Uncategorized

Tsohon bashi: Hukunci zai tabbata kan wadanda suka haddasa tarzoma a zaben 2015 cikin wata jiha a Kudancin Najeriya

4

vllkyt4j7uimiul4f

– Gwamnatin jihar Bayelsa ta ce ba bu ga wadanda suka haddasa tarzoma cikin jihar a zaben 2015
– Majalisar zantarwa ta jihar Bayelsa ta sha alwashin wadanda ke da hannu cikin muguwar ta’adda ta tashin-tashina a zaben gwamnan jihar da gudana a shekarar 2015
– Gwamnatin jihar ta yanke shawarar hukunta wadanda suka haddasa tarzoma a zaben 2015 bayan hukumae Shari’a ta jihar ta kammala binciken ta
Mun samu rahoton cewa, gwamnatin jihar Bayelsa karkashin jagorancin gwamna Seriake Dickson, ta sha alwashin hukunta wadanda suka haddasa tarzoma yayin babban zaben kasa da ya gudana a shekarar 2015 da ta gabata.
Gwamnatin a jiya Juma’a yayin gudanar da zaman majalisar zantarwa na jihar, ta sha alwashin hukunta dukkanin masu hannu cikin aikata muguwar ta’ada wajen haddasa tarzoma da ta auku a jihar yayin zaben 2015.
Majalisar yayin zamanta na 100 da ta gudanar bisa jagorancin gwamna Dickson, ta yanke wannan hukunci bayan da cibiyar Shari’a ta jihar ta gabatar da sakamakon binciken da ta aiwatar kan babban zaben da ya gudana kimanin shekaru hudu da suka gabata.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, majalisar ta bayyana cewa, ba bu afuwa ko rangwami ga wadanda suka haddasa mummunar ta’ada ta tarzoma cikin jihar, inda a halin ta fantsama cikin shawarwari na hukunci da za ta zartar a kansu.
A yayin ganawarsa da manema labarai, sakataren gwamnatin jihar Mista Kemela Okara, ya bayyana cewa hukuncin da majalisar zantarwa ta jihar ta yanke na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da yiwa doka da’a da kuma kiyayewa.

Majiyar jaridarLegit.ngta fahimci cewa, wannan lamari na hukunta wadanda suka haddasa tarzoma a zaben 2015 zai kasance izina yayin da babban zabe na 2019 ke ci gaba da gabatowa domin Hausawa na cewa akan tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro.
JaridarLegit.ngta kuma ruwaito cewa, jam’iyyar adawa ta PDP, ta yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari raddi dangane da rashin amincewarsa da dokar gyara salon zabubbukan kasar nan.

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button