Jam'iyyar PDP: Mulkin APC ya mayar da ma'aikatan Najeriya mabarata'

 Mulkin APC ya mayar da ma'aikatan Najeriya mabarata'


A Najeriya, babbar jam'iyyar hamayya ta kasar, wato PDP, ta yi kakkausar suka ga gwamnatin kasar ta jam'iyyar APC, game da karin albashin da gwamnatin ta yi, da cewa wani mataki ne na an yi ba a yi ba.


Domin kuwa jam'iyyar PDPn na ganin an yi karin albashin ne yayin da jama'ar Najeriya ke ta fama da matukar tsadar man fetur da tsadar kayan abinci da dai sauran matsalolin da suka haifar da tsadar rayuwa.


A ranar Talata, kwana ɗaya kafin ranar bikin ma'aikata ta duniya ne ofishin kula da albashin ma'aikata na Najeriya ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana cewa an yi wa ma'aikatan gwamnatin tarayya ƙarin albashi da kashi 25 zuwa 35 cikin ɗari.


Lamarin ya haifar da cece-ku-ce ganin cewa akwai wani kwamiti da gwamnatin ta kafa wanda aka ɗora wa alhakin samun matsaya kan albashi mafi ƙaranci a ƙasar.

A tattaunawarsa da BBC, Ibrahim Abdullahi, mukaddashin jami'in hulda da jama'a na jam'iyar na kasa ya ce, halin da Najeriya ta shiga a ƙarƙashin mulkin APC cikin shekaru tara, ya sanya ƴan ƙasar sun koma mabarata saboda yunwa "Ana fuskantar mummunan rashin tsaro da halin ha'ula'i da ƙasa ta shiga."


Jam'iyyar ta PDP na ganin ko da an yi ƙarin albashi, adadin ƙarin ba zai samar da maslaha ba a cikin halin ƙunci da kariyar tattalin arziƙi da suke ciki ba.


"Abin da shi ma'aikaci yake tunanin zai samu shi ne sauƙi, ba kawai a ƙara albashi cikin mummunan hali ba saboda ƙarin ba ya iya saya masa kashi goma na abin da a baya yake iya saye, domin haka wannan shi ne ci gaban mai shiga rijiya."


Ibrahim Abdullahi, ya ce abin da ya kamata gwamnati ta yi shi ne ta samar da tsaro ga manoma domin su noma abincin da ƙasa za ta samu ya wadata domin a samu sauƙin abincin.


PDP ta ce janye tallafin man fetur na kan gaba wajen haifar da halin da Najeriya ke ciki.



A baya, farashin litar man fetur bai wuce naira dari da sittin da biyar ba a farsahin gwamnati, a lokacin zuwanta, sai dai yanzu ya nausa zuwa naira dari shida da doriya, kasancewar gwamnati ta kakkabe hannunta ta bari kasuwa ta yi halinta.


Yayin da yanzu ake fusknatar ƙarancin man fetur a Najeriyar duk da ƙoƙarin da hukumomi ke cewa suna yi domin ganin sun shawo kan matsalar amma kullum lamarin ƙara ƙamari yake yi, inda man fetur din ya yi tashin gwaron zabi a dukkan sassan ƙasar.


Wannan ne ya yi sanadin hauhawar farashin kayan masarufi da sauran abubuwan more rayuwa.


Har ta kai ga wasu daga cikin farashinsu ya yi tashin gwauron-zabi, ya ninninka!


A ranar Laraba, shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na Najeriya su ma sun yi watsi da ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta sanar.


A tattaunawarsa da BBC, sakataren ƙungiyar ƙwadago ta TUC, Nuhu Toro, ya ce ba da saninsu aka yi ƙarin ba, kuma har yanzu ba a cimma matsaya a kan sabon albashi mafi ƙaranci da ake sa ran ƙayyadewa ba a ƙasar.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url


';