Uncategorized

Barcelona na nazari kan Arteta, PSG na zawarcin Guimaraes

4
23800280 be35 11ee 8685 316409d66f25

 

Barcelona na nazari kan Arteta, PSG na zawarcin Guimaraes

Kocin Arsenal Mikel Arteta na cikin mutane uku a jeren mutanen da Barcelona ke son daya ya maye gurbin Xavi, da kuma kocin Liverpool mai shirin bankwana, Jurgen Klopp da na Jamus, Julian Nagelsmann. (Gerard Romero via Sun)
Arteta na duba yiwuwar ajiye aiki a Arsenal a karshen kaka duk da cewa akwai sauran wata 18 a kwantiraginsa, ko da yake har yanzu Barcelona a hukumance ba ta tuntube shi ba. (Sport – in Spanish)
Tsohon kocin Jamus da Bayern Munich Hansi Flick shi ma ya shiga jeren mutanen da Barcelona ke nazari. (Bild)
Paris St-Germain na da kwarin-gwiwar za ta daidaita da ɗan wasan Newcastle mai shekara 26 da ke buga tsakiya a Brazil, Bruno Guimaraes a wannan kaka.(Mirror)
Brentford ta amince da yarjejeniyar fam miliyan 25 kan ɗan wasan Club Brugge mai shekara 18, Antonio Nusa, da ya ja hankalin Tottenham. (Standard)
Luton na tattaunawa da Sint-Truiden kan saye ɗan wasanta mai shekara 24 daga Japan, Daiki Hashioka. (Telegraph)
Liverpool na son dauko daraktan harkokin wasanni daga Bournemouth, Richard Hughes domin maye gurbin Jorg Schmadtke, da ke shirin ajiye aiki a karshen watan Janairu. (Mail)
AC Milan ta tuntubi Arsenal kan ɗan wasan Poland mai shekara 23, Jakub Kiwior. (Calciomercato – in Italian)
Ɗan wasan Lille mai shekara 24, Jonathan David ya kasance wanda Chelsea ke zawarci. (Telefoot via CaughtOffside)
Bayer Leverkusen na kokarin saye ɗan wasan Crystal Palace mai shekara 26 daga Faransa, Jean-Philippe Mateta. (Sun)
Fulham na son sake gwada sa’arta kan ɗan wasan Chelsea mai shekara 22, Armando Broja bayan watsi da tayin farko na fam miliyan 25 daga kungiyarsa. (Teamtalk)
Aston Villa ta sake mika tayi kan ɗan wasan Middlesbrough mai shekara 21 Morgan Rogers kan fam miliyan 15. (Birmingham Mail)
Everton na son dauko ɗan wasan Lyon mai shekara 23 Jake O’Brien. (Irish Independent)
Cardiff da Blackburn da Leeds na zawarcin ɗan wasan Liverpool, mai shekara 26, Nat Phillips a matsayin aro. (Mail)
Kocin Greece Gus Poyet ya kasance wanda ake son daukowa domin horas da Ireland bayan Lee Carsley ya nuna ba zai ajiye aikinsa na horas da ‘yan wasan Ingila ajin kasa da shekara 21 ba.(Times – subscription required)
West Hamna fatan cimma yarjejeniya da ɗan wasan FC Nordsjaelland mai shekara 19 daga Ghana Ibrahim Osman. (Sun)
Sunderland na tattaunawa da Arsenal kan ɗan wasan Ingila mai shekara 19 Charles Sagoe Jr. (Football Transfers)
Ya zama wajibi Chelsea ta sayar da ɗan wasa muddin tana son shiga sabon ciniki kafin rufe kasuwar ‘yan wasa. (Football Insider)
Sunderland ta yi watsi da tayin yuro miliyan 16 kan ɗan wasanta daga kungiyar Italiya Lazio. (Fabrizio Romano)

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button