"Laifinku Ne": Shehu Sani Ya Fadi Dalilin Ƙaƙaba Harajin 0.5% da CBN Ya Yi

 "Laifinku Ne": Shehu Sani Ya Fadi Dalilin Ƙaƙaba Harajin 0.5% da CBN Ya Yi 



 Sanata Shehu Sani ya yi shaguɓe ga 'yan Najeriya kan jawowa kansu haraji na musamman daga babban bankin CBN Sanatan ya ce laifin 'yan Najeriya ne inda suka yi ta korafe-korafe kan inda Bola Tinubu ya ke bayan kammala taro a Saudiyya Sanatan ya na magana ne kan ƙaƙaba harajin 0.5% da Babban Bankin Najeriya, CBN ya yi kan masu tura kudi bankuna KumuryaMedia ta bude tasha a manhajar Whatsapp. 

FCT, Abuja - Yayin da ake ta cece-kuce kan sabon haraji da bankin CBN ya saka, Sanata Shehu Sani ya yi martani. Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya ya zargi 'yan Najeriya da jawo matsalar karin harajin da CBN ya yi. 


Shehu Sani ya magantu kan harajin CBN Shehu Sani ya byyana haka a shafinsa na X a yau Talata 7 ga watan Mayu bayan karin haraji da bankin ya sanar. Ya ce 'yan Najeriya sun yi ta korafi kan inda Shugaba Bola Tinubu ya ke yayin da ya ziyarci wani taro a Saudiyya. 


Har ila yau, Sani ya ce korafe-korafen da suke ta yi ne ya jawo aka kawo musu sabon haraji a kasar. "Shugaban kasa ya yi tafiya, kun zo kuna ta damunsa ina ya shiga." "Gashi yanzu kun jawowa kanku haraji, sai ku sake tambayarsa yaushe zai dawo." 

- Shehu Sani . 


An yi ta korafin inda Tinubu yake Martanin na Shehu Sani na zuwa ne kwanaki kadan bayan 'yan Najeriya sun fara binciken Tinubu bayan kammala taron Saudiyya amma bai dawo ba. 

Isra'ila ta karɓe iko da mashigar Rafah a Gaza

A yau Talata 7 ga watan Mayu bankin CBN ya saka dokar biyan harajin har 0.5% domin tsaron yanar gizo a kasar. 


Sai dai CBN ya ware wasu hada-hadar kudi 16 da wannan doka ba za ta shafa ba da suka haɗa da biyan albashi da karba ko biyan bashi. CBN ya kakaba dokar biyan harajin 0.5% Kun ji cewa Babban Bankin Najeriya, CBN ya kakabawa 'yan Najeriya sabon haraji kan hada-hadar kudi da za su yi. 


Bankin ya kara akalla 0.5% kan kowane tura kudi da 'yan kasar zasu yi tsakaninsu domin tsaron yanar gizo. Wannan na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke kokawa kan tsare-tsaren Shugaba Bola Tinubu da ke jefa su cikin mawuyacin hali.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url


';