Uncategorized

Yadda sojin Najeriya suka yi wa ƴanbindiga ruwan wuta a Kaduna

4
40dea040 bf1e 11ee 973c c3e1f67c749c

Yadda sojin Najeriya suka yi wa ƴanbindiga ruwan wuta a Kaduna 

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta yi wa ayarin wasu ‘yanbindiga ruwan wuta da ke kan babura goma sha biyar a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.
Rundunar ta ce kowane babur yana dauke da aƙalla mutum biyu, kuma ta ce ta yi nasarar halaka su, kamar yadda daraktan hulda da jama’a da sadarwa na rundunar sojin saman Najeriyar, Air Vice Marshal Edward Gabkwet, ya shaida wa BBC.
Ya ce sun samu bayanan sirri ne inda suka samu labarin yanbindigar na kan hanyarsu ta zuwa ƙauyen kamfanin doka da ke kusa da ƙaramar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
“Ƴan bindigar sun riƙa takatsantsan saboda suna tunanin ana bibiyarsu, inda daga bisani suka shige wani gida suka ɓoye, da rundunarmu ta ga haka sai aka kawai aka saki bom kan su.”
Kuma mutum ɗaya bai tsira ba,” in ji Vice Marshal Gabkwet.
A cewarsa “Ƙaton bom muka jefa masu kuma ba mu samu labarin harin ya shafi farar hula ko mutum guda ba.”
Sai dai rundunar sojin saman ta Najeriyar ta ce ba ta samu cikakken bayanin sunayen ƴanbindigar da aka kashe ba.
“Sanin sunayen wadanda aka kashe yana daukar lokaci, kuma mutane sun fara goyon bayanmu sun gane cewa waɗannan ƴan bindigar idan aka bar su za su ci gaba da yin abin da suka ga dama, ” in ji Vice Marshal Edward Gabkwet.
Rundunar sojin saman ta bayyana cewa ba ta da labarin ko ayarin ƴanbindigar za su kai hari wani wuri ne.
“Abin da muka sani shi ne, ranar 28 ga watan Janairun, 2024, sun kai hari kan sojojinmu a Kwanar Mutuwa, kuma tun lokacin muke bibiyarsu, ” in ji Vice Marshal Gabkwet.
Najeriya dai na fama da matsalar tsaro a kusan sassan ƙasar, kuma duk ƙoƙarin jami’an tsaro amma kuma ƴanbindiga da ke satar mutane na ci gaba da kai hare-hare musamman a yankin arewa maso yammaci.

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button