Uncategorized

Kisar basarake: Kotu ta yankewa wata mata da ta kashe mijinta hukuncin kisa

4

bd5aead898c90b85

Jastis Aisha Bashir ta babbar kotun jihar Nasarawa dake zamanta a garin Lafia, ta yankewa wata mata mai suna Amina hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta sameta da laifin kisan mijinta.
An gurfanar da Amina gaban kotun ne bisa tuhumar ta da kashe mijinta, Alhaji Adamu Zubairu, mai sarautar ‘Gom Mama’ a masarautar Kwarra da ke karkashin karamar hukumar Wamba a jihar Nasarawa.
Da ta ke yanke hukunci, Jastis Aisha ta ce masu kara sun gamsar da kotu a kan tuhumar da suke yiwa Amina.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar jami’an ‘yan sanda sun kama Amina ne bayan mutuwar Alhaji Zubairu yayin da ya rage saura kwana daya a daura masa aure da wata matar.

Amina, daya daga cikin matan marigayin, ta kasance babbar wacce ake zargi da kisan Alhaji Zubairu.
An gurfanar da Amina a gaban kotun ne bisa tuhumar ta da aikata laifin kisan kai.
Da yake magana a kan hukuncin da kotun ta yanke, Jibrin Aboki, lauya mai gabatar da kara, ya jinjinawa kotun bisa hukuncin da ta yanke tare da bayyana cewar zai zama darasi ga masu sha’awar aikata laifi irin na Amina.
Sai dai, Mista Shekama Sheltu, lauya mai kare wacce ake zargi, ya ce zasu daukaka kara.

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button