Uncategorized

Gaskiyar abinda yasa gwamnati ta tsame Saraki daga zargin fashin Offa

4

d11ced93d8f7b6cb

Jaridar Vanguard ta ci karo da wasu shaidu dake dauke da dalilan da yasa ministan shari’a, Abubakar Malami, ya dage har sai da aka wanke shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, da gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, daga zargin hannunsu a fashin bankunan garin Offa na ranar 5 ga watan Afrilu.
A takardun sakamakon binciken ‘yan sanda da jaridar ta gani, rundunar ‘yan sanda ta kasa samun hujjar dake nuna cewar Saraki da Ahmed sun ingiza ‘yan ta’addar yin fashi a bankuna 9 a garin Offa. Kazalika sun samun hujjar cewar sun bayar da wata gudunmawa ga masu laifin ko kuma ganawa da su kafin su aikata fashin.
Rashin samun hujjar kai tsaye dake nuna akwai hannunsu a cikin fashin ne ya sa ofishin ministan shari’a zukewa daga shiga batun gurfanar da su Saraki, yana mai kafa hujja da cewar hurumin jiha ne tayi hakan, tunda an shirya tare da yin fashin ne a garin Offa, jihar Kwara, ba a birnin tarayya, Abuja, ba.

Rahoton ya bayyana cewar Malami ya nusar da shugaban rundunar ‘yan sanda kan illar gurfanar da su Saraki a kan zargin da babu hujjar da za a iya gabatar wa a gaban kotu.

Yanzu haka dai shugaban rundunar ‘yan sanda ya bayar da umarnin kwace makamai da kudaden dake hannun ‘yan fashin.
Kazalika an gurfanar da Alabi Olalekan, mai taimakawa gwamna Ahmed na musamman, bisa tuhumar sa da mallakar makami ba bisa ka’ida ba. An gurfanar da shi ne tare da ‘yan fashin.

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button