Uncategorized

Sojoji sun ragargaji ‘yan ta’addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu

4

173b257cda826ad4

Dakarun Sojin Najeriya na 8 Division da ke aikin samar da zaman lafiya na Sharan Daji sunyi nasarar kashe wasu ‘yan ta’adda da suka dade suna adabar mazauna karamar hukumar tsafe a jihar Zamfara.
Kamar yadda bayanin sirri na soji ya nuna, an yiwa ‘yan ta’addar kwantar bauna ne Tungar Rakumi a ranar 12 ga watan Disamba. Bayan artabu da ‘yan bindigar, soji sun kashe ‘yan bindiga 2 sannan sun kwato bindigu AK 47 guda biyu da harsasai masu yawa.
Kazalika, dakarun soji na Sector 3 da ke aiki da ‘yan aikin sa kai na Civilian sun damke wani gawurtaccen dilalin bindigu mai suna Lawali Aliyu a hanyar zuwa kauyen Araba da ke karamar hukumar Illela a jihar Sokoto a ranar 13 ga watan Disambar 2018.
An damke shi dauke da bindigu da makamai a cikin buhu. An kwace makaman kuma an tsia keyarsa zuwa ofishin yan sandan Najeriya da ke Sokoto domin cigaba da bincike.
Ga hotunnan a kasa

78d860460552d04c
815731b17717c223
613541c2172b4cac

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button