fita da gudu wata irin gagarumar iska ta taso ta dinga daga mutane da dawakai suna yawo akan iska al'amarin daya dugunzuma hankalin kowa kenan keken dokin sarki maharaz saida ya rabu da kasa zaiyi sama kenan na rikoshi da karfin tsiya amma sai karfin iskar yafara rinjayata saida maharaz ya taimaka min sannan muka sauke shi kasa ni kaina inda badan maharaz ya taimaka min ba da tuni iska tayi sama dani munaji muna gani gagarumar iskar tayi sama da dukkanin abokan tafiyar mu tayita lulukawa dasu tun muna iya hango su har saida suka bace bat ya rage saura mu uku bisa turba wato ni da sarki hubaru wanda cikin keken doki bayan lafawar guguwar ne sarki hubaru ya fito daga cikin keken dokin ya tsaya a tsakiyar mu nan take na zare takobi na kama kallon gabas da yamma kudu da arewa ina jiran tsammani. 

Shiko maharaz sai yafara kallon tafin hannunsa yana karanta wadansu dalasiman tsafi faruwar hakan keda wuya sai mukaga wata katuwar inuwa ta lullube mu koda muka daga kawunan mu sama sai mukaga wata katuwar halitta tana saukowa daga sama mai tsananin muni da rashin son gani sannu ahankali halittar ta iso kasa-kasa yadda kana iya ganin cikakkiwar fuskarta koda mukayi arba da halittar sai duk mu ukun muka firgice ainun kamar zamu zabura da gudu dayake ita dai wannan halitta bakomai bace face wata sihirtarciyar dodanniya mai kawuna takwas kowani kanta guda girmansa yakaina katon dutse gabadaya kawunan takwas ajikin wuya daya yake shiko wuyan nata dogo ne har karawa kanshi tsayi yakeyi kamar yadda wuyan take kara tsawo haka hannayen tama ke kara tsawo ga dukkan alamu dai idanta mike hannunta guda daga inda take zata iya dauko abindake can bayan duniya daga kowace kusurwa kawai sai mukaga dodanniyar nan ta wangame bakinta guda ta kama gabadaya dakarun namun nan guda dubu arba'in harda dawakansu sunata zubowa kasa a mace anan tayita amarsu suna zubowa tamkar an dafa su acikin tukunya har tururin zafi ne ke fita daga jikinsu SBD tsananin zafin dake jikin dodanniyar.

Bayan dodanniyar ta gama amayarda abunda cikinta saita dube mu da idanunta kwala-kwala ta tuntsire da mahaukaciyar dariya maikama da saukar aradu, muka kara firgicewa muka hau kakumar junanmu lokaci guda ta turbune fuska tace kaicon yaku wadannan kananan halittu yau kun gamu da uwar dodannin duniya dayan ku bazai tsira daga bala'i naba duk saina zare muku ruhun numfashi, kuyi sani cewa sarki dumbazu na birnin kailas ne ya aikoni na hallaka sarki hubaru, labari ya riske ni cewa anturo gilzam kun hallaka shi to kusani cewa nina gagari dukkan sadaukan duniya da duk matsafan duniya, yau shekarata dubu tara ina tare mutane da aljanu a can dajin sarbusa ina cinyewa ankasa ganin bayana yanzu Sarki dumbazu yayi min alkawari cewa in dai na hallaka sarki hubaru zai dinga bani mutane dubu ina cinyewa basai nayi wahalar farautar suba, burina shine naci adadin mutane miliyan dubu saba'in a sannan ne zan iya haifan yayana wadanda bazasu bazama ko inaba a duniya sai sun cinye komai da kowa a kwana tara yazamana cewa babu wani abu mai rai a doron kasa saini dasu kawai.

Koda uwar dodanni tazo nan a zancen ta sai naji dukkan tsoro ya kau daga cikin zuciyata kawai saina dubi sarki hubru da maharaz nayi musu inkiya dasu fada cikin keken doki aikuwa sai sukayi wuf suka fada suka rufe kansu niko saina zare takobi na, na fuskanci uwar dodanni nace ai saiki fara gamawa dani kafin ki gamada sarki hubaru koh! nikaina nasan bakin rijiya yafi gaban wasan yara dan haka tsaurin ido kawai dakuma jarraba sa'a nayi amma ko kadan banasa ran cewa zan iya tabuka wani abu saidai nasan ance mai rai baya rasa motsi watakila nadan iya bata mata lokaci.      

