Uncategorized

Dr. Mansur Sokoto: Hukuncin Mutumin da yayi wa ALLAH qarya

4
FB IMG 17145863844769922

 Dr. Mansur Sokoto: Hukuncin Mutumin da yayi wa ALLAH qarya

Facebook: Dandalin Fatawa

Wata fatawar idan aka sako ta – a nan – wallahi sai kanka ya girgiza. Irin fatawoyin nan da ake cewa, da an yi su a zamanin Sarkin Musulmi Umar (ra) ba zai yanke hukunci ba sai ya haɗa mutanen Badar ya ji fahimtarsu. Idan ka koma ga profile ɗin wannan “Grand Mufti” sai ka tarar kawai malamin wata Islamiyyah ne. (Na riƙe misalan da nike da su domin ba ni son in tozarta kowa. Wannan tunatarwa ce kawai. Amma zan isar da su ga waɗanda ya kamata su sani don su fahimci muradina). 

Ya wajaba mutane su ji tsoron Allah. Babu wani abu wanda yakai hatsari ga Musulmi kamar ka yi fatawa a addini da son zuciya a kan abinda ya fi ƙarfin iliminka, domin matsayinsa ɗaya ne da sharara ma Allah ƙarya ka jingina masa tunda yake addini nasa ne. Allah maɗaukaki yana cewa:

(ولا تقولوا لما تصف ألسنتكم الكذب هذا حلال وهذا حرام لتفتروا على الله الكذب، إن الذين يفترون على الكذب لا يفلحون) سورة النحل: ١١٦

Ma’ana: “Kuma kada ku riƙa faɗin ƙarya da abinda harsunanku ke sifaitawa (kuna cewa): wannan halal ne, wannan kuma haram ne, don ku ƙirƙira ma Allah ƙarya. Haƙiƙa, waɗanda suke ƙirƙira ma Allah ƙarya ba su rabauta” Suratun Nahli: 116

Kuma subhanahu yana cewa:

(ويوم القيامة ترى الذين كذبوا على الله وجوههم مسودة، أليس في جهنم مثوى للمتكبرين) سورة الزمر: ٦٠

 Ma’ana: “A ranar alƙiyama kana ganin waɗanda suka yi ma Allah ƙarya; fuskokinsu baƙi ƙirin. Ashe a cikin Jahannama babu matabbatar masu girman kai?” Suratuz Zumar: 60

Wannan ayar ta nuna Girman kai ne ka saki hukunci a Shari’a ba tare da ka tuntuɓi ma’abotanta ba. Akwai wasu mas’aloli gama-gari waɗanda suka shafi al’umma gaba ɗaya da makomarta, bai dacewa – ko ga Malami wanda ya ƙasaita a sanin Shari’a – ya yanke ma al’umma hukunci a kan su shi kaɗai har sai ya tuntuɓi sauran ire-irensa da na gaba da shi.

Da wannan nike jaddada kira ga a samar da Majalisin Fatawa na Malaman Sunnah aƙalla a nan Najeriya wanda zai ƙunshi haziƙai da zaƙaƙuran masana daga fannonin ilimin Shari’a don su riƙa duba irin waɗannan mas’aloli suna masu la’akari da nassoshin Alƙur’ani da Sunnar Manzon Allah (S) da kuma manufofin Shari’a tare da taɗbiƙinsu a kan yanayi da zamani.

Allah ya kyauta.

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button