Ana zargin Isra'ila da laifukan yaƙi bayan kisan yaro Bafalasɗine

 


Ana zargin Isra'ila da laifukan yaƙi bayan kisan yaro Bafalasɗine


Da safiyar ranar 29 ga watan Nuwamban bara, wasu yara Falasɗinawa suka arce a guje daga wani wuri da suke wasa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.


Mintuna kaɗan bayan haka, biyu daga cikinsu - Basil mai shekara 15 da Adam ɗan shekara takwas - suka faɗi a mace sanadiyyar harbi daga sojojin Isra'ila.


A wani ɓangare na binciken da BBC ke yi kan ayyukan sojojin Isra'ila a Gaɓar Yamma, wanda ke ƙarƙashin mamayen Isra'ilar na tsawon kimanin shekara 50, mun tattara bayanai kan abubuwan da suka faru a ranar da aka kashe yaran biyu.


Bidiyon da aka ɗauka da wayar hannu da kuma na kyamarar tsaro, da bayanan ayyukan sojojin Isra'ila a lokacin, da bayanai daga shaidu, da nazari kan wurin da lamarin ya faru, duk sun haɗu sun nuna ƙwaƙƙwarar shaidar an samu mummunan take haƙƙin bil'adama.


Bayanan da muka tattara sun sanya babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da hakkin bil'adama da yaƙi da ta'addanci, Ben Saul, ya bayyana cewa "da alama akwai laifin yaƙi" a kisan da aka yi wa Adam.


Wani masanin shari'a, Dr Lawrence Hill-Cawthorne, ya bayyana cewa ana "yawan" amfani da ƙarfi fiye da ƙima.


Rundunar Sojin Isra'ila ta IDF ta bayyana cewa tana "nazari" kan yadda mutuwar yaran ta faru, sai dai rundunar ta ce ana "buɗe wuta ne kawai a lokacin da ake son a kawar da wata barazana ko kuma domin yin kame, idan sauran matakai sun gaza".


Yayin da aka samu ƙarin tashin hankali a Gaɓar Yamma tun bayan harin da Hamas ta kai cikin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, BBC ta kuma gano yadda aka ɓata gidajen Falasɗinawa da zane-zane a bango, da yi wa Falasɗinawa barazana da makamai tare da faɗa musu cewa su bar yankin zuwa cikin ƙasar Jordan mai maƙwaftaka.


Haka nan akwai wasu alamu na yiwuwar cewa an wulaƙanta gawar wani ɗan bindiga Bafalasɗine.

Bidiyon da aka dauka ranar 29 ga watan Nuwamban ya nuna Basil tsaye kusa da wani kantin sayar da kayayyaki, wanda ke jerin kantunan da aka rufe. A lokacin da sojojin Isra'ila suka je yankin, an gaggauta rufe kantuna a Jenin, wani birni a Gabar Yamma da Kogin Jordan, a yankin da ke karkashin ikon Isra'ila. Sabanin yankin Gaza da Hamas ke iko da shi, ba ƙungiyar ce ke iko da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan ba.


Shaidu sun ce an yi ta jin karar harbe-harben sojojin Isra'ila a sansanin 'yan gudun hijira da ke Jenin.


Adam, mai sha'awar kwallon kafa, kuma magoyin bayan Messi, na tsaye tare da yayansa Baha mai shekara 14.


Kimanin jimillar yara tara ne a kan titin, da dukkansu kyamarar tsaro ta CCTV ta dauka tare da kusan dukkan abin da ya faru a yankin.

Yan mitoci kalilan daga inda yaran ke tsaye, sai ga jerin-gwanon motocin Isra'ila akalla shida sun shawo kwana, suka nufi inda yaran ke tsaye. Nan take yaran suka fara tsorata, kuma da dama suka fara janyewa daga wurin.


A daidai wannan lokaci ne bidiyon da aka ɗauka da waya ya nuna yadda aka bude kofar gaba ta daya daga cikin motocin yakin. Sojan da ke cikin motar ya dauki tsauki saitin yaran.