Lokacin da uwar dodanni taji nayi wannan lafaji a gabanta saita sake bushewa da mahaukaciyar dariya a karo na biyu wadda har zaida walkiya tayita fita daga bakinta tartsatsin wuta yadinga fita cikin dacin rai da shammata ta mangareni da hannunta guda sbd karfin dukkan saida nayi sama na gwara baya ajikin wata bishiya ita kanta bishiyar saida ta tunbuko har jijiyoyin ta daga cikin karkashin kasa muka fadi kasa tare na baje wanwar a sume koh shurawa ban sake yiba azaton uwar dodanni kasusuwan bayana sun karye na mutu don haka saita zuro hannun ta a hankali ta balle kofar dakin keken dokin dasu sarki hubru ke ciki sukayi arba da fuskarta kawai saita kama musu dariya alamarin daya firgita su kenan mussan da suka hango a can gefe daya a kwance a mace ana cikin wannan haline na farfado akayi sa'a kuwa banyi yunkurin mikewa ba yadda hankalin uwar dodanni zai dawo kaina, a sannan ne tazuro hannun ta cikin keken dokin ta damko sarki hubru da maharaz tayi sama dasu da nufin takai kawunan cikin bakinta ta gutsure su kwatsam sai uwar dodanni taji motsi akan jelar ta abinda bata saniba shine nine na ruga na hau kan jelar naketa tsala matsanacin gudu domin na isa kan kafadarta kafin hannunta yakai bakinta, koda uwar dodanni taji motsin yana karuwa saita fara kai duka faruwar hakan ne tasa uwar dodanni tasamu jinkirin kai hannunta izuwa cikin bakinta ta gutsure kawunan su sarki hubaru koda taga motsin yaki karewa saita maida hankalinta wajen kai hannunta cikin bakinta guda saura kiris ta zuro kawunan su sarki hubaru a bakinta na iso kan kafadar ta aikuwa saina daka tsalle daga kan kafadarta nakaiwa hannunta sara wanda ke dauke dasu sarki hubaru take takobi na ya zabtare hannun nata ya fado kasa su hubaru suna cikin yankekken hannun nan kuwa ya kama tsartuwa da feshi daga cikin dulgul min hannun tamkar magudanar ruwa ta balle tsananin zafi da zogine da uwar dodanni tajine yasa tahaukace ta makance tahau kaiwa iska duka tana ruri da kururuwa mai tsananin firgitarwa, koda naga ta dimauce saina dinga saran sassan jikinta da takobina nikaina nayi mamakin yadda nasamu wannan nasara cikin gaggawa haka bayan sassan jikin uwar dodanni ya gama faduwa kasa sai sarki hubaru da maharaz suka fito daga cikin keken doki suka kuramin ido kawai suna mai matukar mamaki na sarki hubaru ya dube ni yace wai shin wannan yaro anya kuwa kai mutum ne tayaya kake yin wadan nan abubuwan alajabi wadanda sunwuce gaban tsammani. Koda jin haka sainayi murmushi na goge jinin dake jikin takobina na sumbaci takobin nace ya shugabana kaga wannan takobin inhar dai ina tare da ita bana shakkar tarar kowani irin bala'i asalinta ta kaka nane na uku indai kaga an cini da yaki to bana tarene takobin nan nayi imani da haka sarki hubaru ya kurawa takobin nawa ido dakyau ya girgiza kai baice komi ba. 

A sannan ne muka dubi gawarwakin dakarun mu dake zube a kasa sai takaici ya turnuke mu bamu san sa'adda idanunmu suka ciko da kwalla ba nan take muka cinnawa gawarwakin wuta sannan muka hau keken dokin sarki hubru muka cigaba da tafiya har muka isa kauyen zumur bamu sake haduwa da wani tashin hankaliba kamar yadda bokan sarki hubru ya fadi haka alamura suka kasance da isarmu kofar gidan yadaga kwagirin sa na sarauta sannan ya sake shi ya fado kasa aiko sai kwagirin ya cake a karkashin kasa bai fadi kasa ba koda ganin haka sai sarki hubaru ya dubeni yace maza ka tone daidai inda kwagirin ya cake, nan take na cika umarni koda nayi rami mai zurfi kamu uku saiga wadansu layu ina fito dasu sai maharaz yayi nuni ga hannunsa akan layun take suka kone kurmus faruwar hakan keda wuya said juyo shewar mata acikin gidan take abul husuna ya fito daga cikin gida ya takawa da kafafunsa cikin koshin lafiya, koda yayi arba da sarki hubru sai yacika da tsananin farin ciki ya rugo gareshi suka rungumi juna abul husuna yace lale marhabin da aminina dama nayi mafarki zan warke daga wannan cuta a ranar daka kawomin ziyara.

