Uncategorized

Kashi 10% na yaran da ba su karatun Boko a Najeriya su na Jihar Kano

4

vllkyt21pidriphugg

Mun samu labari daga Daily Nigerian cewa Kwamishinan harkar ilmi da kimiyya da fasaha na rikon kwarya a Jihar Kano ya bayyana irin matsalar da Jihar ke fuskanta na rashin zuwa makarantar Boko.

Aminu Wudil ya koka da cewa yawan Mutanen Jihar Kano ta sa ana samun karuwar wadanda ba su zuwa Makaranta a Jihar. Wudil ya bayyana wannan ne lokacin da aka yi wani taro da duk masu ruwa da tsaki a harkar ilmi a Jihar.
Babban Sakataren Ma’aikatar ilmi na Kano, Danlami Garba, shi ne ya wakilci Kwamishinan a wajen wannan taro da aka yi a Ranar Lahadin da ta gabata. Garba yace Gwamnatin Jihar dai tana kashe kudi matuka wajen harkar ilmi.
Kididdigar SUBEB ya nuna cewa akwai Makarantun Gwamnati akalla 8, 280 a Kano, sannan kuma akwai Malamai kusan 60, 000. Sai dai Kwamishinan ya tabbatar da cewa akwai yara Miliyan 1.3 da ba su zuwa Makaranta a fadin Jihar Kano

Harsashen da aka yi tun a 2015 ya nuna cewa akwai akalla yara miliyan 1.3 da ba su karatun Boko illa gantali a kan titinan Jihar. Bincike dai ya tabbatar da cewa a Najeriya, yara akalla Miliyan 13 ne ba su halartar makarantun Boko.
Kafin wannan rahoto mu na da labari cewa akwai yara miliyan 20 da su samun ilmin Boko a Duniya, Daga cikin wadannan kaso na sama da yara miliyan 13 a Najeriya, kusan kashi 70% sun fito ne daga Arewacin Kasar irin Kano.
A baya dai Jihar Bauchi ce tayi zarra da Yara sama da Miliyan 1.1. Yanzu dai Jihar Kano ta karbi wannan mummunan ragama. A Jihar Katsina kuma akwai yara fiye da 700, 000 a cikin wannan sahu kamar yadda mu ka ji labari.

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button