Uncategorized

2019: Wani dan takarar kujerar shugaban kasa ya yi furuci mai sanya faduwar gaba ga Buhari

4

vllkyt7s1hj6pt15m

Mun samu cewa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Farfesa Jerry Gana, ya yi wani furuci mai sanya faduwar gaba ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, dangane da yadda za ta kaya a babban zaben kasa na badi.
Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam’iyyar SDP, Farfesa Jerry Gana, ya bayyana cewa ya zama wajibi kuma tilas ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha kasa a yayin babban zabe na 2019.

Farfesa Gana ya bayyana hakan ne a yau Juma’a cikin garin Abuja, jim kadan bayan da babbar kotun tarayya ta tabbatar da shi a matsayin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam’iyyyar SPD.
Tsohon Ministan sadarwar na Najeriya ya bayyana cewa, kasancewar sa dan takara a halin yanzu, ya zama wajibi shugaban kasa Buhari ya sha babban kayi da tun a yanzu ya kamata ya fara tattara komatsan sa daga fadar Villa domin kuwa an kayyade kwanakin da suka rage masa.

Ya kuma yi tarayya da sauran jam’iyyun adawa dangane da kiran shugaba Buhari akan amincewa da gyara dokar zaben kasar nan, inda ya ce hakan zai tabbatar da gudanar ingataccen zabe na gaskiya da ya tsarkaka daga duk wani nau’i na magudi.
JaridarLegit.ngta ruwaito cewa, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, mai wakilcin shiyyar Sakkwato ta Arewa, ya bayyana cewa babban burin sa a halin yanzu shine, Matasa su kauracewa bangar siyasa kuma su jefa kuri’un su ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Nuhu Sa'Ad Kumurya

Webmaster | Blogger| Publisher | WordPress Developer | Website Designer | SEO EXPERTS | Social Media Marketer | Muslim

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button