Daga nan Basil na ruga tsakiyar titin, yayin da Adam ke gaba da shi, mita 12 daga inda sojojin suke, inda ya fara gudu.


Yayin nazarin lamarin, BBC ta gano cewa an harba harsasai a yankin. Harsasai hudu8 sun sami wani karfin turken lantarki, da kofofin kantin da ke wajen, yayin da wani harsasshin ya rasa wata karamar mota da ke tsaye a wurin tare da kuma da katakon da ake rike wa don hawa matattakala.


Rahoton likitoci da BBC ta gani ya nuna cewa an harbi Basil har sau biyu a kirjinsa.


Wani harsashin ya kuma samu Adam mai shekara takwas a ƙeyarsa a lokacin da yake guduwa, dan'uwansa Baha ya yi yunkurin janye shi domin kare shi daga harbin, bayan da ya gan shi cikin jini a lokacin da ya yi kururuwar neman motar agaji.

Sai dai bakin alkalami ya riga ya bushe. Baha ya ce a gabansa Adam da abokinsa Basil suka mutu.


“Na kadu sosai da faruwar lamarin; Ba ma na tunannin me zai faru da ni. Na yi kokarin yi masa magana, na fara kiran sunansa, ‘Adam, Adam!’ amma bai amsa ba saboda ransa ya rabu da gangar jikin nasa,'' kamar yadda Baha ya shaida wa BBC.


Kafin a harbe shi, an ga Basil na rike da wani abu a hannunsa. Ba a iya gane ko mene ne ba.


Daga baya rundunar sojin Isra'ila ta wallafa hoton da ta dauka a wurin, wanda ta ce yana nuna abin fashewa a hannun yaron.


Mun bai wa kwararrun masana - ciki har da lauyoyin kare hakkin bil-adama, da masu binciken laifukan yaki da masana yaki da ta'addanci, da kuma mambobin MAjalisar Dinkin Duniya da sauran hukumomi masu zaman kansa - binciken namu. Inda wasu suka bayar da sharhinsu ba tare da ambata suna ba.


Masanan sun yarda cewa ya kamata a binciki lamarin, inda ma wasu suka ce batun ya saba wa dokokin duniya.


Ben Saul, jami'in Majalaisar Dinkin Duniya da ke aiki a bangaren kare hakkin bil-adama da yaki da ta'addanci na majalisar, ya ce akwai ayar tambaya kan cewa ya halasta a yi amfani da makamin da aka yi amfani da shi kan Basil koda kuwa yana rike da abin fashewa.


''Kan batun Adam, wannan saba wa dokokin jin kai na duniya ne wadanda suka haramta kai hari kan farar hula da gangan, wanna laifin yaki ne tare da saba wa hakkin bil-adama,'' in ji mista Saul.


Dakta Lawrence Hill-Cawthorne, darakta a cibiyar nazarin dokokin duniya a jami'ar Bristol, ya ce: "Sojojin na cikin motocin yakin. Ko da akwai barazana, ya kamata su janye daga yankin daga baya su shirya yadda za su kama yaran, a maimakon bude musu wuta ta hanyar amfani da makamin 'lethal force', wanda ya ci karo da dokokin duniya.''


IDF ta ce wadanda take zargin na yunkurin jefa abin fashewa kan dakarunta, lamarin da ka iya jefa su cikin hatsari. ''Dakarun sun mayar da martani ta hanyar bude wuta, inda aka gano harbin ya same shu,'' in ji sojojin na Isra'ila.


Amma shaidar bidiyon da muka yi nazari, wnda kuma shaidunmu suka tabbatar, ya nuna cewa Adam ba ya rike da makami, kuma yana tsaka da gudu a lokacin da aka harbe shi a bayan kansa.


Rundunar IDF din dai ta ce ''ana sake nazarin'' batun mutuwar Basil da Adam, wanda take yi a kan kowane mutuwar kowane yaro a Gabar Yamma da Kogin Jordan, sakamakon ayyukan sojojinta.


