Uncategorized

Rabon kayayyakin da aka kwace: Hukumar Kwastam ta samu yardar shugaban kasa

4

064a4fce12467951

– Hukumar kwastam ta samu yardar shugaban kasa wajen rarraba kayayyakin da suka kwace ga sansanonin yan gudun hijira da gidajen marayu a fadin kasar
– Kakakin hukumar kwatam ne ya bayyana a lokacin wani taron cin abincin safe a Lagas
– Hukumar ta ce kusan rabin miliyan na shinkafa yar 50kg aka rarraba a yankin zuwa yanzu
Hukumar kwastam na Najeriya ta sam yardar shugaban kasa wajen rarraba kayayyakin da suka kwace ga sansanonin yan gudun hijira da gidajen marayu a fadin kasar.
Joseph Attah, kakakin hukumar kwatam ne ya bayyana a lokacin wani taron cin abincin safe a Lagas a ranar Litinin, 17 ga watan Disamba cewa kafin amincewar, ana rabon kayayyaki kamar su kayan sawa, shinkafa da man gyada ga sansanonin yan gudun hijira a yankin arewa maso gabas kawai.

Kusan rabin miliyan na shinkafa yar 50kg aka rarraba a yankin zuwa yanzu, inji hukumar.
Mista Attah yace tsakanin watan Janairu da Nuwamban wannan shekarar, hukumar kwastam ta biya naira triliyan 1.1 a asusun tarayya.

Yace an rigada an tanadi jerin sasanonin yan gudun hijira da gidajen marayun da za’a rarrabawa kayayyakin ba tare da bata lokaci ba.
I

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button