Uncategorized

Shekaru 15 ga saurayi da jaraba ya kai lalata da akuya

4

vllkyt1ai80vubqjq

-An yankewa wani mutum hukuncin shekaru 15 a gidan kaso
– Wannan mutumi dai ya sadu da akuya ne mai ciki
– Mai shari’a Emeria Sunkutu tace ta tsorata da jin wannan batu

An yankewa wani mutum shekaru 15 a gidan Kaso a bisa tarawa da yayi da wata akuya mai ciki.
Wata kotu a kasar Zambia ta fara yankewa Reuben Nwamba shekaru 5 a gidan kaso yayin da wadanda sukai karar suka ga hukuncin bai musu ba suka daukaka karar zuwa kotun koli.
A halin yanzu wannan kuto ta Kasama ta yankewa mutumin dan shekaru 22 a duniya hukuncin shekaru 15 a gidan kaso tare da aiki mai tsanani.

Kotun tace Nwamba ya sabawa dokar kasar sannan duk wanda aka kara samu ya tara da wata dabbar to shima sai fuskanci irin wannan hukuncin.
Mai shari’a Emeria Sunkutu wadda ke shari’a a kotun Kasama tace tayi mamaki matuka da jin wannan batu.
Sannan daga karshe ta kara masa shekaru 10 akan wadancan 5 din ya koma shekaru 15.

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button