Uncategorized

Badakallar NEMA: Majalisa tayi karin haske a kan batun tsige Osinbajo

4

97a30ec7462d08da

– Majalisar Wakilai na tarayya ta ce babu kanshin gaskiya cikin ikirarin da akayi na cewa tana shirin tsige mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo
– Ciyaman din kwamitin yada labarai da hulda da jama’a na majalisar, Abdulrazak Namdas ne ya yi wannan karin hasken
– Kakakin majalisar, Dogara Yakubu ya gayyaci dan majalisar da aka ce shine ya yi wannan ikirarin a jiya domin ji ta bakinsa
Majalisar wakilai na tarayya ta musanta cewa wai ta fara shirye-shiryen tsige mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo sakamakon zargin da akeyi na cewa ya sanya hannu an fitar da Naira biliyan 5.8 ga hukumar bayar da agajin gaggawa NEMA ba bisa ka’ida ba.
Kakakin majalisar, Yakubu Dogara ya gayyaci dan majalisa mai wakiltan mazabar Egor/Ikpoba-Okha daga jihar Edo, Mr Johnson Agbonayinma wadda shine ya yi ikirarin cewa wasu ‘yan majalisar sun fara rattaba hannu kan wata takarda domin tsige Osinbajo.
Agbonayinma ya yi wannan ikirarin yayin hirar da ya yi da manema labarai a ranar Talata a Abuja.

Sai dai a hirar da ciyaman din kwamitin kafafen yada labarai da hulda da jama’a, Mr Abdulrazak Namdas ya yi da Punch, ya ce babu gaskiya cikin batun.
Namdas ya ce,”Babu wani batun tsige mataimakin shugaban kasa a halin yanzu. Ni ne ke magana da yawun majalisar kuma a halin yanzu babu wannan maganar a majalisa sai dai ba zan iya magana a kan ra’ayoyin ko wane dan majalisa ba saboda haka idan akwai wannan batun, ni ba san dashi ba.
“A matakin majalisa mu dai bamu san da maganar ba.”
Sai dai ko a jiya da ya yi ikirarin, Namdas bai bayyana sunayen ‘yan majalisar da ya ce sun fara shirin tseige mataimakin shigaban kasar ba a lokacin da manema labarai suka tambaye shi.
Amma ya ce wasu ‘yan jam’iyyar APC ne da ke fushi saboda jam’iyyar ta ki basu tikitin sake takara a zaben 2019 suka fara shirin.
An dai dade ana cece-kuce a kan wannan batun amma mataimakin shugaban kasar ya ce ya bi ka’ida a dukkan abubuwan da ya yi yayin fitar da kudaden domin bawa NEMA.

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button