Uncategorized

Wacce bajinta Mourinho ya yi a horar da tamaula?

4

104868936 gettyimages 1060204862

Manchester United ta sallami koci Jose Mourinho, bayan da Liverpool ta doke ta 3-1 a Anfield a gasar Premier wasan mako na 17 a ranar Lahadi.
United tana ta shida a kan teburin, inda Liverpool wadda take ta daya ta ba ta tazarar maki 19.
Me ya kamata United ta yi bayan korar Jose Mourinho?
Wadanne nasarori Mourinho ya yi a fagen horar da tamaula.
Kungiyoyi bakwai ya horar da suka hada da Benfica tun daga shekarar 2000, ya kuma horar na karamin lokaci a Uniao de Leiria daga nan ya Porto sai Chelsea da ya horar sau biyu.
Mourinho ya yi kocin Inter Milan da Real Madrid da kuma Manchester United, inda ya ja ragamar wasa 909.
Kocin ya lashe kofi 25 har da na gasar cin kofin Zakarun Turai na Champions Leagues biyu da Premier League uku da Serie A da LaLiga da wadan da ya lashe a Portugal.
Sau uku Mourinho yana lashe kyautar gwarzon mai horar wa a kakar Premier League a 2004-05 da 2005-06 da kuma 2014-15.
Kazalika sau uku ya karbi kyautar Kocin da ya fi kwazo a wata-wata a gasar Premier, inda ya lashe na watan Nuwambar 2004 da Janairun 2005 da kuma Maris din 2007.

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button