Barcelona na son Nunez, Chelsea na kokarin sayen Osimhen

 Barcelona na son Nunez, Chelsea na kokarin sayen Osimhen



Ɗan wasan gaba a Liverpool da Uruguay mai shekara 24, Darwin Nunez ya kasance wanda Barcelona ta shiga farautar domin maye gurbin Robert Lewandowski na Poland mai shekra 35. (Sun)


Nunez ya hura wutan jita-jita da ake yadawa kan cewa zai barin Liverpool bayan goge duk wani hotonsa na Anfield a shafinsa na Instagram. (90min)


Mai buga gaba a Ingila Jadon Sancho, ɗan shekara 24, baya son komawa Manchester United a karshen kwantiraginsa na zaman aro da ya je Borussia Dortmund. (Talksport)


Chelsea ta matsa kaimi a farautar ɗan wasan Shakhtar Donetsk da aka yiwa kudi fam miliyan 65 daga Ukraine, Georgiy Sudakov, mai shekara 21, akwai ƙungiyoyi irinsu Arsenal da Manchester City da Liverpool da ke bibbiyarsa. (Mail)


Chelsea na kuma son sayo ɗan wasan Najeriya da ke taka leda a Napoli, Victor Osimhen mai shekara 25, da yarjejeniyarsa ta bashi daman tafiya wata kungiya a kan fam milyan 100. (Sky Italia)


Mai tsaron raga a Atletico Madrid da Slovenia Jan Oblak, mai shekara 31, ya kasance wani ɗan wasa da Chelsea ke farauta a wannan kaka, sai dai ƙungiyar da yake takawa leda a Sifaniya na kokarin kara masa kudi domin ta rike shi.(Fichajes)


West Ham United da Tottenham Hotspur na kan gaba wajen neman saye ɗan wasan Brentford da Ingila, Ivan Toney mai shekara 28 a wannan kaka, inda kowanne su ke shirin gabatar da kusn tayin fam miliyan 50.(Football Transfers)


Mai buga gaba a Sweden Viktor Gyokeres ɗan shekara 25, yaƙi ya yanke hukunci kan cigaba da zama a Sporting Lisbon yayinda Arsenal ta kwaɗaitu da shi. (Standard)


Arne Slot, da ake sa ran ya maye gurbin Jurgen Klopp a Liverpool, na iya komawa Feyenoord domin dauko ɗan wasan tsakiyar Netherlands Mats Wieffer,mai shekara 24, da mai tsaron baya Lutsharel Geertruida, mai shekara 23. (Football Insider)


Sevilla na cikin ƙungiyoyin da ke farautar kocin Leicester City Enzo Maresca mai shekara 44, bayan ya taka rawar sake dawo da ƙungiyar cikin Firimiya. (Mail)


Manchester United na neman wanda zai saye ɗan wasanta na Brazil mai shekara 32 Casemiro a wannan kaka a kokarin rage kudaden kashewa. (TEAMtalk)



Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url


';