Uncategorized

DUBA WANNAN: Buhari zai mika mulki ga dan kabilar Igbo a 2023 – Sakataren gwamnatin tarayya

4

eb034d5475ffe471

Jam’iyyar APC ta kara jaddada aniyarta kan cewar shugaba Buhari zai mika mulki ga dan kabilar Igbo bayan gama wa’adinsa a shekarar 2023, a cewar sakataren gwamnatin tarayya, Boss Gida Mustapha.
Sai dai wannan mataki na Mustapha ya saba da na ministan aiyuka, gidajen, da lantarki, Babatunde Raji Fashola, na cewar shugaba Buhari zai mika mulki ga dan kabilar Yoruba a 2023.
Da yake magana yayin jawabi ga kwamitin masu goyon bayan Buhari a Umuahia, jihar Abiya, a karshen makon na, Mustapha ya bayar da tabbacin cewar shugaba Buhari ga dan kabilar Igbo idan ya kammala wa’adinsa.
A cewar sa, hanya mafi sauki da ‘yan kabilar zasu samu damar yin mulkin Najeriya shine su goyawa Buhari a zabukan shekarar 2019.

Mustapha, da yake magana ta bakin wakilinsa, Mista Gideon Sammani, ya ce ya yi farinciki da karbuwar da jam’iyyar APC ke kara samu a yankin kudu maso gabas na ‘yan kabilar Igbo. Ya kara da cewar daga abinda ya gani yana da yakinin cewar shugaba Buhari zai lashe zabe a yankin.

Ya ce shugaba Buhari ya nuna kauna da soyayya ga yankin kudu maso gabas da ‘yan kabilar Igbo ta hanyar mayar da hankali ga gina babbar gadar Neja ta biyu.
A jawabinsa, Injiniya Chemberline Adiaso, shugaban kwamitin masu goyon Buhari a yankin, ya ce shugaba Buhari ya tabbatar da cewar shi mutum ne mai kima da daraja.
Ya kara da cewar zasu goyi bayan shugaba Buhari don samun cikar burinsu na samun mulkin Najeriya a 2023.

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button