Uncategorized

Da duminsa: Kotu ta kwace takarar shugaban kasa a SDP ta bawa Jerry Gana

4

vllkyt40oguq7crg8

A yau, Juma’a ne babban kotun Abuja da ke zamanta a Maitama ta yanke hukuncin cewa tsohon ministan sadarwa Farfesa Jerry Gana ne ya lashe zaben fidda gwamni na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) da aka gudanar a ranar 6 ga watan Oktoba.

Jam’iyyar dai ta ce tsohon gwamnan jihar Cross River, Mr Donald Duke ne ya lashe zaben kuma shine dan takarar jam’iyyar a babban zaben 2019 mai zuwa.
Jam’iyyar ta ce Duke ya samu kuri’u yayin da Gana ya samu kuri’u 611.

Sai dai, Gana ya garzaya kotu inda ya nemi a bashi takarar shugabancin kasar saboda tsarin karba-karba da ke cikin kundin tsarin jam’iyyar.

A hukuncin da ya zartas, mai shari’a Hussein Baba-Yusuf ya ce dole ne dukkan mambobin jam’iyyar suyi biyaya ga dokokin da ke cikin kundin tsarin jam’iyyar.
Ya ce tsarin karba-karba da ke cikin kundin tsarin jam’iyyar ya ce ba zai yiwa shiugaban jam’iyya da dan takarar shugabancin kasa su fito daga yanki guda ba.

“A yanzu, shugaban jam’iyyar, Cif Olu Falae ya fito daga Kudu ne kuma shima Duke daga Kudu ya fito. Doka ta yi bayani karara, babu wani abin jayaya a nan.

“Doka ya ce jam’iyyun siyasa suyi biyaya da dokokin da suka kafa da kansu.

“Mai shigar da kara ya gabatar da hujoji da suka gamsar da kotu, an saba kundin tsarin mulkin jam’iyyar, kotu ba za ta iya goyon bayan saba doka ba,”inji shi.

Alkalin ya soke zaben da akayi a baya, ya kuma bukaci SDP ta mika sunan Gana ga hukumar INEC a matsayin dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar a zaben 2019.

Bugu da kari, ya umurci Duke ya dena gabatar da kansa a matsayin dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar.

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button