Uncategorized

BURIN YAN MATAN YANZU

4

%255BUNSET%255D

BURIN YAN MATAN YANZU

Tsaya ki karanta Yar uwa….

Da yawan Yan Mata a wannan zamani basuda wani buri da ya wuce auren Miji kamar na cikin labarin Littafan Hausa ( Hausa Novels ).

Ina mai ba mai irin wannan buri shawara akan ta aje wannan aqida ta nemi Miji tayi aure, domin idan ba haka ba zata mutu batayi aure ba.

Mijin Novel ya mallaki wasu Abubuwa masu matuqar wuyar samu…..:

– A koda yaushe Mijin Novel, dogo ne kyakkyawa, qaqqarfa da kwarjini, wanda a koda yaushe matan cikin labarin suke rubibinshi, suna kawo kansu gareshi shi kuma yana yarfasu….

– Ya kasance a ko kullum Miskili ne, wanda Magana tana masa wahalar furtawa….

– Ya kasance a koda yaushe mai r
a’ayin auren Mace daya ne, kuma a lokacin da yaga Macen da yake so, idan zaije wurin tad’i yakan bata fiye da 100k, kuma idan ya dauketa zuwa shopping zai kashe mata fiye da 350k .

– Idan ya tashi aure ya kan gina katafaren Gida wanda tsayawa misalta kyawunshi 6ata lokaci ne.
– Shine wanda idan za’a kai akwatunan aurenshi, yawansu zaikai na wani shagon, kuma daga kasar waje aka yo odarsu.

– A na daukar fiye da sati biyu ana events na aurenshi, a kowane event kuma Miliyoyin dollar ne za’a riqa 6atawa.

– Bayan aure, a gidanshi kullum fridge cike take da Naman kaji, kifi, kayan ciki da yayan itatuwa. Kuma store kamar wata baitul Mali ta wani gari ..lol

– A koda yaushe gidanshi anayin abinci fiye da kala biyar safe da rana. Haka Matarshi a rana sai ta sake kaya sama da kala shida.

– Kullum shi gwanin iya soyayya ne da lallashin matarsa koda kuwa ita tayi masa laifi.
Kai idan fa tsayawa zanyi nayita baku labarin Mijin Novel, to fa maganar daukar wattani ne, Wanda ni na gaji da posting ku kuma ku gaji da karantawa.

To yanzu saboda Allah ‘Yar uwa a ina kike tunanin samun irin wannan Miji?

Dan girma Allah Yar uwa ki tsaya ki auri wanda yake sonki tsakani da Allah, ki fidda wannan Mafarkin daga cikin zuciyarki domin wahalar da kanki kawai kike…..

Kuma dan Allah MARUBUTA ku sassauta tsara irin wannan Namijin a cikin labarinku, domin kuna cutar da dayawan Mata…..

YA ALLAH KA GANAR DA MASU IRIN WANNAN BURI….

By

Dan Gatan Hajiya

Source: Www.Ashblog.com.ng
Please share to groups

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button