Uncategorized

Colombia za ta yanke hulɗa da Isra’ila kan ‘kisan kiyashin’ da take yi a Gaza

4

Colombia za ta yanke hulɗa da Isra’ila kan ‘kisan kiyashin’ da take yi a Gaza

19743548 0 0 760 428

Colombia za ta yanke hulɗa da Isra’ila kan ‘kisan kiyashin’ da take yi a Gaza

Yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza ya shiga kwana na 208, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 34,568 – kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata – tare da jikkata sama da 77,765.

19755360 0 0 760 428

1737 GMT — Colombia za ta yanke hulɗa da Isra’ila kan ‘kisan kiyashin’ da take yi a Gaza

Shugaban Colombia Gustavo Petro ya ce za su yanke hulɗar jakadanci da Isra’ila kan yaƙin da take yi a Gaza.
Tuni da ma Petro yake caccakar Firaiministan Benjamin Netanyahu sannan ya yi kira ga Afirka ta Kudu ta saka shi a cikin ƙarar da ta kai Isra’ila a kotun duniya kan zarginta da kisan ƙare-dangi a Gaza.
“A yanzu kuma a gabanku, gwamnatin canji da shugaban ƙasar jamhuriya suna sanar da cewa gobe za mu yanke hulɗar jakadanci da Isra’ila…saboda kasancewarta gwamnati da shugaban ƙasa masu kisan ƙare-dangi,” in ji Petro a yayin da yake jawabi ga dandazon jama’a a Bogota, don tunawa da Ranar Ma’aikata da kuma goyon bayan sauye-sauyen Petro kan walwala da tattalin arziki.
1400 GMT — Sama da ma’aikata 1,000 sun gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Birtaniya
Sama da ma’aikata dubu ɗaya a faɗin Birtaniya suka gudanar da zanga-zanga a Ranar Ma’aikata ta Duniya inda suke kira kan a daina sayar wa Isra’ila makamai.
Ma’aikatan sun toshe Ma’aikatar Cinikayya ta Birtaniya da ke Landan da wasu kamfanonin makamai da ke Scotland da Wales da Lancashire.
A Landan, masu zanga-zangar sun buƙaci gwamnatin ƙasar ta ƙwace lasisin fitar da makamai ga Isra’ila daga kamfanonin ƙasar.
A ɗayan ɓangaren kuwa, mambobin ƙungiyar goyon bayan Falasɗinawa ta Palestine Action group ta yi zanga-zanga a gaban ofisoshin bankunan Barclays da BNY Mellon da ke Manchester inda ƙungiyar ke zarginsu da alaƙa da Isra’ila

19755366 0 0 760 428

Rasuwar Hauwa Maina 2018 Yau Shekaru (6) Kenan Tarihin Ta da Aiyukan Da Tayi

 1023 GMT — Adadin jama’ar da Isra’ila ta kashe a Gaza ya kai 34,568 — Ma’aikatar Lafiya

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta bayyana cewa aƙalla mutum 34, 568 Isra’ila ta kashe a Falasɗinu kusan watanni bakwai tun bayan da ta soma kai hare-hare a Gaza.
Daga cikin waɗanda suka rasun akwai mutum 33 da aka kashe a sa’o’i 24 da suka gabata, kamar yadda Ma’aikatar Lafiyar ta bayyana a sanarwar da ta fitar, inda ta ce akwai mutum 77,765 da suka samu rauni a Gaza tun bayan da yaƙin ya ɓarke.
0641 GMT — Hezbollah ta yi iƙirarin kai hari kan sojojin Isra’ila a iyakar Lebanon
Ƙungiyar Hezbollah da ke Lebanon ta yi iƙirarin cewa ta kai hari kan sojojin Isra’ila a kusa da kan iyakar ƙasar.
A wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta ce mayaƙanta sun kai hari da makamai masu linzami da igwa kan tawagar sojojin Isra’ila a harabar barikin sojoji na Branit.
Kawo yanzu rundunar sojojin Isra’ila ba ta ce komai kan wannan sanarwa ta Hezbollah ba.
0551 GMT — Amurka za ta tabbatar Isra’ila da Hamas sun ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta ‘yanzu’— Blinken
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya jaddada kiransa ga Hamas domin ta amince da tsagaita wuta tare da sakar mutanen da ta yi garkuwa da su a yayin da ya gana da shugabannin Isra’ila.
“Ko a wannan mawuyacin hali muna so mu tabbatar da ganin an mayar da mutanen da aka yi garkuwa da su gida sannan a tsagaita wuta yanzu,” in ji Blinken a yayin da ya gana da shugaban Isra’ila Isaac Herzog.
04:30 GMT — Jami’ar Columbia ta yi barazanar korar masu zanga-zangar adawa da yaƙin Gaza
Jami’ar Columbia ta yi barazanar korar ɗaliban da ke zanga-zangar adawa da hare-haren da Isra’ila take kai wa Gaza.
Jami’ar ta ce ɗaliban da ke zaman dirshan a wani ginin harabar makarantar a matsayin zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu, na fuskantar korar daga karatunsu, saboda sun karya doka.
“Ɗaliban da suka mamaye ginin na fuskantar kora,” in ji ofishin kula da harkokin jama’a na Columbia a cikin wata sanarwa, inda ya ƙara da cewa an ba masu zanga-zangar “damar fita cikin lumana” amma a maimakon haka suka ƙi tare da kara ta’azzara lamarin.
Ana kallon wannan a matsayin keta hakkin ɗaliban da ƙoƙarin hana su faɗin albarkacin bakinsu a ƙasar da take iƙirarin kare ƴancin ɗan’adam.
2130 GMT —Mamayar da Isra’ila za ta yi a Rafah za ta zama ‘mummunan bala’in da baki ba zai iya faɗa ba’ — MDD
Babban jami’in ba da agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya Martin Griffiths ya yi gargaɗin cewa duk da kiraye-kirayen da ƙasashen duniya ke yi wa Isra’ila na ta ƙyale birnin Rafah na kudancin Gaza, “tana dab da fara kai hare-hare ta ƙasa.”
Griffiths ya ce “Maganar gaskiya ita
ce, farmakin ƙasa a Rafah babban bala’i ne da baki ba zai iya misalta shi ba. Babu wani shirin jinƙai da zai iya daƙile hakan,” in ji Griffiths, bayan da firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin ƙaddamar da farmaki a Rafah.
Griffiths ya ce ci gaban da aka samu daga Isra’ila na kai agaji a Gaza “ba za a yi amfani da shi ba don shiryawa ko kuma tabbatar da harin da sojoji za suka kai a Rafah ba.”
Netanyahu ya yi barazanar mamaye Rafah “ba tare da la’akari da ko an cim ma yarjejeniyar sulhu kan mutanen da ake garkuwa da su ba” da suke hannun ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas.
Ga dukkan alamu dai ya yi kalaman nasa ne da nufin gamsar da abokan tafiyarsa masu tsattsauran ra’ayi, amma babu tabbas ko za su yi wani tasiri kan duk wata yarjejeniya da ta kunno kai da Hamas.
“Za mu shiga Rafah kuma za mu kawar da bataliyoyin Hamas a can – tare da ko ba tare da wata yarjejeniya ba, don cim ma nasarar gaba ɗaya.”
Hamas ta ce Netanyahu ba zai cim ma komai ba idan sojojin Isra’ila suka mamaye Rafah inda Falasɗinawa sama da miliyan 1.5 suke samun mafaka daga mamayar Isra’ila da kuma kai hare-hare a wasu wurare a Gaza.

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button