Computer Science

Asali Da Tarihin Samuwar System UI Da UX A Ilimin Computer

4

 

Asali Da Tarihin Samuwar System UI Da UX A Ilimin Computer
KUMURYAMEDIA IMAGE

Asali Da Tarihin Samuwar System UI Da UX A Ilimin Computer 

Tarihin UX/UI design

Menene UX/UI design? to duk da nayi bayani akan ma’anar UX da kuma UI a fayyace a cikin darasin da nayi a Flowdiary yanzu ma zan ƙara yi a taƙaice. Da farko dai na zaɓi rubuta UX ne saboda shine yake fara zuwa a farko duk da dai ko a yaya aka rubutasu daidai ne. Da farko zan fara da amsa wasu ƴan tambayoyi da suke shigowa cikin akwatin saƙonni na, na social media.

Menene UX? 

UX yana nufin “User Experience” wanda wannan fasaha ta mayar da hankali ne ɓangaren tsara duk wani mataki da masu amfani da na’ura zasu fuskanta, misali idan user ya danna madanni me zai faru, ko shafin da zai kaishi kokuma abinda zai sauke dadai sauransu, sannan a UX ne ake tsayawa ayi tunani akan wane irin design manhaja kokuma shafin yanar gizo yake buƙata, kuma dai a UX ne ake tantance shafuka nawa ake buƙata, wane irin matakai user zai taka domin kaiwa ga cimma dalilin shigowarshi cikin wannan manhajar.

Menene UI?

UI yana nufin “User Interface”, shikuma UI design ana fasalta yanayin yanda na’ura zata kasance ne, kuma ayi design ɗin ta yanda wanda yayi design ɗin zai iya gwadawa sannan ya gayyaci masu gina wannan shafin na yanar gizo waƴanda akafi sani da “Front-end Web Developers” kokuma “Full-Stack Web Developers” idan kuma design ɗin na software ne to zaka bawa masu gina wannan manhajar ta na’ura mai ƙwaƙwalwa wato “Software Engineers” domin suga duk irin motsi da shige da ficen da akeso wannan manhajar ta kasance dasu.

Shin UX/UI designer yana gina Website ko Software kokuma Application?

A’a sam-sam wannan ba aikin UX/UI designer bane, shi UX/UI designer yana fasalta yanda shafin yanar gizo zai kasance ne, kokuma manhajojin na’ura mai ƙwaƙwalwa, sannan ya miƙawa Engineers kokuma ya gayyacesu su gani sannan su kwaikwayi wannan design ɗin da yayi domin su gina asalin software ɗin, saboda su software engineers suna da ƙwarewa ɓangaren yarukan gina manhajojin na’ura mai ƙwaƙwalwa, amma basu da ƙwarewa ɓangaren design, wannan dalilin yasa idan aka basu UI design sai su kwaikwaya su ƙirƙiri manhajojar da za’ayi amfani da ita. Saboda haka design ɗin da UX/UI designer yakeyi, yana yinsu ne saboda sauƙaƙewa Engineers gurin ƙirƙira.

Bayan UX da UI akwai CX.

Menene CX? CX yana nufin “Customer Experience” Shikuma CX ya mayar da hankali ne ɓangaren kula da buƙatar abokin cinikayya wato “Customer” da kuma tabbatar da an janyo hankalinshi kan kayan da suka dace da ra’ayinshi, kunga bambancin da yake a tsakanin UX da kuma CX shine, shi CX ana yin tunanin matakan da abokin ciniki zai taka, shikuma UX ɓangaren mai amfani da manhaja. To wannan bazan zurfafa bayani a kanshi ba, saboda zamuyi tarihin UX da UI ne.

Mu dawo kan batun mu na tarihin UX/UI. Tarihin ya fara ne tun shekarun baya masu yawa, da suka shuɗe, a lokacin da na’ura mai ƙwaƙwalwa ta kasance sabon abu, amma dabarun UX/UI sun fara kasancewa masu amfani tun a shekarar 1900s. A shekarar 1960s, kuma na’ura mai ƙwaƙwalwa ta kasance tana iya bayyana rubutu ne kawai, akan screen ɗinta. 

Na’urar tafi da gidanka wacce akafi sani da “Smartphone” ta samu shiga gari a 1992s, a lokacin da masana’antar Apple ta ƙirƙiri na’urar da ake yiwa laƙabi da “Macintosh” a shekarar 1984 tana iya nuna hotuna, rubutu da alamu wato “Icons” wato a taƙaice dai tazo da “Graphical User Interface (GUI)” duk da cewa ƙungiyar Xerox PARC (Palo Alto Research Center) sun riga masana’antar Apple gabatar da na’ura mai (GUI) mai suna “Xerox Alto” tun a shekarar 1970s.

