Ma’anar kalmomin Crypto da ya kamata kasani Fitowa ta ɗaya...

0
Ma’anar kalmomin Crypto da ya kamata kasani
 
Fitowa ta ɗaya...
 


Ana cewa “idan kana so mutane su fahimce ka to kayi Musu magana da Yaren su” haka ma “idan zaka Fahimci Crypto to Ka fahimci/koyi Yaren Crypto” 
 
A Crypto akwai Kalmomi da salon maganganu da inkiyoyi da ake amfani dasu wajen mu’amala da kuma aiwatar da Kasuwar sa.
 
 Wadannan kalmomi suna da matukar tasiri da kuma amfani ga wanda duk yake a cikin Crypto, domin sune yaren da ake magana dasu, idan ya zamana mutum baya gane su to zai iya fuskantar samun matsala wajen rashin sanin hatta inda kasuwa take yi.
 
1. All Time High (ATH):Mafi kololuwar farashin da coin ya taba kaiwa. Ana rubuta ta kamar haka Bitcoins ATH: $64K.
 
2. All Time Low (ATL): Ana Nufin mafi munin karyewar farashin da Coin Yayi a Kasuwa. Ana rubuta ta ne kamar haka, Ripple XRP ATL: $0.5
 
3. Bag:Ana amfani da ita ne Wajen fadar cewa mutum ya mallaki adadi mai yawa na wani coin. 
 
4. Buy The Fucking Dip (BTFD): Ana amfani da ita wajen fitar da Analyst na Coin ma’ana jama’a su sayi mafi saukar farashin Coin din. Misali ka sayi Doge BTFD $0.23
 
5. Alternative Coin (Altcoin): Ana Nufin dukkanin wani coin da ba Bitcoins ba. 
 
 
6. Shitcoins: Ana nufin Coin din da baida da Daraja, Idan ma yayi to ta wani gajeren lokaci ce.
 
7. Bear/Bearish: Ana Nufin lokacin da Coin yake faduwa kasa a farashin sa. Za’a iya cewa WIN ma yanzu yayi Bearish.
 
8. Bull/Bullish: Ana Nufin yanayin da Coin yake haw-hawa a Farashin sa. 
 
9. Dump: Ana amfani da ita Wajen fadar an sayar da wani Coin Mai yawan gaske.
 
10. Pump: Ana amfani da ita wajen fadar cewa Coin kaza yayi mugun tashi, musamman idan aka samu wani ko wasu masu kudi suka zuba makudan kudade acikin sa. Wanda hakan shi zai saka ya tashi.
 
 
11. Gas fee/Gas: Sune kuɗin da ake biya Wajen Transaction, wato charges na transactions.
 
12. Transaction: Ana Nufin shige da ficen kuɗi ta hanyar siye ko sayarwa.
 
13. Stablecoins: Sune Coins din da ake hadashi da kudin dala domin a tsayar musa da farashi kuma a hanashi yawan bazuwa a kasuwa. Misali USDT, BUSD d.s.s
 
14. Whitepaper: Wani Kundi ne daya yake ɗauke da Bayanin coin da dalilin kirkiro sa da kuma abinda ake so a cimma manufa akansa.
 
15. Fiat: Kudin da ke karkarshin ikon gwamnati kuma ta yarda ayi cinikayya dasu. Misali Dollar, Naira, Euro d.s.s
 
 
16. Tokenomics: Kalmomi ne guda biyu Token + Economics. Fasahar da ake amfani da ita wajen gane yawan coins din da za’a fitar da kuma yawan masu Buƙatar sa.
 
17. Airdrop: Tsarin da ake amfani dashi Wajen rabawa ko Tallatawa jama’a Tokens ko Coins Kyauta domin su fara Ajiye shi.
 
18. Cryptography: Hanyar da ake amfani da ita wajen kirkiran Coin, da Kuma gudanar da shi akan na’urorin kwamfuyutoci domin tabbatar da tsaro a kansa.
 
19. Wallet: Jaka ko lalitar da Mutum yake adana Coins dinsa a ciki. Misali Trust Wallet, Safepal Atomic wallet Metamask d.s.s
20. Decentralize Finance (DEFI): Tsarin Kasuwancin Crypto da ya bada yancin gashin kai na cinikayya ba tareda wani ya shiga ciki ba.
 
 
21. Centralized Finance (CEFI): Tsarin Farko da aka fara gudanar da Kasuwancin Crypto kafin (DEFI), Wannan tsarin Kasuwancin Crypto ya kunshi amfani da kasuwanni/Exchangers wajen Kasuwancin. Maslan Binance, Kucoin FTX d.s.s
23. Initial Coin Offering (ICO): Shine tsarin da ake siyar da coins ga wani adadin mutane domin a fara samun kuɗin da za’a yi amfani dasu wajen ɗaukar nauyin project din. 
 
24. Initial Dex Offering (IDO): Shine Dora Coin na akan kasuwar Decentralized Exchange (DEX).
 
25. HODL: Wato Kalmar kodumo ce wannan ainihin ta haka take “HOLD” ma’ana Riƙewa. Ana amfani da ita idan mutum ya sayi Coin Kuma zai ajiye zuwa wani lokaci da idan ya tashi zai sayar.
 
 
26. Fear of missing Out (FOMO): Wannan kalmar ana amfani da ita Wajen bayyana yanayin da mutum yake sauri ya sayi coin sakamakon wani tashi da yayi a baya yanzu ya sauka to sai kaga Mutum nata kokarin sai ya mallaka domin kada nan gaba idan romon yazo ya wuce shi.To a wannan hakan yana kai mutane da dama zuwa ga yin asara sakamakon wannan saurin da zumudin domin kuwa mutum zai saya ne “sama taka” bai san halin Coin din a Kasuwa ba.
 
27. Not Gonna make it (NGMI):Sara Ce da masana Crypto Suke Amfani da ita wajen faɗin cewa wane zai rasa Riba mai yawa a wani coin.
 
28. Erc-20: dukkanin wani token da aka gina shi akan network na Ethereum to sunan wannan token din Erc-20 Token
 
29. Bep-20: Dukkanin token din da aka ƙirƙire shi akan Binance Smart Chain (BSC) to Sunan sa Bep-20 (BSC) Token.
 
30. Trc-20: Dukkanin token din da aka ɗora shi akan Tron Network to Sunan sa Trc-20 Token.


Zamu cigaba a rubutu na biyu insha allah...


Ku biyomu a telegram:- t.me/kumuryamediadotcom

Facebook:- facebook.com/kumuryamediadotcom

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)

#buttons=(Accept !) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn More
Accept !
To Top