To sai dai tsoffin sojojin Isra'ila da suka kallon hujjar ta BBC, sun ce sun tabbata bangaren shari'ar Isra'ilar zai kare sojojin da suka yi amfani da makamin na ' lethal force' koda kuwa bai dace su yi amfani da makamin ba.


Wani tsohon sajan, da ya yi aiki a Gabar Yamma da Kogin Jordan daga 2018 zuwa 2020 ya ce ''kisan da sojan Isra'ila zai yi wa Bafalasdine ba a fiye daukartsa a matsayin kisan kai ba kamar yadda za a yi a Isra'ila'', kuma akwai yiyuwar ba za a tuhumi soja da laifin ba, a irin abin da ya faru da Adam.


Wasu alkaluma daga hukumar kare hakkin bil-adama da Isra'ila Yesh Din ya nuna cewa kashi daya cikin 100 na duka korafe-korafen da ake shigarwa kan sojojin Isra'ila na karewa ne matakin shigar da kara.


Bidiyon harin da Hamas ta kai ranar 7 ga watan Okotoba, wanda aka kashe mutum 1,200 tare da yin garkuwa da mutum 253, lamarin da ya girgiza mutanen Isra'ila da ma duniya baki daya.


Tun da nan ne kuma hankalin duniya ya karkata kan yakin da kuma ayyukan jin kai a Gaza, inda aka kashe fiye da mutum 34,000, kamar yadda ma'aikatar lafiyar Hamas da ke GAza ta bayyana.


A lokaci guda kuma, sojojin Isra'ila suka karfafa ayyukansu a Gabar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye, lamarin da ya sa shekarar da ta gabata ta kasance shekarar da aka fi samun mutuwar kananan yara a yankin.


Jimillar kananan yara 124 ne aka kashe a 2023, in ji Unicef, inda ta ce 85 daga ciki an kashe su ne bayan 7 ga watan Okotoba.


Kawo yanzu a 2024, kananan yaran Falasdinawa 36 ne 'yan kama wuri zauna ko sojojin Isra'ila suka kashe.


Tun da ba a daukar Gabar Yamma da Kogin Jordan a matsayin filin daga, bai kamata ba a yi amfani da karfi, kamar yadda dokokin duniya suka tanadar.

A yayin da rundunar IDF ke ci gaba da boye dokokinta na amfani da makamin, tsofaffi da sojojin Isra'ila sun shaida mana cewa ana amfani da makamin da ke kisa ne kawai a matsayin mataki na karshe idan aka tabbatar da cewa ana cikin hatsarin rasa rai. Daga nan ne za a yi amfani da makamin.


Sun ce ana fara wa ne da gargadi na fatar baki da harsunan Larabci da na Hebrew, kafin a kai ga amfani da makaman da ba sa kisa kamar tiya gas, sannan a kai matakin harbi a kafafu, duka kafin a kai ga matakin kisa.


BBC ta samu ganin rahoton lafiya na hukumar PA da ke kula da ma'aikatar lafiyar Gabar Yamma da Kogin Jordan, da ya nuna cewa kananan yara 112, masu shekaru tsakanin biyu zuwa 17 da sojojin isra'ila suka kashe tsakanin Janairun 2023 zuwa Janairun 2024.


Ba mu san hakikanin abinda ya haddasa harbin wadannan yara ba, kuma abu ne mai yiwuwa cewa wasu dalilan na iya haifar da hatsarin ga rayukan sojojin na Isra'ilar.


To sai dai bincikenmu ya nuna cewa kusan kashi 98 na yaran na da raunuka a saman jikinsu, inda harbi ka iya yin mummunar illa, abin da ke nuna cewa sojojin sun yi harbin ne don su kashe, maimakon su raunata.


Lamarin da ke aza ayar tambaya game da ko sojojin na bin ka'idojin mayar da martani a Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma yadda dabi'ar sojojin wajen harbi kisa.

Bayan kwashe fiye da mako biyar muna nazarin tasirin ayyukan sojin Isra'ila a Gabar Yamma da Kogin Jordan, mun ga hujjoji na abubuwan da suka faru, wadanda suka haifar da ayar tambaya kan ayyukan sojin.


