Uncategorized

Tsohon shugaban Amurka George Bush ya mutu

4

104575285 mediaitem104575282

Tsohon shugaban Amurka George Bush ya mutu yana da shekara 94 da haihuwa. Dansa George W Bush ne ya fitar da wannan sanarwar.
Tsohon shugaban da aka fi sani da George Bush Senior ya mutu ne ranar Juma’a da yamma kamar yadda wani kakakin iyalin gidansa ya bayyana.
Shi ne shugaban Amurka na 41 tsakanin shekarar 1989 da 1993 bayan ya shafe shekara takwas a matsayin mataimakin shugaban kasa Ronald Reagan.
Amma duk kasancewa farin jininsa ya kai kashi 90 cikin 100, an tuhume shi da rashin kulawa da harkokin cikin gida, inda Bill Clinton ya kayar da shi a zaben 1992.

Ya taba zama matukin jirgin yaki a lokacin yakin duniya na biyu kafin daga baya ya shiga siyasa a 1964 a karkashin jam’iyyar Republican.
A watan Afrilu aka kwantar da shi a wani asibiti bayan da ya kamu da rashin lafiya, lamarin da ya faru mako guda bayan mutuwar matarsa Barbara.

Statement by the 43rd President of the United States, George W. Bush, on the passing of his father this evening at the age 94. pic.twitter.com/oTiDq1cE7 h— Jim McGrath (@jgm41) 1 Disamba, 2018

Wane ne George HW Bush
George Herbert Walker Bush ya fara shiga harakokin siyasa a 1964 bayan ya fara kasuwanci na man fetur inda ya zama miloniya yana da shekara 40.
Matukin jirgin sama ne a lokacin yakin duniya na biyu, amma Japan ce ta harbo jirginsa a 1944 yayin da yake kokarin kai harin bama-bamai ta sama.
Ya fito ne daga gidan masu hannu da shuni kuma ‘yan siyasa a Amurka. Mahaifinsa tsohon sanatan Amurka ne.
Bush ya taba zama shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta Amurka CIA.
A 1980 ne ya zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Republican amma ya sha kaye a hannun Ronald Reagan, amma kuma aka ba shi mukamin mataimakin shugaban kasa.
Shi ne mataimakin shugaban kasa na farko tun 1936 da aka zaba a matsayin shugaban kasa a Amurka.
A 1988 ya sake tsayawa takarar shugaban kasa kuma ya samu nasara.
Bush ne ya jagoranci yaki wanda ya tursasawa Saddam Hussein fice wa daga Kuwait.
Bayan ya bar sojan ruwa a 1945, Bush ya auri Barbara Pierce lokacin tana shekara 18.
Ya mutu ya bar ‘ya’ya biyar, da jikoki 17 da kuma tattaba kunne guda takwas.

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button