Koda jin haka sai sarki hubaru yayi murmushi yace aiko mafarkinka gaskiya ne tunda gashi ya tabbata nan take sarki hubaru yabawa abul husuna duk abunda yafaru tsakaninsa da bokansa akan rashin lafiyansa koda jin haka sai abul husuna ya cika da tsananin mamaki yace aiko shi makiyi bashida kama domin aduk fadin garin nan babu mai nuna min kauna samada tsohon shugaba ashe kaunar ta karyace da yaudara, rufe bakin abul husuna keda wuya saiga matar tsohon shugaban da yayan sa sun rugo da gudu suna kuka da zuwa sai suka zube a gaban abul husuna suka bada lbr cewa ga maigidan su can yayi wata irin mutuwa mai ban tsoro, koda jin haka sai sarki hubru ya dubesu yace kuje ku kone gawar maigidanku domin sharrin dayaso yayi abokina abul husuna ne ya koma kansa, koda jama'ah sukaji lafazin da sarki hubaru ya fada akan tsohon shugabansu sai duka hai tsine masa da murna akan muturwar sa, nan take abul husuna ya shigar damu cikin gidansa ya kaimu har izuwa turakarsa zaman mu keda wuya sai wata tsaleleliyar budurwa wadda muka gani tamkar hussainar gimbiya sahira ce sbd tsananin kyawu shi kansa sarki hubru baisan sa'adda ya kura mata idanu ba dan tsananin alajabi itadai wannan budurwa bambamcinta da sahira kawai tafita shekaru ne akalla zata girmeta kamar da shekaru biyu budurwa ta nufo mu da farantin abinci sannan ta durkusa har kasa ta gaisheda sarki hubru sannan muma ta gaishe mu sannan ta koma cikin gida har sarki hubaru ya bude baki zaice wani abu sai abul husuna yace kada kace komai yakai abokina wannan budurwa dakuka gani yata ce ta cikina sunanta husna kamar yadda ka boye yarka ga jama'ar kasar nan haka nima na boye tawa kuma bokan da yamaka bayanin cutata shine yasa na boye tawa yar kuma ya gayamun cewa duk ranar daka kawo min ziyara tare da matasa biyu masu tsaron lafiyar ka to acikin sune yata zata samu mijin aure sa'adda abul husuna yazo nan azancensa sai sarki hubaru ya cika da tsananin mamaki. Daga can sai sarki hubaru ya kallemu yace ku tashi ku fita inason ganawa da abokina.

Haka muka tashi muka fice duk kuwa da cewa muna matukar jin yunwa kuma ga abinci mai rai da lafiya an kawo. Bayan fitarmu daga gidan Abul Husuna sai muka samu waje muka zauna muka yi shiru dayanmu bai ce uffan ba, daga can sai na dubi Maharaz nace da shi ya kai abokina nifa abubuwan nan dake faruwa da mu suna jefamu cikin rudani da rikittarwa, kaga dai ance dole a cikinmu ne daya zai auri Gimbiya Sahira sannan ance a cikin mune daya zai auri wannan budurwa Husuna, ina ganin tun yanzu ynaa da kyau kowanne daga cikinmu ya banbance zabinsa, kai yanzu a cikin yan matan nan biyu wacce ta kwanta maka a rai.

Yayin da Maharaz ya ji wannan tambaya sai yayi murmushi yace ya kai abokina kayi sani cewa ai ni bani da zabi sai abinda ka zaba, dan kada na zabi wacce kake so a ranka, nikam duk wacce na samu babu matsala.


Tabbas ko nine Sarki Maharaz abinda zance kenan, amma fa karya yake yi aradu ya fi son wannan kyakkyawan budurwar kodan ya zama sarki ai dole ya sota au ashe satar amsa nake kokarin baku...๐Ÿค”


Inayi wa daukacin masu bibiyar wannan labari barka da hutun karshen mako da fatan kuna cikin koshin lafiya.


Shin kana bukatar wani littafi na yaki kawai tuntubeni ta wannan Number ko kuma kayi mani magana da profile dina 08138873799.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url


';