BBC ta samu shaidar wani gagarumin harin da sojojin Isra'ila suka shafe sa'o'i 45 suna yi a sansanin 'yan gudun hijira na Tulkarm a watan Janairun 2024, da nufin fatattakar wata kungiyar msu dauke da makamai da aka fi sani da masu turjiya a yankin.


Bayan hakan ne kuma, wasu falasdinawa da dama suka shaida mana cewa sojojin Isra'ila sun yi ta yi musu barazana da bindiga suna ce musu su koma kasar Jordan mai makwabtaka.


Rundunar sojin Ira'ila ta ce za ta yi nazarin duk wani korafi da aka shigar kan yi wa fararen hula barazana.


Haytham, mai shekara 12, wanda Bafalasdine ne dan asalin Canada, ya ce wani sojan Isra'ila ya yi masa barazana da wuka, ikirarin da dan'uwansa da mahaifinsa suka tabbatar.


A wajen wasu iyalan da ke sansanin, mun samu wani kyalle na masallacin al-Aqsa, wuri na uku mafi daraja wurin musulmi - da aka yi zargin cewa sojojin Isra'ila ne suka cire shi daga masallacin.


A jikin kyallen akwai hotunan taurari da ka yi wa fenti, sai kuma wani da aka rubuta 7 ga watan Oktoba da harshen Hebrew, wanda ke nufin harin da Hamas ta kai Isra'ila.


Rundunar IDF ta ce wannan barna ta saba wa ''ka'idojin IDF'' kuma ya saba wa abin da take tsammani daga sojojinta.


An tarwatsa saman gidan, aka lalata kayan kichin na gidan, aka wargaza kayan wasan yaran gidan, tare da fasa talabijin din gidan. Kuma wanna shi ne kwatankwacin abin da aka yi wa duka gidajen da ke sansanin.


Dakta Eitan Diamond, babban jami'i masanin shari'a a cibiyar kula da dokokin jinkai ta duniya da ke Diakonia a birnin Kudus, ya ce ''Barnata kayyaki, kamar cire kyalle mai dauke da hotunan taurari da rubutun 7 ga watan Okotoba a masallacin Kudus, karara laifi ne''.


Rahotonni barazana ga kananan yara da wuka a sansanin'yan gudun hijira na Tulkarm da sauran da aka yi wa da bindiga, za su iya zama laifukan da suka saba dokokin duniya.


A wani hari da sojojin Isra'ilar suka kai, bayan sun kashe wani mutum da aka yi zargin cewa mayakin Falasdinu ne da ke dauke da abin fashewa, shaidu sun gaya mana cewa an yi wa gawarsa fitsari, tare da dukanta, aka kuma daureta tare da janta a kasa a kan titi.


An nuna wa BBC gawar da aka dauren. Bayan nazarin jinin da ya zuba a wurin, mun gano cewa tufafi da wayar da aka bari sun yi daidai da tufafin da aka yi amfani da shi wajen daure gawar da muka gani hotuna.

Mun kuma nuna wa wani kwararen masani, Farfesa Marco Sassoli, masanin dokokin duniya a jami'ar Geneva, wanda kuma ya ce ''Dole ne a martaba gawarwakin mutane, ko da an kashe su bisa ka'ida. Abin da rahotonku ya kunsa ya saba wa dokokin duniya, kuma zai iya zama laifin yaki.''


Rundunar IDF ta ce bayan nazarin gawar mayakin, an samu abin fashewa, kuma jami'in kungiyar agaji ta Red Crescent ya ki taba gawar.


"Da wannan dalili, dole ne dakarun IDF su daure hannaye da kafafunsa don tabbatar da tsaron lafiyarsu, tare da dubawa ko akwai makami a karkashin gawar''.


Wasu tsoffin sojojin Isra'ila da suka yi nazarin shaidar BBC, sun ce suna fargaba kan yadda ayyukan sojojin Isra'ila a Gabar Yamma da Kogin Jordan ke kara tursasa wa Falasdinawa masu dauke da makamai''.


"Abubuwa suna kara rincabewa."


Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url


';