Uncategorized

Borno: Tubabbun ’Yan Boko Haram Sun Sake Daukar Makamai, Sun Farmkaki Jami’an Tsaro

4

 Borno: Tubabbun ’Yan Boko Haram Sun Sake Daukar Makamai, Sun Farmkaki Jami’an Tsaro

Borno: Tubabbun ’Yan Boko Haram Sun Sake Daukar Makamai, Sun Farmkaki Jami’an Tsaro
Borno: Tubabbun ’Yan Boko Haram Sun Sake Daukar Makamai, Sun Farmkaki Jami’an Tsaro @Kumuryamedia

Zagazola Makama, wani mai sharhi kan al’amuran tsaro ya ruwaito cewa tubabbun ‘yan Boko Haram sun farmaki jami’an tsari a Borno Makama, ya ce lamarin ya faru a ranar Laraba inda wadanda ake zargin suka kona shingayen bincike na hukumar NDLEA da NCS Jim kadan bayan kona shingayen ne Makama ya ce ‘yan ta’addan suka farmaki ofishin rundunar ‘yan sanda na Kasuwar Fara 

Jihar Borno – Wasu da ake kyautata zaton ‘yan ta’addan Boko Haram ne da suka tuba sun sake daukar makamai yayin da suka farmaki jami’an tsaro a jihar Borno.

An ruwaito cewa sun kona shingayen binciken kwakwaf na hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) da hukumar kwastam ta Najeriya (NCS). 

‘Yan Boko Haram sun farmaki jami’an tsaro Zagazola Makama, wani mai sharhi kan al’amuran ta’addanci a yankin tafkin Chadi, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba. LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng Makama ya rahoto cewa tubabbun ‘yan Boko Haram din sanye da kakin sojoji sun mamaye Kasuwar Fara a Maiduguri inda suka fatattaki jami’an hukumomin. Ya ce ‘yan ta’addan sun kona dukkanin shingen binciken, inda suka koma ofishin ‘yan sanda reshen Kasuwar Fara da yunkurin sakin mambobinsu takwas da ke tsare. ‘Yan sanda sun yi artabu da mayakan Makama ya ce an kama wadanda ake tsare da su ne a ranar 24 ga watan Afrilu yayin wani samame da ‘yan sanda suka kai a wani kauye mai suna Kasuwan Fara, in ji jaridar The Cable. Mai fashin bakin ya ce jami’an ‘yan sandan sun yi artabu da ‘yan ta’addan, inda ya kara da cewa an fi karfin ‘yan ta’addan lamarin da ya tilasta su guduwa daga wurin. 

Ya ce kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Kenneth Daso, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin kamo maharan. Kudin fansho: Ma’aikata a Borno sun koka A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa ma’aikata a jihar Borno sun koka kan Naira 4,000 da wasu tsofaffin ma’aikata ke karba a matsayin kudin fansho a wata. Kungiyar kwadago reshen jihar yayin da take rokon Gwamna Babagana Zulum da ya duba lamarin ta yi nuni da cewa babu abin da kudin za yi a wannan yanayin na tsadar rayuwa. 

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button