Ba mu yarda a bai wha Amurka da Faransa damar kafa sansani a Najeriya ba - 'Yan Arewa

Ba mu yarda a bai wa Amurka da Faransa damar kafa sansani a Najeriya ba - 'Yan Arewa


Wasu manyan shugabanin arewacin Najeriya sun yi wa gwamnatin ƙasar gargaɗin kan bai wa Amurka da Faransa damar kafa sansanin soji a Najeriya bayan korarsu da aka yi a yankin Sahel.

Cikin wata wasiƙa da suka aike wa shugaba Bola Tinubu a ranar Juma'a da kuma shugabancin Majalisun ƙasar, shugabannin sun ce kada gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayar da kai bori ya hau.

Cikin waɗanda suka sanya hannu kan wasiƙar akwai Farfesa Abubakar Siddique Mohammed na Cibiyar Ci gaban Dimokradiyya da bincike da ba da horo ta (CEDDERT), da ke Zaria, da Farfesa Kabiru Sulaiman Chafe tsohon Ministan mai, da Farfesa Attahiru Muhammad Jega tsohon shugaban INEC da Farfesa Jibrin Ibrahim na CDD da Auwal Musa Rafsanjani shugaban (CCISLAC) sai kuma Y. Z. Ya’u na CITAD.

Wasiƙar ta yi zargin cewa gwamnatocin Amurka da Faransa sun yi kamun kafa wajen Najeriya da kuma wasu ƙasashe da ke mashigar tekun Guinea, tare da samar da wata yarjejeniya da za ta basu samar sake tsugunar da dakarunsu da aka kora daga Mali da Burkina Faso da kuma Nijar a yankin.

Waɗanda suka aike wasiƙar sun nuna damuwa kan cewa Najeriya na wani wuri ne da yake mai santsi tsakanin ƙasashen yakin mashigar tekun Guinea, idan ta bayar da kai bori ya hau hakan zai iya jefa tsarin tsaronta na cikin gida cikin hadari.

"Korar dakarun Amurka da na Faransa da aka yi a baya-bayan nan daga Nijar saboda gaza katabus, ya aza ayar tambayar amfanin samar da sansanin sojin ƙasashen waje'', kamar yadda wasiƙar ta yi bayani.

'Yan arewar ta cikin wasiƙar sun ce babban maƙasudin samar da sansanonin shi ne a magance matsalar ta'addanci a yankin Sahel, amma babu wani abu da aka gani sai ƙaruwar ta'addanci tun bayan samar da sansanonin.

"Yana da kyau mu faɗa wa kowa a bayyane babu komai sai hadari cikin samar da sansanonin soji irin wadannan," in ji sanarwar.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url


';