Uncategorized

Batun mayar da birnin tarayya zuwa Legas ba gaskiya ba ne – Fadar shugaban Najeriya

4
0d60b761 be28 4974 90cd d0474ff2ac87

 Batun mayar da birnin tarayya zuwa Legas ba gaskiya ba ne – Fadar shugaban Najeriya

Mai bai wa shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga ya ce shugaban kasar ba shi da aniyar ɗauke babban birnin tarayyar ƙasar daga Abuja zuwa Legas.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, ranar Laraba, Onanuga ya ce masu yada jita-jita ne ke yaɗa maganar domin jan hankalin al’umma gare su.
Wannan na zuwa ne bayan matakin da gwamnatin tarayyar ƙasar ta ɗauka na mayar da wasu ɓangarori na Babban bankin Najeriya da kuma Hukumar kula da filayen jiragen sama na ƙasar zuwa Legas, daga Abuja.
Lamarin da ya janyo ƙorafi da kiraye-kiraye daga wasu ƙungiyoyi na wasu ɓangarorin ƙasar, inda suka yi zargin cewa tamkar wani mataki ne aiwatar da wata ‘manufa ta daban.’
Onanuga ya ce matakin mayar da wani sashi na ma’aikatar FAAN bai kamata ya ja hankalin mutane da yawa ba saboda jihar Legas ita ce cibiyar kasuwanci kuma cibiyar sufurin jiragen sama a Najeriya saboda haka ya ce har yanzu FAAN za ta ci gaba da kasancewa a Abuja.
“Akwai ma’aikatu da yawa da ba a Abuja suke ba dangane da aikinsu kamar NIMASA da take Legas. Haka kuma NPA da kuma hukumar kula da sufurin ruwa (NIWA) da ke Lokoja.’
Sanarwar dai ta ƙara da cewa bai kamata a siyasantar da lamurran gwamnati ba.
Article share tools

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button