Uncategorized

Da duminsa: Shugaba Buhari, babu gaskiya cikin al’amarinka – Atiku ya yi mumunan raddi

4

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam’iyyar Peoples Demcoratic Party PDP, Atiku Abubakar, ya yi mumunan raddi ga shugaba Buhari kan rashin rattaba hannu kan sabuwar dokar zabe.
Atiku ya nuna bacin ransa kan wannan abu da shugaba yayi kuma ya nuna shakku kan maganar Buhari cewa zai gudanar da zaben 2019 cikin gaskiya da amana.
Legit.ng Hausa ta samu wannan rahoto ne ta bakin mataimakin shugaban kasan a shafinsa na Tuwita inda yace:
“Ya kai shugaban kasa, ka bamu shakku kan tabbacin da kake badawa cewa gwamnatinka zata gudanar da zabe cikin gaskiya da amana. Ga yan Najeriya da kuma mu yan jam’iyyun adawa, ka nuna babu gaskiya cikin kalamunka.”
Mun kawo muku rahoton cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da gyararren dokar zabe.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yi watsi da dokar zabe ne saboda yana iya kawo cikas ga zaben 2019.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wata wasika da ya aikewa majalisar dokokin kasar.
A wasikar an tattaro cewa shugaban kasar ya ce sanya hannu a dokar zaben na iya haifar da rashin gaskiya da rudani a zabe mai zuwa.
Shugaba Buhari ya kuma roki yan majalisan da su nsake duba wasu rukuni na dokar, inda ya ba da yakinin cewa hakan zai fara aiki bayan zabe.

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button