Aston Villa na zawarcin Iheanacho, Jesus ba ya son ya bar Arsenal, Xavi na son Silva

 Aston Villa na zawarcin Iheanacho, Jesus ba ya son ya bar Arsenal, Xavi na son Silva



Manchester United ce a gaba- gaba wajan sayan dan wasan tsakiya na Crystal Palace da Faransa a tawagar 'yan kasa da shekaru 21,Micheal Olise dan shekara 22. (ESPN)


Ita ma Juventus ita ce a gaba wajan sayan dan wasan Ingila da Manchester United Mason Greenwood, dan shekara 22, wanda aka ba da shi aro ga kungiyar Getafe ta Safaniya. (i Sport)


Kocin Barcelona Xavi ya fadawa kungiyar cewa yana son dan wasan tsakiya na Manchester City da Portugal Bernardo Silva, mai shekara 29, amma kuma Bayern Munich ita ma tana zawarcinsa. (Sport - in Spanish)


Chelsea na nazari a kan mai tsaron ragar Poland Wojciech Szczesny, mai shekara 34 wanda tsohon golan Arsenal ne wanda yanzu ke wasa a Juventus. (Tutto Juve - in Italian)

Chelsea ta bi sahun Newcastle wajan bibiyar halin da tsohon dan wasan tawagar Ingila Tosin Adarabioyo mai shekara 26 ya ke ciki wanda zai bar Fulham a bazara (Fabrizio Romano)


Manchester City na cikin wadanda suka so daukar dan wasan baya na Borussia Dortmund da Netherlands Ian Maatsen, dan shekara 22 a ranar Laraba wanda Chelsea ta bada shi aro . (TBR Football)


Dan wasan gaban Brazil Gabriel Jesus, mai shekara 27, ya tashi tsaye wajan ganin ya ci gaba da taka leda a Arsenal yayin da rahotanni ke cewa watakila ya bar kungiyar a bazara . (Sun)


Kocin Brighton Roberto de Zerbi kawo yanzu yana cikin jerin sunnayen wadanda da Bayern Munich ke son ta dauka a matsayin sabon kocinta bayan Ralf Rangnick ya ki amincewa da tayin da ta yi masa. (Bild - in German)


Leicester City na zawarcin dan wasan tsakiya na Coventry City da Ingila Callum O'Hare, mai shekara 26. (Football Insider)


Celtic na cikin kungiyoyin da ke son su dauko mai tsaron ragar Aston Villa da Finland Viljami Sinisalo, mai shekara 22, wanda aka bada shi aro ga Exeter City tun kakar bara. (Sun)


Brighton da Fulham da West Ham da Benfica na zawarcin dan wasan gefe na Vitoria de Guimaraes da Portugal Jota Silva (Rudy Galetti)


Dan wasan tsakiya na Aston Villa da Brazil Diego Carlos, mai shekara 31, na cikin wadanda AC Milan ta ke son ta saya. (Teamtalk)


Villa na son ta dauko dan wasan gaba na Leicester da Nigeria Kelechi Iheanacho, mai shekara 27, a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasa mai kai hari na Ingila Ollie Watkins, mai shekara 28. (Football Insider)


Inter Miami ta fara tattaunawa da dan wasan gefe na Benfica da Argentina Angel di Maria mai shekara 36. (ESPN Argentina - in Spanish)

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url


';