Masana’antar IBM ta taka irin nata rawar ganin, a shekarar 1992 wanda ta ƙirƙiri wata na’ura mai ƙwaƙwalwa mai suna “Simon Personal Communicator” wannan na’ura tazo da abubuwa kamar su email, fax, pager bugu da ƙari tazo da applications irin su calendar da kuma address book. Waƴannan manhajojin da tazo dasu, suma duk akwai fasahar UX/UI a cikinsu.

A shekara ta 1990s, kuma shafin yanar gizo yazo da ƙalubale masu yawa da kuma damarmaki. A lokacin da aka gabatar da HTML a 1991s shikuma CSS a 1994s domin ginawa da ƙawata shafukan yanar gizo. A shekarar 2000s an samar da dabarun da ake kira da “user-centered design” (UCD) wannan dabarun sun mayar da hankaline ɓangaren kula da buƙatun masu amfani da manhajar na’ura mai ƙwaƙwalwa, shafukan yanar gizo da makamantansu, sannan a daidai shekarar 2000s zuwan ƙananan na’urorin tafi da gidanka wato “Smartphone Devices” ko muce yaɗuwarsu, saboda masana’antar IBM sun gabartar da Smartphone tun a 1992s, ya angiza masana domin samar da mafita ɓangaren UX/UI.

A yau fasaha ko muce dabarun UX/UI sun kasance abu mai muhimmanci ta yanda ake matuƙar buƙatarsu, a ɓangarorin da dama kamar samar da manhajojin manya-manyan na’urorin zamani da ƙananan na’urorin tafi da gidanka, da shafukan yanar gizo.

Matakin aikin ƙwararren UI Designer ya fara samun daraja a masana’antun fahasa a 1980s a lokacin da dabarun Graphical User Interface (GUI) suka zama gama gari, an gabatar da na’urar masana’antar Apple wacce muka yi bayani a sama, mai suna Macintosh ta farko a shekarar 1984s, wannan na’ura ta taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa fasahar UX/UI a duniya, a matsayin babbar fasaha da ta kawo ci gaba. Wannan yaja hankalin wasu masana’antun ƙere-ƙere na lokacin.

Abinda yasa kukaji ina ta maganar GUI, shine indai na’ura tana da fasahar Graphical User Interface to ana buƙatar ƙwararru a ɓangaren UX/UI design saboda su tsara kuma su fasalta yanayin yanda akeso Interface na na’ura mai ƙwaƙwalwa ya kasance, da kawar da duk wani abu da ya zama ba dole ba, wanda zai iya janyowa masu amfani da na’urar ɓata lokaci mara dalili.

UI design ya cigaba da zama abu mai daraja ko muce aiki mai daraja, a masana’antun fasaha, saboda mutane suna ƙara cin karo da sababbin ƙere-ƙeren fasaha, wanda hakan yasa ake buƙatar ƙwararru a ɓangaren domin suyi design daidai da kowacce sabuwar ƙira da akayi, sannan su samar da duk wata hanya da mutane zasuji daɗin amfani da manhaja ko shafin yanar gizo. 

Ga jerin wasu daga cikin mutanen da suka bada gudun mawa a duniyar UI design.

1. Jony Ive: Wannan designer ɗin yayi aiki a masana’antar Apple, inda ya shugabanci rukunin design na UI ɗin iPhone, iPod, da kuma MacBook, a lokacin yana matsayin “Chief Design Officer (CDO)” duk da cewa bashi kaɗai yayi aikin ba, amma shine ya shugabanci rukunin da suka samu kyakkyawan kusanci da Engineers, sannan kuma sunyi design masu kyau kuma masu jan hankali.

2. Susan Kare: Itama tayi ƙoƙari sosai a lokacin da tayi aiki a ƙarƙashin masana’antar Apple, inda tayi designs masu kyau na na’urar Apple Macintosh, designs ɗin da tayi sun
haɗa da Icons da kuma elements masu yawa na wannan na’ura, sannan ta duk da ana kallonta a matsayin Graphic Designer amma wannan gagarumar gudun mawar da ta bayar zamu iya kallonta a matsayin UI design.

3. Dieter Rams: Wannan ma yayi designs masu kyau a lokacin da UI design ya kasance sabon abu. Ya ƙware a ɓangaren design irin wanda ake kira da “Minimalist Design” a lokacin da yayi aiki a masana’antar Bruan kuma ya samu ɗaukaka ta hanyar sanuwar da littafinshi mai suna “Ten principals of design” yayi a duniya.

4. Don Norman: Norman ƙwararrene ɓangaren design kuma Professor ne a babbar jami’ar Amurka da take a California, San Diego, kuma director a design Lab na jami’ar. Shima ya rubuta littafi mai suna “The design of everyday things” 

Bari mu tsaya anan kada labarin yayi yawa.😎

#yasincoder

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Leave a Reply

Back to top button