Uncategorized

Wasu Mutanen Arewa sun yi watsi da Atiku za su marawa Buhari baya a 2019

4

e684be704e50a37d

– Wata Kungiya ta ‘Yan Arewacin Najeriya tace tana tare da Buhari a 2019
– Kungiyar tace Gwamnatin Buhari tayi aiki da-dama a Arewacin Najeriya
– Hakan ya sa Kakakin Kungiyar yace Buhari ya fi kowa cancanta a 2019

Mun samu labari cewa wata Kungiyar siyasa mai suna North Central Union, NCU tayi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari mubaya’a a zaben da za ayi a 2019. Kungiyar tace Shugaban kasar ya fi kowa cancanta da kujerar.
Realwan Okpanachi, wanda shi ne Kakakin wannan Kungiya ta Mutanen tsakiyar Arewacin Najeriya ya bayyana cewa duk a cikin masu neman kujerar Shugaban kasa a 2019, babu wanda ya dace da kujerar irin Shugaba Buhari.

Kakakin wannan Kungiya, Okpanachi ya sha alwashin cewa za su ba Shugaba Muhammadu da kuma Jam’iyyar APC mai mulki kuri’u miliyan 10 a zaben na 2019. Mista Okpanachi yace Gwamnatin APC ta cancanci tazarce.
Daga cikin ayyukan da Gwamnatin nan tayi a Arewa maso tsakiyar Najeriya akwai aikin titin Mokwa zuwa Ilorin da ake yi da kuma titin Abuja har Lokoja. Kungiyar tace Buhari ne ya dawo da aikin da ake yi na gadar Owetu.
Okpanachi yace sauran ayyukan da Buhari yake yi sun hada fadada hanyar Keffi zuwa Akwanga da kuma titin Benuwai zuwa cikin Makurdi. Bayan wadannan kuma akwai wasu ayyuka na jawo mai daga cikin Jihar Kogi.

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button